TSINTACCIYAR MAGE CHAPTER 7 BY AUFANA TSINTACCIYAR MAGE CHAPTER 7 BY AUFANA Www.bankinhausanovels.com.ng Tasowa tai dasauri hanunta rik’e da wuk’ar idanuwanta na zubda kwallah tayo gun momy sai suka ja da baya da sauri momy nafadin “a,a wannan yarinyar nan anya tanacikin hayyacinta kuwa security’s kukamata mana kar muma tahad’a damu takashe” itakuwa kuka take tana fad’in “momy waya lashe hamma faruk momy waya kasheshi” cikin matsanancin kuka take maganar,,,….. Security’s hud’u suka kamata suka rik’eta momy tazo ta wanketa da kyawawan marika sunfi a kirga tana fad’in “kin cucemu MUFIDA kin yaudaremu kin rabani da mijina abun k’aunata sannan kuma kin kashe faruk wallahi bazan barkiba saina kema saina kasheki” tana maganar tana marinta kuma tana dukanta, dakyar mubina da d’aya dagacikin security’s d’in suka jata,,,….. Tsintsar mamakine ya bayyana a fuskar MUFIDA kwallah nazubarmata cikin mamaki tace “momy kina nufin kice dady na ma yamutu” mubina ce tai magana cikin kuka tace “to wazaki tambaya bayan kece da kanki kika kasheshi…