ZABI NA CHAPTER 6 BY FADEELARH ZABI NA CHAPTER 6 BY FADEELARH Wani ikon Allah kuwa tun daga wannan ranar Layla ta fita harkar Habib gaba daya.. idan ya kira wayarta bata picking, haka idan ya aika mata text message bata replying. Idan ya je school wurinta bata fitowa.. Haka saqonnin da yake ba Haleema ta bata duk bata sauraron ta.. Abin mamaki sai gashi kullum tare da Layla ake lectures har a gama…1 Ameera ta ji dadi sossai ganin yadda ta mayar da hankali akan karatu musamman don saboda an kusa fara jarabawa. Qawayen su Yusrah da Maryam sunyi mamakin yadda Layla ta canza.. sun kula kwana biyu Habib ya daina zuwa.. Ko da suka tambayeta sai ce musu tayi sunyi fada ne. Su kam har ga Allah sun ji dadi don kuwa daga Yusuf har Habib basu kwanta musu a rai ba. Fatan su shine Allah yasa kar su shirya.. A bangaren Habib tun yana sa ran Layla zata haqura ta biyo shi har abin ya fara bashi tsoro.. Ya kula dagaske fushi tayi kuma da alama bazata sauko ba.. sossai ya shiga damuwa sannan ga muguwar sha’awar ta da ke addabar shi. Ga…