ZABI NA CHAPTER 8 BY FADEELARH ZABI NA CHAPTER 8 BY FADEELARH Www.bankinhausanovels.com.ng AHMAD MUHAMMAD FADOUL RESIDENCE MAITAMA-ABUJA+ Tsaye take a tangamemen kicin din gidan.. Wannan kicin dai babba ne sossai wanda ya hadu iya haduwa.. Komai na cikin shi fari ne sol sai dan touch of black.. Idan ka kalli bangon kicin din zaka rantse da glass aka gina shi.. Floor din ma gani zakayi kamar idan ka taka shi da qarfi zai iya fashewa.. POP kuwa ban ma taba ganin irin shi ba.. Ga wasu lafiyayyun chandeliers da recess lights da aka jera stylishly a jikin POP din wanda ya bada ma’ana sossai. Na’urorin yin girki da suke kicin din masu kyau da tsadan bala’i, wasu ma idan ka gani ba lallai ka san abinda ake yi da su ba.. Kicin din spotlessly clean kamar kullum.. da ganin wannan kicin din ka san cewar mai shi tana ji da shi. Hajiya Aisha wadda suke kira Ammi ita ce tsaye gaban cooker tana qoqarin kammala Shredded chicken sauce din da take yi.. Gaba daya kicin din ya dauki qamshin girke-girken ta as usual. Farar bafillatana kyakya…