ZURI'A DAYA BOOK 1 CHAPTER 4 BY SA'ADATU WAZIRI GOMBE
ZURI'A DAYA BOOK 1 CHAPTER 4 BY SA'ADATU WAZIRI GOMBE ZURI’A DAYA BOOK 1 CHAPTER 4 BY SA’ADATU WAZIRI GOMBE Www.bankinhausanovels.com.ng Aziza na da shekara biyar aka yi mata Kani mai suna Nasir, a lokacin ne ma aka haifi Muhammad Kani na biyu ga Hameed. Sannan sai a shekarar Allah Ya bama Maryam haihuwa, ya bata da namiji, ta yiwa Mustapha takwara, wato Ya Abban ki. Sannan kuma a wannan dai shekarar Murja matar Alh. Aminu dan wajen ‘Haj. Saude itama ta haifi da namiji mai suna Sameer. : – In taKaita miki a shekarar nan dai sai da – kusan duk yaran. mu suka haihu, a Kalla cikin shekaru biyu sai da muka yi jikoki sun kai bakwai, kuma duk maza, mata biyu. Amma bayan shekara daya sai da muka rasa mutum uku, cikin su na farko Kabir wanda yake bin Hameed, sai Nasir Kanin Aziza, sai kuma Fiddausi ‘yar wajen Hajara. Shekarun Aziza goma a duniya lokacin Allah Ya dauki ran Alh. Nasir, rasuwar da har yanzu bamu mayar da gurbinta ba, tsayawa baki labarin irin tashin hankalin da muka shiga ba zai yiwu ba, domin kowa yasan mun yi rashin babban bango. Ya…