ZURI'A DAYA BOOK 1 CHAPTER 5 BY SA'ADATU WAZIRI GOMBE

ZURI'A DAYA BOOK 1 CHAPTER 5 BY SA'ADATU WAZIRI GOMBE
ZURI’A DAYA BOOK 1 CHAPTER 5 BY SA’ADATU WAZIRI GOMBE  Www.bankinhausanovels.com.ng  Na so na nuna cewa Aziza ta dawo gida, amma gudun kada na haifar da wata matsala cikin ZURI’A sai na ja baki na nayi shiru, domin dana ce wani abu za a iya canza min abin da nake nufi. Hakan yasa na yi wata hikima nayi shiru, sai dai abu daya nasa cikin raina zan saka idanu akan rayuwai aziza a cikin gidan, domn ban so ta tana mace ta taso da tarbiyyar taurin kai. Haka, na yi wata hikima da wayo da dabara, nakan shiga gidajen sauran yaranmu ba don komai ba sai don kada su gano cewa gidan – Jafar kadai nake zuwa ayi tunanin da bana zuwa sai da jikata ta koma gidan sannan na tsiri zuwa, sai na mayar da abin cikin hikima yadda babu wani da zai zarge ni da wani tunani, yau naje ‘ gidan wannan gobe naje gidan wancan, hakan _yasa na fara janyo Aziza jiki na. . A duk ranar da naje gidan nasu nakan ganin abinda raina baya min dadi, domin sai ina ganin Hameed na yawan jan Aziza jikinsa, wata rana idan tana zaune…