YAR NAJERIYA CHAPTER 4 BY SUMAYYAH ABDULKADIR YAR NAJERIYA CHAPTER 4 BY SUMAYYAH ABDULKADIR Www.bankinhausanovels.com.ng BAKIN KANON-DABO (MAGANA ZARAR BUNU….) Kwanaki goman suka zo suka shude kamar kiftawar ido, a cikin kwanaki goman nan Hasna’u gata nan ne dai, ita ba mara lafiya ba ita ba mai lafiya ba. Uncle Saheeb bai kara neman ta ba yana can yana ayyukan sa amma komai yake yana tuna Hasna’u, yana Allah-Allah ranar hutu ta zo su tafi Kano tare. Yana so yayi amfani da wannan damar ya kara sanin Hasna’u ya kara jan ta a jiki ta saba da shi ta yadda zata iya gaya masa kowacce irin damuwa take ciki. Ya alkawartawa ransa zama bango abin jinginar ta wanda har nauyin karatun ta zuwa jami’a zai dauka in har Kawu Sama’ila zai bar ta.+ Aka ce yau da gobe kayan Allah, a kwana a tashi ba wuya yau Asabar ranar hutu ta zo. Tun asubah da Hasna’u ta dawo masallaci sallahr asubah bata koma barci ba, wanka ta yi ta sanya wankakkun uniform din ta wadanda ta ninke suka kwana kasan filon ta suka bada Karin guga. Sayayyar da Saheeb yayi mata tana…