SAINA AURI MARUBUCI CHAPTER 1 BY Xayyeesherthul-humaerath
SAINA AURI MARUBUCI CHAPTER 1 BY Xayyeesherthul-humaerath SAINA AURI MARUBUCI CHAPTER 1 BY Xayyeesherthul-humaerath Www.bankinhausanovels.com.ng Wata Yar matashiyar yarinya na hango da bazata huce shekara goma sha bakwai ba aduniya, kwance take tana barci cikin nishadi da walwala domin da zaran an kalli yadda yanayin murmushi ke bayyana afuskarta wannan ka dai ya isa laburta cewa tana cikin yanayi na farinciki,ta kankame littafin Hausa akirji tamkar tana gundu a kwace mata, mafarkine Wanda ta sabayi kamar kullum Amman ko wanne da salonsa ko na yau din ya yake? Bara mu lekye cikin mafarkin Nafeesa. “Nafeesa kin San cewa ba jin cewa akwai Wata ‘ya Mace da zan so kamarki? Kina jin cewa zan iya furta Kalmar so ga Wata ‘ya Mace bayan ke?, Hmm babu tantama cewa ke ce zabina sannan kuma kece burina,ina miki so fiye da yadda majnun ke son laila,ina kaunarki fiye da yadda kifi ke bukatar ruwa domin rayuwa.” Cewar Nafseen da ke zaune gaban Nafeesa. Gyara zama tai tare da kara kura mai kallo tai murmushi kan ta fara da, “Da ace ana Iya…