TSINTACCIYAR MAGE CHAPTER 13 BY AUFANA
TSINTACCIYAR MAGE CHAPTER 13 BY AUFANA Www.bankinhausanovels.com.ng 3pm dot jirginsu yasauka gida Nigeria a katafaren filin jirginnan na AHMADU BELLO INTERNATIONAL AIRPORT dake cikin babban birnin k’asar kebbi, koda jirginsu yasakko tini munira da uncle hisham dasu musty dakuma bodyguard’s sun iso domin tarbanta, tana sakkowa acikin jirgi dagudu su munira sukaje sunamata oyoyo oyoyo itama cikin fara’a suka rungume juna cikin tsintsar farincikin ganin junansu, daga nan kai tsaye suka shiga motocinsu suka wuce izuwa gida,,,”……+ Koda suka isa gida kuwa tini baba mai tuwo tsohuwar y’ar aikin hajiyarsu dady tamata had’adden girkinda takeso, cikin fara’a taje tarungume hajiya itama hajiya tana dariya cike da kewar y’ar jikar tata, bayan sungaisa sannan suka wuce ciki ita da munira, suna shiga tacire kayanta tad’aura towel tashiga toilet, wanka tai sannan tad’auro alwala tafito, bayan tafito tasaka kayanta sannan tagabatarda sallan azahar, bayan tagama kuma tahau kan gado sai bacci,,,…. Sai kus…