NI DA YAYA SADEEQ CHAPTER 9

NI DA YAYA SADEEQ CHAPTER 9
NI DA YAYA SADEEQ CHAPTER 9 Www.bankinhausanovels.com.ng  a bangaran su Zuby  abinda ya faru kuwa shine, + kwatsam wata rana suna cikin gidan da suke yin mitin, kamar kullum yadda aka saba, manyan mata suka zo suka zabe su suna tsaka da sheke ayar su, mai gadin su taji ana buga get koda ta bude matan yan sanda ta gani da bazata iya shaida a dadin su ba, ture ta sukai suka kutsa cikin gidan kai tsaye, har cikin katon falon suka shiga inda suka ganewa idan su zahiri take suka shiga jibgar su, ko wacce sai da taji saukar kulki a jikin ta tasan cewa an musu cune, haka yan sandan suka tarasu a guri guda, can na hangi Zuby da Lubancy sai raba ido suke, koda suka fito motocin yan Sanda ne sunkai goma Sha biyar da DSP Sadeeq ya ke jagoran ta, haka aka tarkata su aka kai su sell, koda labari yaje kunnen Abban Zuby ba karamin cikin tashin hankali ya shiga ba duk da alokacin baya Nigeria gashi bikin ta da Maheer a lokacin bai huce saura wata uku ba, ba shiri ya dawo nigeria, bai zarce ko ina ba sai …