UMM ADIYYAH CHAPTER 59 BY AZIZA IDRIS GOMBE

UMM ADIYYAH CHAPTER 59 BY AZIZA IDRIS GOMBE
UMM ADIYYAH CHAPTER 59 BY AZIZA IDRIS GOMBE Www.bankinhausanovels.com.ng  Mun tsaya  TJ dai ji yake yi kamar Juma’a ta yi nisa, yana shiga gida, ya tarar da Rahma da Minaal sun sha kyau cikin kyakkyawar shiga. Da fara’arsa ya isa garesu, ya Cauki baby Minaal ya fara mata wasa, ita kuwa tana ganin sa ta fara KyalKyala dariya. “Za ka zarar min da yarinya Wallahi. Wannan dariyar ai ta fi Karfin jinjira.” “Wannan ce jinjirar? Ki na ga yarinya da wayonta, tana hira tana gayu tana zama, ki wani ce mata jinjira, ai an mana demotion, ko bayb princess? “Kwa dai ji da shi ku kadai, kun ce mata baby, kun ce kuma ba jinjira ba.” Minaal na kafaclarsa ya shige ciki, don ya kimtsa ya rage kayan jikin sa, zuwa Kanana. Sai da suka shiga, ya juyo ya dubi Rahma. “Meye?” Ta fada tana gimtse dariyar fuskarta. “Kin fi ni sanin meye ne ai, wato ke za ki yi wayo ki zille, to ban manta ba.” Hannu ya sa ya zagayeta cikin riKonsa, “A’a na sani ko ganin ‘yarka ya dauke maka hankali.?” “Ke ma kin san ita ce first love dina…