YAR NAJERIYA CHAPTER 3 BY SUMAYYAH ABDULKADIR YAR NAJERIYA CHAPTER 3 BY SUMAYYAH ABDULKADIR Www.bankinhausanovels.com.ng A duka kwanakin da suka biyo baya da Hasna’u yake kwana yake tashi a ran sa. Don haka bayan kwana uku da zuwan Hasna’u clinic ya bi kwatancen da ta yi masa ya shiga cikin garin Kachako. Karo na farko da ya taba shiga garin tun fara service din sa. Gwamnatin Tarayyah ta turo shi asibitin ‘Unity College Kachako’ domin hidimtawa kasa, a matsayin sa na wanda ya karanci MBBS.+ Da tambaya da kwatance kuma dama aka ce zabiya baya taba buya a cikin mutane, musamman a karamin gari kamar Kachako, don haka bai sha wahala ba ya gano gidan Kawu Sama’ila. Ya sauka daga kan machine din okada da ya kawo shi ya taka zuwa kofar gidan sannu a hankali, abinda ya dau hankalin sa shine cincinrindon mutane kamar ana daurin aure, sai da ya lura kuma ya gane fuskokin su duka babu walwala kuma kowa alwala yake yi, alhalin ba lokacin kowacce sallahr farilla bane, ba jimawa kuma kafin ya yanke shawarar abin yi ya ga an f…