MAI TAFIYA CHAPTER 5

MAI TAFIYA CHAPTER 5
MAI TAFIYA CHAPTER 5                  Www.bankinhausanovels.com.ng  Son kasancewarmu tare daga zuciya ne!+ Kano, Nigeria “A’ataqidhu inni waqa’at fil hub!” ( ina tunanin na fada soyayya)2 Luba ce ke zuba wannan zance a gaban Hindu , Rukky da ‘yar modu. Zaune suke a falon Hajiya Kububuwa ana taya Hindu kwashe kayanta za ta koma sabon gida. To amma aikin na su bai je ko’ina ba saboda abun almarar da Luba ta shigo masu da shi. Bin ta kawai suke da kallo saboda tsananin mamaki. Ta ce ” Sai ina ganin kamar ba ni ba ce. Kun ga Almustapha kuwa Wow..mashallah..mashallah. Ban taba haduwa da mutumin da na ji ina son shi farat daya kamar shi ba! Ai kwana biyun nan da ba ku ganni ba ina gidansa. Kun ga gidan? Aljannar duniya!Dole ne yau na wuce wajen Iyannan na gaya mata yau fa na samu mijin aure! Don bazan juri na ga Almustapha da wata ba! Almustapha…ya rouhi..ya habibii qalbee!”8 Rukky ta taso ta zunguri Luba ta ce ” Wai mafarki ki ke ko idonki biyu? Ko dai wani abu kika sha ya gaya miki karya? Na ji ha…