ZURI'A DAYA BOOK 2 CHAPTER 11 BY SA'ADATU WAZIRI GOMBE
ZURI'A DAYA BOOK 2 CHAPTER 11 BY SA'ADATU WAZIRI GOMBE ZURI’A DAYA BOOK 2 CHAPTER 11 BY SA’ADATU WAZIRI GOMBE Www.bankinhausanovels.com.ng Mun tsaya maimakon ya nuna fushin sa na abin da tayi sai ya yi wani irin murmushi yace. “Haana, (smart girl, I like this Attitude)”. Da murnarta ta Karaso gurinsu yadda suka ganta cikin fara’a suma sai suka fara yin tasu fara’ar, tunanin su komai ya dai daita tsakanin su. Zahra ce ta fara tararta da cewa, “Hajiya ta ya kuka yi ne? Da alama dai komai ya saitu? Don naga alamar farin ciki a tare dake”. Murmushi ta yi ta ce, “Yes Zahra na, komai ya dai-dai ta domin yau na amayar masa da dukkan abin da yake raina. Nan ta kwashe duk yadda sukai ta fada musu. . Mamaki ne Karara ya bayyana a fuskar su, nan suka hauta da fada kowa da abinda ya zo bakin su. Murmushi tayi, ta ce, “Kan ku ake ji, idan za ku zo mu tafi tam, idan ba za ku tafi ba ni kunga tafiya ta, tunda naga alama ranku ya Baci tunda na taba gwaninku”. Tana fadin haka nan taga malam hamza ya shigo ya nufo inda suke (waving) dinsu tayi tana murmushi …