ZURI'A DAYA BOOK 2 CHAPTER 5 BY SA'ADATU WAZIRI GOMBE
ZURI'A DAYA BOOK 2 CHAPTER 5 BY SA'ADATU WAZIRI GOMBE ZURI’A DAYA BOOK 2 CHAPTER 5 BY SA’ADATU WAZIRI GOMBE Www.bankinhausanovels.com.ng Tsawon zaman da muka yi a gurin muna cikin zulumi da sauraro, babu wani daga cikin ZURI’A dinmu da ya zo idan ka cire Hafsat matar Alh. Habibu data samu labarin zuwan mu ta buga masa waya kasancewar yana Lagos gurin aikinsa, shi ne ya bata damar ta zo, domin shi ne kadai bai juya mana baya ba, yana mu’amala damu don ma zamansa ba a nan yake yinsa ba, jifa-jifa yake zuwa amma iyalinsa ya barsu a nan. Awa kusan daya da rabi muka_shafe domin ,har mun saki ranmu da muka samu labarin farfadowarta, zuwa can kuma sai ga wani likita mai suna Dr. Shafi’u ya nufo inda su Mustapha suke, yana zuwa duk suka miKe mu muna daga can gefe muna jiyo abin da suke cewa. Alh. Mustapha sai dai fa kuyi haKuri, domin rai ya yi halinsa, Allah Ya yi mata cikawa sakamakon toshewa da zuciyarta tayi da jini”. Cewar likita. “ Inna lillahi wa inna ilaihi raji’un!”. Abin da duk muka shiga fadi kenan, nan – take Ammin ku ta yanke jiki ta …