SAINA AURI MARUBUCI CHAPTER 2 BY Xayyeesherthul-humaerath

SAINA AURI MARUBUCI CHAPTER 2 BY Xayyeesherthul-humaerath
SAINA AURI MARUBUCI CHAPTER 2 BY Xayyeesherthul-humaerath                      Www.bankinhausanovels.com.ng  Karasowar Da Mammah za tai nan take Nafeesa ta Fada kasa sumammiya. Ba karamin tashi hankalin Mammah da na sauran malaman ya yi ba, kokarin daukatar suke domin kai ta cikin gida. Dakinta sukaje sannan aka shimfideta kan gadonta. Cike da Mamaki Mammah ke kallon ‘Yar ta ta gata nan dai domin ba suma tai ba alamu sun nuna cewa barcine ya kwasheta lokaci guda. Mammah ta ce, “Ikon Allah daga isowa gida sai wani kalan barci mai ban mamaki.” Ta kalli Malaman tare da fadin, “Mun gode Allah ya saka da alkairi.” Da “Ameen.” suka amsa sannan sukai mata sallama. Kara gyara mata kwanciyar tai sannan ta fice daga dakin. Kamar wasa karfe biyar tayi ko alamar tashi Nafeesa ba tai ba, Mammah ta dubata gata dai lafiya Amman bata tashi ba. Ko da Abhi ya kira waya abaiwa Nafeesa, kawai  Mammah cewa tai tana barci domin ta San da zaran ta Fada mai hankalinsa tashi zai mussaman yadda yake matukar kaunar ‘yartas…