NI DA YAYA SADEEQ CHAPTER 4

NI DA YAYA SADEEQ CHAPTER 4
NI DA YAYA SADEEQ CHAPTER 4 Www.bankinhausanovels.com.ng  _____A gaggau ce yayi faking motar sa ya fito ya shiga cikin gidan yayi sa’a babu kowa a falon sai TV da aka bar sa a kunne yana ‘kira’ar alQur’ani mai girma, darect sama ya haura bai zarce ko ina ba sai d’akin sa, yana shiga ya aje wayo yinsa ya cire a gogan hannun sa sannan ya fad’a bayi bai wani d’auki lakaci ba ya fito d’aure da towel a ‘kugun sa da wani a hannun sa yana tsane ruwan jikin sa gaban madubi ya zauna mayuka ne kala kala da tura ruka masu ‘kamshi da tsada ya shafa wannan ya mutstsuka wancen saida yabi yagama shafa ko wanne, sannan ya fesa body spray mai sanyin ‘kamshi wata dakakkiyar shadda fara ya d’auko wanda aka ‘kawata ta da ado da dinkin zamani hular zanna bukar ya ciro ya a je a gefe sannan ya d’auko agogon hannu da safa da ba’kin takalmi mai sheki, a tsana ke ya shirya abin sa tsaf sannan ya d’auki wayo yin shi ya fito. Da sauri sauri yake sauka akan step d’in tun kan ya ‘karasa saukar yake jin hayaniyar su…