ZURI'A DAYA BOOK 2 CHAPTER 16 BY SA'ADATU WAZIRI GOMBE
ZURI'A DAYA BOOK 2 CHAPTER 16 BY SA'ADATU WAZIRI GOMBE ZURI’A DAYA BOOK 2 CHAPTER 16 BY SA’ADATU WAZIRI GOMBE Www.bankinhausanovels.com.ng Mun tsaya BIRNIN LONDON Zaune yake cikin (garden) na (Hilton ; Whatford Hotel) dake birnin London, yana — kallon (Rushing waterfall) din da aka yi (designing) cikin hotel din. Ya harde Kafa daya kan daya, duk wanda ya hango shi-a lokacin zai dauka yana kallon kyan (waterfall) din ne yana yabawa, sai dai abin ba haka yake ba, asali ma idanunsa da tunanin sa sun tafi ga rikicin da Haaya take.son jefe shi da wannan jarrababben son da take masa wanda ya kawo masa tsaiko da karan tsaye a cikin rayuwar Sa. A zahirin gaskiya bashi da wani sauran (feelings) shauki da zai iya bawa wata mace, saboda ya riga da ya bawa Haana dukkan wani shaukin sa, soyayyar sa, Kaunar sa, tunaninsa, kukan sa, dariyar sa, kai da duk wnai (emotions) dinsa, don haka tuni zuciyar sa ta gama cike duk. wani gurbi na yadda babu wata mace da zata samu wani matsayi da sunan ya Ce yana sonta. Ta kai fiye da minti biyar tana kallon sa, shauK…