ZURI'A DAYA BOOK 2 CHAPTER 7 BY SA'ADATU WAZIRI GOMBE

ZURI'A DAYA BOOK 2 CHAPTER 7 BY SA'ADATU WAZIRI GOMBE
ZURI’A DAYA BOOK 2 CHAPTER 7 BY SA’ADATU WAZIRI GOMBE  Www.bankinhausanovels.com.ng  ya janyo wannan tashin gwauron zabin (go-slow) da ake. Ban da Karar (horn) babu abin da kake ji, ita bata yi gaba ba shi kuma wanda ya yi laifin yaki fitowa daga cikin tashi-motar don yaje ya bata haKuri. Motar Kirar Peogoat ce C350 ash colour, sabuwa fil da ita sai daukar ido take. Cikin mutanen da suka matsu suna gaggawa nan take suka shiga Korafi ganin babu – mai motsi cikin su, kai tsaye wasu suka nufi bakin motar tata, nan suka fara mata ihu da hayaniyar ta kauce ta basu guri idan bata da abin yi susuna da shi. Kashe motar tayi daga (slow) din da take, ta bude Kofar motar ta fito. Kyakkyawar matashiyar budurwa ce ajin farko, jajir da ita kamar ta hada jini da jinsin Larabawa. Doguwa sosai, tsayin ta bai yi yawa ba kuma bai yi kadan ba. Sanye take cikin English wears doguwar riga ce jikinta har Kasa, sannan ta dora top mai dogon hannu akan rigar. Kayan sun yi matuKar karbar jikinta, kanta dauke da dau…