UWAR GIDAN BAHAUSHE CHAPTER 8 BY SHATU UWAR GIDAN BAHAUSHE CHAPTER 8 BY SHATU Www.bankinhausanovels.com.ng Ayaan! Ayaan!!” Ta Shiga fada a firgice, Baba dake gefenta ya Mike tareda saka wayar shi ya haske fuskarta, gaba ta jike da gumi, kafafunta dake a kannanade se shura su take, haka hannunta da take ta mikawa alamar Ayaan din take son kamawa, wani takaici ya lullube Baba yaji tamkar ya dada Mata duka, ya girgiza kai tareda saka hannun shi ya bubbuga kafadar ta, tayi saurin bude idanunta a gigice, tasa hannunta ta dafe goshinta Jim yadda ruwa yake diga kawai se ta fara sharce gumi tareda kallon Baba dake gefenta, bakinta se rawa yake tace ” Mafarki nayi! Wai…” Tsaki kawai yayi ya juya baya yayi kwanciyar shi, idanunta ta zaro cikeda mamaki tace ” Likita magana nake maka fa, na tsorata fa Amma ka juya min baya” ” Me kike so na Miki? Dare ne Dan Allah ki barni nayi bacci” Daga haka ya kashe flash light din wayar shi ya juya Mata baya da niyyar komawa bacci,a wasu lokutan baka sanin komai ya lalace maka se ya Gama…