TSINTACCIYAR MAGE CHAPTER 6 BY AUFANA

TSINTACCIYAR MAGE CHAPTER 6 BY AUFANA
TSINTACCIYAR MAGE CHAPTER 6 BY AUFANA Www.bankinhausanovels.com.ng  Zama tai anan bakin k’ofar tana kuka maiban tausayi tana zubda kwallah zuciyarta sai zafi take mata,,,….+ Ganin kuka bashine mafita agaretaba yasa ta tashi tacire mayafinta tarufe hancinta dashi sannan tafara kwashe kwalaben giyar tawuce toilet tazube sauran giyardake cikinsu sannan tadawo dak’in tafara tsabtaceshi sai k’ara toshe hancinta take saboda ji take kamar tai amai saboda tsananin warin giyar,,,”….. Bayan ta tsabtace dak’in sannan tawuce d’akinta tad’akko tirarukan d’aki masu k’amshin gaske irin na mutan kebbi tadawo d’akinsa tafesheshi da tirarukan nantake dak’in yad’auki k’amshi, bayan tagama saitai tsaye tana kallonsa yana kwance tarasa yanda zatayi dashi saikawai tad’auki jakarta da phone d’inta tafita ta janyomasa k’ofa tarufe,,”…. D’akinta takoma tacire kayanta tawuce toilet tai wanka sannan tad’auro alwala tafito, bayan tafito tai sallah tasaka kayanta sannan tafito parlor, kitchen tawuce tadafa indomie da …