MAI TAFIYA CHAPTER 3 MAI TAFIYA CHAPTER 3 Www.bankinhausanovels.com.ng Burirrika kamar mayaka su ke a fagen daga wasu sukan kai labari, wasu duk yanda aka so ba za su taba kai labari ba.+ Kano, Nigeria Ranar Asabar aka kaddamar da sababbin ‘yan kungiya. Hindatu, Lubabatu da Rokaiyatou. Aka kafa musu dokokin kungiya kuma duk suka yi mubaya’a.8 Shugaba Hajiya Kububuwa wace irin ingarmar mace ce mai jarabar tsawo kamar daren wahala. Fuskarta baka ce kirin mai dauke da kalangu a kuncinta. Yanayin girman jikinta kadai ya isa ya yiwa dan adam kwarjini ya sa ma sa tsoro, ga ta da zafi kamar barkono. Sai dai mace ce mai haba haba a inda ta san za ta samu Naira.18 Hajiya na da wasu irin “connections” a kasar Najeriya da ketare wanda idan ka ji sai ka sha mamaki. Mace mai tarin jama’a da dukiya. Duk wani wanda ya ci ya tada kai da Nera kuma shedan ya ma sa fitsari a ka ya san da Hajiya kububuwa kuma ta san da zamansa. Babu irin deal din da bata yi, ita ce safaran mata kano to jiddah, ita ce safarar mata da maza kasar it…