ZANEN DUTSE CHAPTER 6 BY AISHA-SHAFIEE

ZANEN DUTSE CHAPTER 6 BY AISHA-SHAFIEE
ZANEN DUTSE CHAPTER 6 BY AISHA-SHAFIEE                    Www.bankinhausanovels.com.ng  Yawwa riƙe sosai.”+ Maganganun da kake ji kenan a cikin shirun dake ratsa katafariyar makabarta dake cikin gidan masarautar Kiyari, mutane ne jingina wanda ke ta ratsowa suna bi ta tsakanin tarin kaburburan dake jere a ciki. A haka aka dinga tahowa da gawar ta hannun mutane har aka iso zuwa gaɓar da ƙasar kabarin da aka haƙa ke tone tana jira, cikin wani rami da yake gida matabacci ƙarshe kuma mai jiran duk wani mai rai, kowa gare shi zai koma banbancin kawai shine sanadin zuwan kowanne ran daban yake kamar ubangiji ya tsara.1 Bayan masu aikin kabarin, a gefe ƴanuwa kuma majiɓanta mamacin ne ke tsaye har zuwa sanda makarar ta iso gare su aka saukar da ita a gefe. Madaki na tsaye kusa da Saifudeen kafaɗa da kafaɗa cikin yanayin tsawo iri guda, dukkaninsu sanye da fararen kaya wanda babu aiki a jikinsu, sai dai Saifudeen na sanye ne da wani sassauƙan naɗi da ya tsaya kamar hula a kansayayin da Madakin ke s…