YAR NAJERIYA CHAPTER 8 BY SUMAYYAH ABDULKADIR

YAR NAJERIYA CHAPTER 8 BY SUMAYYAH ABDULKADIR
YAR NAJERIYA CHAPTER 9 BY SUMAYYAH ABDULKADIR                      Www.bankinhausanovels.com.ng  Tuki Saheeb yake amma hankalin sa ba ya jikin sa, a kan titin da zai mai da shi Kano bayan ya baro Hasna’u a kauyen Kachako, tunanin ta ina zai fara yake yi, yayi alkawarin zama bango abin jinginar Hasna’u. Hakan ba zai taba dorewa ba ba ta hanyar aure ba. Idan a da tausayin Hasna ya ke ji to yanzu son ta yake yi, so guda daya mai tsayawa a zuci, soyayya daga indallahi daga inda bai zata ba. Mama is such a kind of person da dosar ta da maganar da bata gamshe ta ba sai mutum ya shirya. Amma kuma dole itan zai fara dosa, in ya so in ta ki, sai ya nemi Barr. Dalha wato aminin Alhaji Wamakko dake zaune a garin Zaria. Ya soma shirya duk kalaman da zai yi amfani dasu wajen lallashin Mama, yana yi yana rehearsal don kalaman su zauna sosai a kwakwalwar sa. Hasna’u will become his wife no matter what…. Mother of his children, koda kuwa su duka zasu zamo albino ko rabi su zamo albino, he will take care…