YAR NAJERIYA CHAPTER 1 BY SUMAYYAH ABDULKADIR

YAR NAJERIYA CHAPTER 1 BY SUMAYYAH ABDULKADIR
YAR NAJERIYA CHAPTER 1 BY SUMAYYAH ABDULKADIR                     Www.bankinhausanovels.com.ng  SADAUKARWA          Sadaukarwa ne ga dukkan ALBINISM din Najeriya…. You are special a yadda Allah ke son ganin ku. +                                                         “YAR NAJERIYA Na taso cike da dokin ranar zuwan ziyarar ‘yan makaranta, ba don komai ba sai don in ga Inna ta, na san kuma Inna zata kawo min kanzo, kuli da kwaki, wadanda su ne kadai abinda nake samu a kowanne visiting, sabanin sauran dalibai masu uba a raye, idan aljihun Inna da dan nauyi (in ta samu surfe mai yawa) kafin zuwan ranar ziyarar mu to tana hadomin da mankuli, manja, da dunkule wani lokacin har da busashishiyar yakuwa (rama) wadda zan dade ina jikawa ina kwadantawa. Makarantar mu makaranta ce ta hadakar ‘yan Najeriya (UNITY COLLEGE) wadda nayi nasarar samu sabida hazakata ba don ina da gatan zuwan ta ba. Duk fadin kauyen mu na fi kowa kwazo a karatun boko da na muhammadiyya har wani suna ake kira na da shi (Huda-Hu…