UWAR GIDAN BAHAUSHE CHAPTER 9 BY SHATU UWAR GIDAN BAHAUSHE CHAPTER 9 BY SHATU Www.bankinhausanovels.com.ng Haka na dawo gidan bikin jikina a sanyaye, hannuna rike da wayata da Kuma novel din da ya kawo min. Dan guri na samu na zauna na cira wayar na cire ta daga flight mode da na saka ta kafin naje gurin Usman. A hankali naji Abu me dumi ya saukar min akan kumatu na, cikin sauri na goge hawayen tare da waigawa kada wani ya ganni Ina hawaye ayimin sharri ace saboda Ismail Bai aureni bane. Gaba daya se naji zaman ya gundure ni kawai so nake na kadaice, dakin su Amira naje, dake ana Shirin tafiya dinner yasa Babu mutane Dan haka na shiga toilet na rufe na tsaya gaban mirror din Ina kallon fuskata yadda ta koma so pitiful, se kawai na fara kuka tareda jingina jikina jikin bangon toilet din, nayi kukan me isata sanan na tatso wani face gel Dana gani cikin toilet trolley na wanke fuskar, Amma dukda haka tayi ja Dana fito, haka Kuma idan na tuna ya tafi se naji hawaye na Kara taruwa cikin idanuna, I wonder me zuciyata…