ZURI'A DAYA BOOK 1 CHAPTER 3 BY SA'ADATU WAZIRI GOMBE

ZURI'A DAYA BOOK 1 CHAPTER 3 BY SA'ADATU WAZIRI GOMBE
ZURI’A DAYA BOOK 1 CHAPTER 3 BY SA’ADATU WAZIRI GOMBE  Www.bankinhausanovels.com.ng  Ganin yadda ZURI’A ta soma yawa farin ciki yana ta samuwa a cikinta yasa Alh. Nasir yin tunanin yiwa yaransa gini yadda za su hadu guri daya har Karshen rayuwar sa, don baya son ya ga abin da zai raba kansu. Don haka ya samu Katon fegi (wato fili) iya ganinka ya ce anan yake son ya gina ma zuni’ar sa gidaje inda za su dunKule guri guda har zuwa lokarin da kowa zai yi nasa iyalin suma su zauna ciki. Lokacin duniya na kwance, ga filaye nan ko ta ina, kuma gashi babban mutum da suke da alfarma a wannan gwamnatin, don haka ya zuba kudinsa sosai ya samu abin da yake so don har matansa mun fara yi masa surutu ya ce mu dai mu barshi, yasan abinda yake, kowa ya zo ya ga filin sai ya girgiza kai.Haka aka fara gini iri daya har gidaje  sama da sha biyu, kuma duk tsarinsu iri daya, sai dai guda daya da ya bambanta da sauran wurin girma. Nan ya fara gaya mana cewa gida ne zai . gina tunda yara maza har mata kowa ya …