YAR NAJERIYA CHAPTER 2 BY SUMAYYAH ABDULKADIR YAR NAJERIYA CHAPTER 2 BY SUMAYYAH ABDULKADIR Www.bankinhausanovels.com.ng Tun gani na da shi na farko, zuciya ta bata kara zama lafiya ba, rayuwa ta bata kara komawa daidai ba har yau shekaru talatin a gaba. Ya jirkita rayuwa ta upside-down ta duk yadda yake so, ya hargitsa tunani na ya mayar da shi yadda yaga dama, ya zamo silar da na san cewa ZABIYA ma mutum ne kuma mai ‘yanci, amma kuma shigowar sa cikin rayuwar tawa ba farin-ciki ta haifar ba sai akasin sa. In ma da farin-cikin to takaitace ne na wani dan kayyadadden lokaci. He gave me love but the people around him gave me hatred.+ “What are you crying for Hasna’u?” Ya tambaya cikin kulawa. Ban yi niyyar Magana ba amma sai naji bazan iya share shi ba, duk da na san ba abinda zai iya akan kawo min Inna ta. Ko gano min dalilin rashin zuwan ta. “’Yan gidan ku basu zo bane?” Ya sake tambaya kafin in bashi waccan amsar. Ganewa da yayi cewa hankali na ba ya jikina sabida yunwar da ke sakadata. Ban san san da nace ma…