UWAR GIDAN BAHAUSHE CHAPTER 11 BY SHATU

UWAR GIDAN BAHAUSHE CHAPTER 11 BY SHATU
UWAR GIDAN BAHAUSHE CHAPTER 11 BY SHATU Seda akai sadakar bakwai sannan washegari Baba yazo Dan daukata tareda Ammi da Gwoggo da zata Kara musu gaisuwa, Tunda garin ya waye Mama ke kuka, Baffa kamar yadda suke Kiran mahaifin su Yana ta lallashin ta da ni kaina da nake ganin zuciyata ta gaza, Ina ganin kamar rayuwata karewa zatai, ban taba kawowa cewa haka zamu rabu ba, ban taba kawowa zai tafi ya barni a duniya ba so early, Allah ya kaddara hakan ce zata kasance, Amma ban kawo hakan ba. Da kyar aka banbare ni daga jikin ta na nufi mota, inata kuka Wanda har yau idan na tuna dacin da naji lokacin da nake kukan se naji idanuna sun ciko da kwalla, se naji wani Abu more of a lump ya tsaya min a makoshi. Kuka nayi na rashin abinda zuciya take so, I just longed for him, his voice and everything about him, lokuta da dama se naji kamar echo din muryar shi,  ko kuma Ina zaune se naji kamar ya shigo na Jima ban daina kukan rasuwar shi ba, ta girgiza ni tazo min a bazata, ta Kara sakawa na Kara Z…