ZANEN DUTSE CHAPTER 6 BY AISHA-SHAFIEE

ZANEN DUTSE CHAPTER 6 BY AISHA-SHAFIEE

                   Www.bankinhausanovels.com.ng 

Yawwa riƙe sosai.”+

Maganganun da kake ji kenan a cikin shirun dake ratsa katafariyar makabarta dake cikin gidan masarautar Kiyari, mutane ne jingina wanda ke ta ratsowa suna bi ta tsakanin tarin kaburburan dake jere a ciki.

A haka aka dinga tahowa da gawar ta hannun mutane har aka iso zuwa gaɓar da ƙasar kabarin da aka haƙa ke tone tana jira, cikin wani rami da yake gida matabacci ƙarshe kuma mai jiran duk wani mai rai, kowa gare shi zai koma banbancin kawai shine sanadin zuwan kowanne ran daban yake kamar ubangiji ya tsara.1

Bayan masu aikin kabarin, a gefe ƴanuwa kuma majiɓanta mamacin ne ke tsaye har zuwa sanda makarar ta iso gare su aka saukar da ita a gefe.

Madaki na tsaye kusa da Saifudeen kafaɗa da kafaɗa cikin yanayin tsawo iri guda, dukkaninsu sanye da fararen kaya wanda babu aiki a jikinsu, sai dai Saifudeen na sanye ne da wani sassauƙan naɗi da ya tsaya kamar hula a kansayayin da Madakin ke sanye da hula tangaran kalar ruwan ƙasa mai haske, wadda ta dace kuma ta haska yanayin fuskarsa da ba zaka taɓa hasko ɗimbin alhinin dake faruwa a ƙasanta ba.

Tunani ne kala-kala ke yawo a cikin kansa tun daga zuwansu a yau na labarin da ya iske game da ciwon Fulani da kuma ganin fuskar mahaifinsa, Mai martaba.

Ance wai sarki shugaba ne mai ɗaukan dukkan alhakin jama’arsa da kuma matsalolin su har ma ya iya magance su, amma abinda ya gani a safiyar yau bayan zuwa nasa ya tabbatar masa cewa al’amarin dake faruwa a yanzu ya taɓa mai martaba fiye da tarin abubuwan da ya sani a rayuwarsa.

Don bai taɓa ganinsa ya gaza ko ya karaya a kan komai ba tsawon saninsa dashi, shi mutum ne mai tsayawa da jajircewa akan abu, wata irin jajircewa da ta sanadinta ne ya tsinci kansa a rayuwar da yake yi yanzu, shine mutumin da yake kwaikwaya a irin wannan halin har yake ganin cigaba a nasa al’amuran shima, amma idanun mai martaba da ya gani a yau, wasu idanu da suka faɗa suka zangwaye suka ƙara haska tsufan da kwarjini da haibarsa ke ɓoyewa, sun tabbatar masa cewa yana cikin wani hali ne da yafi ƙarfin na nauyin al’ummar dake kansa, wani hali da watakila shi kaɗai zai iya fassara shi a duniyar nan fiye da kowa.

Kuma abinda ya sani shine mutuwar Umar zata taba zuciyarsa kamar yadda hakan zai iya lahani ga kowanne uba, amma tabbas ya sani cewa zancen rashin lafiyar Fulani da ya tsinta a yau shine giɓi mafi girma da yafi lahani a zuciyar tasa.

Tun daga lokacin da ya fara wayon fahimtar al’amura a duniya ya fahimci cewa Mai martaba na mutuƙar son Fulani fiye da yadda yake son tarin abubuwa a rayuwarsa. A baya ba ya taɓa ganin laifinta, duk abinda tayi masa fushinsa iya na wani lokaci ne kawai amma da zarar an ɗan kwana biyu m, da kansa zai koma ya lallashe ta ya bata haƙuri, matsalar da aka samu guda ɗaya ce kawai, Fulanin bata alkinta wannan damar da ta samu akansa ba, tayi watsi da ita har aka kai gaɓar da ya iya furta mata saki, kuma daga wannan lokacin ne vsai zuciyarsa ta kekashe akanta, ya daina damuwa da al’amuranta kamar balle har ya nuna mata damuwarsa.

Amma ance wai ƙauna wata aba ce da bata mutuwa balle ta shuɗe, don haka duk yadda abubuwa suka kai ga canjawa ya san wannan son da Mai martaba ke wa Fulani yana nan, wannan son da yake mata tun daga lokacin da ya yanke shawarar sanyo ta cikin rayuwarsa har zuwa sanda ta gama cike kowanne gurbi ta zama uwar ƴaƴansa, saboda haka ba tabbas ya sani dole ne zuciyarsa ta karye a lokacin da ya fuskanci wani abu mafi muni ga matar da ya raba zuciyarsa da ita.1

“Bismillah…”

Muryar Saifudeen dake gefen Madaki ta janyo shi daga dogon tunanin da ƙwaƙwalwar sa ta faɗa, ya juyo ya kalle shi sannan gawar dake gabansu wadda aka fito da ita daga cikin makarar, a lokaci guda sai kalaman mai martaba suka haska a cikin a kansa, sanda ya durƙusa a gabansa ɗazu bayan isowarsa garin, hannunsa na hagu ya kamo har cikin nasa sannan a hankali cikin kausashshiyar muryarsa yace.

STORY CONTINUES BELOW

‘Ka wakilci ni wajen saka Umar a kabarinsa Ibrahim, ka wakilce ni, na danka maka wannan damar.”

A hankali ya sunkuya har kasa daidai kan gawar, Saifudeen da biyu daga cikin ƙannen Mai martaba waɗanda suke hakimai suka tallafi sauran jikin yayin da shi kuma ya tallafi kansa a hankali da hannu guda har zuwa cikin ramin kabarin. Daga haka ƙwaƙwalwarsa bata ƙara wani tunani ba komai ya zame daga tunaninsa yayin da idanunsa suka tsaya cak akan farin likkafanin, yana kallonsa har haskenta ya disashe yayin da tukwane da tudun jar ƙasa suka shafe shi.5

Karo na farko tun bayan wani lokaci yaji ƙwalla ta taru a duka idanunsa, zuciyarsa ta matse da wani irin ƙarfin imanin dake ƙaruwar a ƙirjinsa, tabbas duk wanda bai yarda da Ubangiji ba yayi asara, asara mai girma kuwa… Don waye zai iya juya duniyar nan ya danƙawa kowa sakamakonsa idan ba Ubangijin ba? A baya zuciyarsa bata taɓa hasashen wannan ranar ba balle har yayi tunanin faruwarta,3

A baya zuciyarsa bata taɓa hasashen wannan ranar ba, hasalima reshe ne ya juya da mujiya akan irin tunaninsa, a wani labari da zuciyarsa ta tsara, shine a cikin kabarin nan, yayin da Saifudeen da Umar ɗin ke sanya shi, a ƙasan zuciyoyinsu da hasashen tarin ribar dukiyar da ya ɗora musu akan jarin da Mai martaba ya danƙa masa. Yayin da a can cikin gida kuma, Fulani ke cikin murna fal tare da ƴaƴanta mata tana ɗokin a share makoki duniyarsu ta dawo sabuwa dal!2

Sai gashi komai ɗin ya juya, komai ya juya zuwa kishiyarsa… Baƙin ciki ya maye guraben da yake musu hasashen farin ciki. Ya zama kamar shi ɗin ne rayuwarsa ke ƙoƙarin gyaruwa a yanzu, kuma Allah ya sani yana jin kamar bai san me zai yi ba, kamar bai san me ya kamata yayi ba…1

Alhali ya sani ɗin.

***

Cikin Masarauta, Ɓangaren Hajja.

12:30pm.

Kusan awa guda kenan da zaman Jidda a katafaren falon da Madaki yace ta zauna ta jira fitowar wata Hajja, don kai tsaye bayan sun iso cikin masarautar wajen ya kawo ta da cewar a duk sanda yazo masarautar nan ne masauki da nan kaɗai yake iya zuwa bayan wajen Mai martaba, yace tana daya daga cikin matan sarki mai rasuwa ma’ana kishiya ce a gurin mahaifiyar mai martaba kenan. Kuma ta san ya dace din dama ace wajenta suka zo amma zuciyarta ta kasa nutsuwa don tun a jiya da ta tabbatar cewa tafiyarsu babu fashi shikenan zuciyarta tayi tsuntsuwa ta tafi wajen ƴan uwanta.

Balle kuma a yanzu da take zaune a cikin masarautar, wani waje da ta barshi ba tare da ta shirya ba balle har tayi sallama da ƴan uwan nata, don haka dole zaman wannan ƙaton falon ya dame ta musamman da yake banda wasu mata biyu a can nesa babu kowa a cikinsa sai wani ƙamshin irin na gidan masu kuɗi dake zagaye hancinta.

Tun sanda suka shigo tare da Madakin akace ita Hajjan tana ganin likitan dake mata gashin ƙafa, don haka yace ta zauna ta jira ta shi zai wuce wajen jana’izar don tun a hanya suka hango ƙofar fada jingim da mutane ana shirin gabatar da sallar, shikenan ya tafi ya barta, gashi kusan awa guda kenan har yanzu babu shi balle Hajjan.

Ta gyara zamanta ta sake gyarawa, fiye da kowa  Sadiya zuciyarta tafi ɗokin gani don tana jin kamar ta shekara goma ne bata ganta ba. Labari da bayani ba irin wanda bata gama haɗawa da tsarawa a cikin kanta ba wanda zata zayyano mata.

Ga kayanta ma suna cikin mota ba’a ko fito dasu ba, dogwayen rigunanta biyu ta ɗaukowa Sadiyar ɗaya da kuma Jamila wadda ta haɗo mata Jamilar har da lace ɗinta. sannan har meatpie ta tashi da sassafe nan tayi saboda Baddo dake mutuƙar sonsa. A hankali ta dunƙule yatsunta cikin tafin hannunta sanda ta tuna abinda ya faru lokacin yin meatpie ɗin nan…

Wajen ƙarfe shida saura ne na safiya, don tana idar da sallar asuba kitchen ɗin kawai ta nufa da niyyar tayi meatpie ɗin kuma don aƙalla tayi sallama da kitchen ɗin dai idan har baza ta dawo ba.

STORY CONTINUES BELOW

Kuma sai da ta gama haɗa komai na fillings ɗin tazo murza fulawar sannan ta duba koina a kitchen din taga babu rolling pin, haka tayi ta bincike kaya da kyar ta samo wata tsohuwar kwalbar lemo a cikin store don haka ta dawo ta goge kan island ɗin nan ta baɗa fulawar ta ta fara murzawa da kwalbar, yana yi kamar ba zai yi ba a haka ta samu dai ta ɗan tara da yawa kafin taji buɗewar ƙofar kitchen ɗin.

Madaki ya shigo sanye da wasu fararen kaya saɓanin wanda ta barshi dasu a jiya, don tun bayan zuwan su Mubarak da ta tabbatar yasha tea da ƙwan da ta soya Masa, bayan jollof ɗin taliya da sauce ɗin kifin data yi da rana sanda suka dawo shi kenan ta ajiye masa magungunansa akan dining ba tare da bari su Mubarak ɗin sun shigo sun same ta ba, ta nufi ɗaki ta shiga harkokinta, ta haɗa ƴan kayanta waje guda tana faman lissafi a cikin kanta na yadda tafiyar zata kasance da kuma abinda ya kamata tayi.

A haka har bacci ya ɗauke ta, kuma bata farka ba sai da aka fara kiraye-kirayen sallar asuba, a sannan ta tashi taga ba kayan data haɗa ɗin a gefen gado, kuma sanin wanda zai ɗauka yasa ta cigaba da harkokinta kawai da tunanin in ta gama abinda zata yi sai ta haɗa komai gabaɗaya a jakar da ya samo mata.

Ta gefen idonta ta ga Madakin ya shigo cikin kitchen ɗin saboda haka sai bata nuna wata alamar ta kula dashi ba har ya rufe ƙofar ya ƙaraso ciki, babu ƙarar takunsa ko kaɗan akan tiles ɗin shi yasa kuma bata lura ya ƙaraso ba sai tsaiwarsa taji a gefen teburin, sai ta tsaya da murza fulawar gabanta ta juyo ta kalle shi, hannunsa mara lafiyan na sanye cikin aljihun kayan da rigar bata kai gwiwa ba yayin da ɗayan ke ƙoƙarin jawo ɗan bowl ɗin da ta zuba naman meatpie ɗin.

A lokaci guda wani abu da bata sani ba ya zarce cikin maƙogwaronta, me yasa ne wai mutumin nan yake wani irin fresh da safe? Allah ya sani har yanzu a wasu lokutan musamman irin yanzu sai taji kamar zuciyarta na kokwanton anya kuwa ya dace koda na kwana ɗaya ne ta karbi matsayin matarsa? Kamala da annurin fuskarsa kaɗai in aka ɗora a sikeli aka kawo ta a ɗaya gefen sai sun rinjayi gabaɗayanta kai tsaye.

“Kin tashi lafiya?”

Muryarsa ta fito a hankali bayan ya gama kallon naman dake cikin bowl ɗin ya juyo gare ta, sai tayi saurin ɗauke kanta ga barin kallonsa, sannan maimakon ta amsa sai itama tace.

“Ina kwana, ya jikin naka?”

Ai tana da hankali sarai, ta san gwada hankalinta yake yi yaji in har zata amsa gaisuwar tasa, tunda tun farko ta fahimci shi mai son a gaishe shi ne.

“Alhmdlilah, na ƙara warkewa. Me kike yi?”

Ya faɗi hakan duk a jere, cikin ɗan hasken safiyar da ya fara ratsowa kitchen din, don duka-duka a lokacin bai fi karfe shida da ƴan mintuna ba.

“Meatpie ne, nake son in kaiwa su Baddo…”

Ta faɗi hakan sai kuma taga wautarta, ai sai yace bata tambaye shi ba ta ɗebi kayan abincinsa zata kaiwa ƴan uwanta, saboda haka sai tayi saurin ƙarawa da…

“… Kuma na san watakila zaka ci wani abun a hanya kafin muje.”

“Me yasa kike yi da kwalba?”

Ya kara tambaya yana kallon hannunta wanda yayi futu-futu da fulawar.

“Babu abin murzawar, na duba koina ban gani ba.”

“Da kin faɗa jiya da mun tsaya an siyo.”

“Nima sai da daddare nayi tunanin in yi.”

Taga sanda ya gyada kansa a hankali, sannan ya ƙara matasa dab da ita, hakan yasa ta juyo ta kalle shi, kamar a ɗan tsorace.

“Da wuya ne yin meatpie ɗin?”

Ta dan yi gajeren tunani kafin ta girgiza kanta.

“Ba dai sosai ba, bayan na isar daga sallah fa na fara, gashi kuma har nayi rabin aikin.”

STORY CONTINUES BELOW

Sai ya gyaɗa kansa sannan Adam’s apple ɗinsa suka motsa kafin hannunsa ya miƙa a hankali zuwa fuskarta, gaban gashinta da ɗankwalin ya fara zamewa ya shiga karkaɗewa a hankali, tana jin saukar yatsunsa guda huɗu akan fatarta.

“Sauri kike tayi kenan, shi yasa har kika bata fuskarki baki sani ba.”

Jidda ta sake haɗiye wani abun da a yanzu ta san sunansa yawu a maƙogwaronta, watakila zata fito ƙiri-ƙiri ta gaya masa cewa bata iya wani tunani mai kyau duk sanda yake kusa da ita haka, sai dai kalaman tambayar da take son yi masa tun shigowarsa, sun fi jeruwa akan hakan.

“Kaga kayana jiya a daki?”

Ya ɗaga kansa har a lokacin bai daina taɓa gashinta ba.

“Yes, na haɗa su waje ɗaya da nawa ne, I might say kin ɗiba da yawa ma, kwana uku fa kawai zamu yi.”1

A wannan lokacin tabbas Jidda ta san cewa inda ita ke ɗauke da irin ciwon zuciyarsa, babu abinda zai hana zuciyarta bugawa a wajen, don kamar bomb biyu ya haɗa mata a cikin jerin kalamai guda, ‘Ya haɗa kayansa da nata waje ɗaya… Kwana uku kawai zasu yi…’

Kuma abubuwa biyu da ta kasa ganewa kenan har a yanzu bayan isowarsu da take zaune tana jiran fitowar Hajjan, don tsabar kaɗuwa a lokacin bata sami damar yi masa tambayar ƙarin fashin baƙi ba, tana jinsa yana cigaba da zira yatsunsa tsakanin gashinta har sanda wayarsa tayi ƙara, wani sunusi ne mai kiran, yana shaida masa cewa gawar mamacin ta iso Nigeria don ance masa a lokacin suna Abuja zasu sake hawowa wani jirgin zuwa Kano, daga nan sai su ƙarasa Kiyari a mota kamar dai yadda tafiyar take.

“A’a’a’aaa….! cancaɗi, maraba lale, maraba maraba…”

Muryar wata dattijuwa dake fitowa daga wata hanya a cikin falon tasa Jidda ɗago da kanta da sauri daga tunanin da take tana son ganin wa ake yiwa tarbar, sai da ganin tsohuwar tana nufo inda take da tare da wata kamar Jakadiyarta a baya, yasa ƙwaƙwalwarta ta hankaɗo da tunaninta waje guda ta fahimci cewa itace Hajjan da take kira tun ɗazu kuma gaisuwar tata ce.

“… Maraba, maraba da matar Madaki, yau Allah ya nuna min wannan ranar dai na ganta, akace wai tsawon kwana mai rana.”

Jidda ta zamo har ƙasan kujerar tun kafin ta iso ta shiga gaishe ta, sai dai Hajjan na ƙarasowa ta ɗago hannayenta.

“Miƙe ƴar nan, in ban gaishe dake ba ai ke ba kya gaida ni ba, bayan a yanzu kece da fadar, hausawa suka ce wai amarya itace cikon gida don haka yanzu kece tauraruwar ai, Maijidda ko?”

Ta ƙarasa tana tambayar sunanta a lokacin da su duka biyun suka zauna a kujera. Jakadiyar kuma ta tsugunna daga ƙasar kujerar.

Jidda ta ɗaga kanta alamun haka ne sannan ta gaishe tan dai.

“An tashi lafiya ya ƙarin hakuri kuma?”

“Haƙuri sai ma’aki ƴar nan, mun gode Allah. Ina shi Angon? Ance tare kuka shigo.”

A cikin kan Jidda ta kasa hada fuskar Madaki da kalmar ‘Angon’ nan, musamman da Hajjan ke kiranta da amarya.

“Ya tafi wajen jana’izar tun ɗazu.”

“A’a…” Cewar Hajjan tana neman wani tafkeken agogo a ɗaya bangon ɗakin.

“Ke! kice ashe lokaci ya tafi, ai ban lura ba. Wallahi yau tashi nayi da matsanancin ciwon ƙafa nan, shi yasa ba shiri nasa aka kira min likita, shakiyin yaron kuma yazo yayi min dai abinda ya saba ni ban ji wani canji ba.”

A lokaci guda sai Jidda taji ta ɗan fara sakewa da ita, da alamun ita babu ruwanta da ɗagawar dukiya ko kuma sarautar su, hira take mata kawai kamar ta samu kokari ta, sai dai kafin ta bude baki ta bata amsa, waɗannan matan biyu suka karaso suka zube akan ƙaton carpet din dake zube a ɓangaren falon mai tsananin laushi.

STORY CONTINUES BELOW

“Barka da fitowa ranki ya dade, barkanmu da safiya Hajja.”

Cewar daya daga cikinsu.

“A’a Ladi ce? Ai ban shaida ku ba, mun tashi lafiya?”

“Alhamdlilah ranki ya dade, ai daga cikin gida muke, munje munyi ta’aziyya, nace bari mu ƙaraso mu yi miki gaisuwa kema tun yanzu.”

“Ai kuwa kinyi dabara, don yanzu ana dawowa zaki ga falon nan ya ɗinke, Nagode sosai Allah ya bada lada, Allah yasa a mizani kuma. Wannan ƴar wajenki ce?”

Cewar Hajjan tana kallon daya matar da bata kai Ladin a shekaru ba, kuma daga wannan tambayar Jidda ta ayyana dama ba lallai a sake juyowa kanta da wuri ba don ta san irin wannan hirar sarai a wajensu Baddo, sai an ɗauko tarihi tun farkonsa an fadi ita matar wacece da kuma iyayenta, ilai kuwa hakan ce ta faru, Ladi tace..

“Au baki gane ta ba ranki ya dade? Hansatu ce fa ƴar wajen Awwalu, ai wajena ta dawo da zama yau shekaru bakwai kenan…”

Shikenan sai aka tafi tarihin Hansatu da aure-aurenta yadda take samun matsala daga mazajen tana fitowa, Hajja na ta gyada kai tana tausayawa, yayin Jidda ta shiga gyara zama tana ƙare wa falon kallo, a haka ne ta hango wani ƙaton hoto da aka kafe shi kusan bango guda a can ƙarshen falon inda shima aka zagaye wajen da saitin kujeru, a hankali shiga nazarin tarin mutanen dake tsaye a cikin hoton, tana kallon kowacce fuska tana wucewa har zuwa kan Madaki, yana tsaye daga bayan wasu ƴanmata biyu sanye da shuɗayen kaya da kuma hular data dace dasu, da alama hoton ya ɗan jima don a yanzu ya ƙara kiɓa kadan kuma sajensa ma yafi haka yawa, sannan yanzu akwai wani abu kamar yanka a ƙarshen girarsa ta hagu da ya ƙarawa girar tasa kyau…

Sai ta cije leɓɓenta na ƙasa a hankali tana jinjina kanta, lallai da gaske ne ko banza ta san ta rike mukamin matarsa in ba haka ba ta yaya zata san wannan ɗan banbancin da ba lallai ido ya hango su ba… Bayan shi sai idonta ya zamo kan fuskar mai martaba wanda ke tsakiya zaune kan karagarsa, matansa uku da kuma ƙannensa mata na zaune a kasan kujerar daga kowanne ɓangare, bata ko bi ta kan fuskar Fulani ba ta tsaida idonta akansa kawai, zuciyarta na ƙara yarda da abinda ta sani akansa cewa shi ɗin mutum ne mai karimci mai adalci da kyakkyawar zuciya, in ba haka ba ko sanin cewa Madaki ba ɗansa bane ba zai bari a sako shi cikin hoton nan na iya jinsin gidan sarautar ba, amma zuciyarsa a wanke take, ya karɓe shi a matsayin ɗan sa kuma baya taɓa banbanta shi da ƴaƴan nasa kamar yadda ta fahimta.

“… Eh, can ɓangaren mai martaba aka yiwa gawar wanka, don haka ita Fulanin ma bana jin ta san an shigo dashi tunda ance tana killace, ba’a ma bari ake inda take.”

Maganar Ladin ta janyo da hankalin Jidda cewar an gama zancen Hansatu, don haka ta juyo ta kalle ta da mamakin Fulanin ce bata lafiya? Ita ta daɗe da cire al’amarin a ranta tun a farko da tayi dukkan hasashenta akanta kuma taji shiru, shikenan ta watsar da tunaninta kawai ta rungumi abinda lokaci ya bata, amma wace irin rashin lafiya ce ta same ta? Wace irin rashin lafiya ce da har ɗanta zai mutu ace za’a tafi dashi a binne ba tare da ta ganshi ba?

“Naga dai su ƴanuwan nasa mata an kira su suje suyi masa addu’a tun sanda zamu fito, to zuwa yanzu ina kyautata zaton an tafi kaishi kenan.”

Cewar Ladin dai. Kuma daga haka Jidda bata ƙara fahimtar hirarsu ba tunaninta ya tafi can kan halin da masarautar ke ciki, musamman mai martaba, yaya zai ji ace ga mutuwar ɗa kuma ga rashin lafiyar matarsa kuma uwargidansa duk a lokaci guda? duk yadda zuciyarta ta kai ga tsanar Fulani sai da tausayinta ratsa zuciyarta a lokacin nan, taji imani ta ƙara ratsa ta, ta yarda cewa duniya ba matabbata bace kuma babu wani abu dake ɗorewa a cikinta walau baƙin ciki ko farin cikin.

Yanzu du-du-du tsakanin lokacin da akayi bikin A’isha da yanzu watanni nawa ne? Kuma a wannan lokacin komai daidai yake a rayuwar Fulani, tana cikin arziƙi da isashiyar lafiyar da har take hango wata nasararta tana binne asiri akan Madakin da take son kassara tasa rayuwar.

STORY CONTINUES BELOW

Amma sai gashi cikin abinda bai ko kai cikar shekara ba anyi juyin waina, abubuwa sun canja canji mafi muni a rayuwarta har ta rasa lafiyarta da tafi komai ga kuma ciwon mutuwar ɗa, kuma babu wani ƙoƙarin ta da zai canja hakan, don tabbas bayan gargaɗin Ubangiji ga bayinsa, Allah kuma ya kan nuna ishara akan wasu mutane don wasu su hankalta. Kuma Jidda ta tabbata Fulani tasha ganin irin wannan ayar akan waɗans, amma son zuciya da huɗubar shaidan suka rufe idanunta ga ganin hakan, sai gashi a yau ta zama misali itama ga wasu masu hankalin a gefe.

Bayan fitarsu Ladi, Hajja ta bada umarnin cewa a kawowa Jidda abinci sannan ta shiga tambayarta wasu abubuwa akanta, musamman game dasu Baddo da akace mata a masarautar suke, sai dai kafin hirar tasu tayi nisa ko kuma kuma abincin ya iso, sai wata Jakadiya ta shigo da sakon wai wasu su Aminu sun zo yi mata ta’aziyya, don haka aka basu izinin suka shigo, kuma sai hakan ya zama kamar buɗewar ƙofa ga tarin mutanen da a lokacin ke dawowa daga makabartar, maza suka dinga shigowa bi da bi, daga wannan jerin sai waɗannan, Hajja nata amsa ta’aziyya yayin da Jidda ke faman gyara mayafinta.

Sai da taga dai abin ba mai ƙarewa bane sannan ta samu ta yiwa Hajjan magana bayan fitar wasu tawaga guda, tace mata tana so ne taje ɓangaren suwajen ƴan uwanta, don zuciyarta ta kasa daurewa, gani take ma kamar ba’a masarautar take ba wani waje ne daban, tunda ita bata taba zuwa ɓangaren Hajjan ba ma sai a yau.

“Kunyi zancen dashi ne? Yace yanzu zaki je?” Hajjan ta tambaya.

Jidda ta girgiza kanta.

“Ya san dai zanje, amma naga bai dawo bane kuma gashi rana ta fara yi.”

Ta bada amsar kuma a cikin zuciyarta tana jin wani iri, banda wani abu ma na aure, ace wai yau wai har ita ce don zata je wajensu Baddo sai ta tambaya? Sai ta tambayi wasu mutane da suke baƙi a rayuwarta.

“To bari a ɗauki waya sai ki kira shi, kar yazo yana tuhuma ta na ɓatar masa da amarya.”

Duk yadda Jidda taso ga daurewa sai da tayi wani ɗan guntun murmushi jin hakan, sai dai har Hajja zata aika a ɗauki wayar, sallamar wasu mazan ta katse su, suka shigo wajen su bakwai don haka da Jakadiyar tazo sai tace ta raka ta falon da wayar take ta kira mata nambar Madaki. Jidda ta miƙe tabi bayanta.

Daga cikin wannan ƙaton set falon hanyar wani faffadan korido ne daga can karshe inda a cikin koridon akwai ƙofofin ɗakunan masu kallon junansu, sak da irin tsarin gine-ginen turawa na farko, kuma an shimfiɗe ko’ina da wani tattausar carpet kalar ja, sai tashin ƙamshin fentin bangwayen suke, falon da wayar take a can ƙarshe yake, ɗan madaidaici mai kalar labulayen ruwan ƙasa, da irin kujerun nan na da masu tsarin C, a tsakiyarsu tebur ne da kuma wata hadaddiyar waya mai ƙirar landline irin dai ta da, sai ƙyalli take kamar ma sabuwa ce.

Jakadiyar ta tsugunna a gaban teburin ta danna wasu nambobi alamun alamun tana neman nambar da zata kira ne, zuwa can sai ta juyo ta miƙo mata kan wayar tana murmushi.

“Ta shiga, in kin gama kawai ajiye wa zaki yi sai ki same ta a can falon.”

Jidda ta gyada kanta alamun ta fahimta sannan ta karbi kan wayar itama ta tsugunna a gaban teburin, Jakadiyar ta miƙa ta fita, kuma sai a sannan ta lura cewar ɗakin tsit yake babu ƙarar komai, wani irin shiru da ya haddasa ƙarfin ƙarar shigar kiran a kunnenta, ta kalli jikin wayar sai taga har da screen mai kyau a cikin alamun dai bata da ɗin bace an sabunta ta da zamani itama.

“Assalamu Alaikum.”

Muryar Madaki tar! Ta ratsa cikin kunnen Jidda da wani irin amo da na’urar speaker ta sake inganta shi, ya kara taushi da kuma zaki, ya ankarar da ita cewa bata taɓa jin muryar tasa a cikin waya ba, to ina ta ganta ma, sai ta sake damƙe hannun wayar tana kallon adadin kiran dake tafiya akan screen ɗin.

STORY CONTINUES BELOW

“Hajja…”

Kafin tace wani abu ya sake faɗa ta cikin hayaniyar mutanen da take ji a bayansa.

“Ba ita bace nice.”

Shiru na sakan biyu ya biyo baya kafin a hankali muryarsa ta sake tambaya.

“Yaya kike?”

Yaya take? Yanzu fa suka rabu, bayan tafiyar kusan awa biyu da rabi tare, saboda haka haka maimakon ta amsa sai itama tace.

“Yaya hannun naka?”

“Alhmdlilah, wani abu kike so?”

Sai ta girgiza kanta kamar yana kallonta.

“A’a, dama ina son inje wajen su Baddo ne sai Hajjan tace in tambaye ka tukunna.”

Wannan karon sai shirun nasa ya wuce na sakan biyu.”

“Zaki gane hanya ne daga nan?”

Ko ba zata gane ba ai bata ce a’a ba, balle ma da ta fara kurɗawa ta cikin lungu a da soraye kamar yadda take yawon ta a baya tsaf zata iso inda ta sani.

“Ko ince da Hajjan a sami mai raka ki?” Kafin ta amsa ya sake faɗa.

“A’a zan gane, na san hanyar.” Tayi saurin tararsa.

“Okay… Sai kin dawo kenan.”

“Akwai kayana a mota.”

“Wanne?”

“Na cikin leda wanda na saka kayan meatpie.”

“Sunusi zai kawo miki, anything else?”

Ta sake girgiza kanta.

“Shikenan, nagode. Allah ya ƙara hakuri.”

“Ameen.”

Ya faɗa kuma bai katse wayar ba, sai itama ta ɗan tsaya tana sauraren hayaniyar gaisuwar dake fitowa daga ciki ba tare da ta san jiran me take ba kuma.

‘Ranka ya daɗe Galadima yace kazo ku gaisa dasu Alhaji Tukur…’

Muryar wani a cikin wayar ta faɗa, saboda haka sai kawai ta sauke hannun wayar ta maida shi inda yake kamar yadda baiwar nan tace sannan ta miƙa.

A can falon Hajja data koma a yanzu har da mata bayan maza falon ya cika taf, don haka bata sami fita da wuri ba sai da Hajjan tayi ta gabatar da ita ga mutane tana fadin ‘Matar Madaki ce’

Kuma abincin da taki zaunawa ta ci, Hajja tasa aka hada mata su flask kusan hudu sannan wata baiwa ta bita dashi, don haka bata sami damar kurɗawa ta cikin lungunan kamar yadda ta tsara ba, baiwar na gaba da kwanuka tana binta a baya kamar dai Matar Madakin…

In ba ikon Allah da aikin wata ƙaddarar ba, ko a mafarki Jidda na zata taba hasko makamanciyar wannan ranar a rayuwarta ba.

Wata ƙaddarar…

Haka mahaifiyarta tace.

***

“Lailahailallahu….! Haka ɗan adam ke canjawa?”

Abinda Jamila ke ta fadi kenan duk lokacin da ta kalli Jiddan dake zaune a gaban Baddo ta tankwashe kafafu tana lomar dambu a bakinta.

Murna fal ba irin wanda ba’a yi ta ba yau a ɓangaren nasu don a sanda Sadiya ta shigo kawowa Baddon dambun da Aunty Zainab tayi musu suka ji ana ta ihu daga waje ana ‘Ga Jidda , Ga Jidda..’ a lokacin kunnenta kasa fassara mata hakan suka yi, sai da suka bazamo Ita da Sadiyan har tana tuntuɓe a kofar sannan nasu mamakin ya sarke da ganin Jiddan dake ta faman murmushi tana nufo hanyar ɗakin, sanye take da wata hadaddiyar doguwar riga dake ƙyalli a cikin hasken ranar tsakar gidan sannan tayi wani irin haske da kyau sai washe baki take yi tana kallonsu daga inda take tahowa.

STORY CONTINUES BELOW

Kuma har ta kai ga shigowa cikin ɗakin zuciyarta bata gama yarda da idanunta ba, sai da ta rungume ta da ƙarfi bayan ta saki Sadiya tana faman kyalkyala dariyar data santa da ita sannan ta fara ganin kammaninta da Jiddan data sani. Sanda taje wajen Baddo kuwa ƙin sarkinta tayi sai da wasu daga cikin mutanen ɓangaren da suka biyo bayanta ke fadin cewa zata ƙarasa ɓalla kafar tata sannan ta ɗaga ta.

Kuma kowa kawai kallonta yake yana mamakin canjawarta, wanda a wajen Jamilar ba ƙaramin dadi hakan ya mata ba, don yanzu duk masu kafa gulma da hasashen cewar Jidda ba dadi take ji ba an rufe bakinsu, gulma ta kare basu da abin cewa tunda Fulanin ma da ake zaton sun hada kai da ita don wata manufar kowa ya san halin da take ciki a yanzu. Don haka masu hasaddar ma duk sai suka zubar da ƴar gulmarsu kowa ya dinga shigowa da fara’a ana gaisawa tare da yiwa Baddon barkan zuwan Jidda, wasu ma ba ko kunya sai a lokacin suke shigowar Allah sanya alherin auren.

Aunty Zainab da Hajiya Laraba ba irin murnar da basu yi ba bayan sun ji labarin zuwan nata, sai ɗakin nasu ya zama tamkar kishiyar cikin gida inda ake faman karbar gaisuwar mutuwa da kuma jajen ciwon Fulani, su a bangarensu wani irin farin ciki ne fal a zukatansu wanda ko a lokacin auren basu same shi ba, sai a yanzu hankalinsu ya kwanta rayuwarsu ke ƙoƙarin komawa daidai, watakila ma har tafi da.1

Dazu bayan fitar ta ne ta dawo ta tarar Aunty Zainab dasu Baddon na yiwa Jiddan wata magana a cikin ɗaki wadda ta tabbata akan zancen kai garar nan ne da kuma asirin da suka ƙone, sai dai  bata wani damu taji yaya Jiddan taji ba don ita duk abinda ya wuce a wajenta shikenan ya tafi kenan.

Jidda ta juyo ta kalleta tana ƙoƙarin kai lomar abincin da take ci bakinta.

“Ai dama na sani duk yadda kika yi missing ɗina awa daya tayi yawa zaki dawo da halinki, Allah zaki sa daga lace dinki har abinda na taho miki dashi ma in fasa baki, shekararta nawa a gidan nan ban canja ba, sai a yanzu don nayi watanni a wani waje?”

“Haba Hauwa’u, da nan da can ai ba ɗaya bane don aure rahama ne, yanzu ko makaho ya shafa ai ya san kin canja, kwanciyar hankali bata ɓuya.”

Cewar Baddo da sai a lokacin ta samu tayi wanka tana shafa mai daga gefe.

“Wai Baddo ni nace muku hankalina a kwance yake? Wallahi kullum da tunaninku nake kwana nake tashi.”

“Duk da haka, don tunda ba zaluntarki yake yi ba ai dole hankalinki ya kwanta.”

“Waya yake maganar zalunci ma Baddo? Kin manta ta ne? Ai wallahi idan Jidda ce ma sai dai ta zalunci mutum.”

Jamilar ta faɗa. Jidda ta sake haɗe rai tana kai lomar dambun nan bakinta.

“Wanda ya aure ki ya shiga uku wallahi, in kika kafawa mutum kahon zuka komai sonsa da kike sai kin zuƙe shi.”

“Ai kuwa Sulaimanun ne dai, don a cikin watan nan ma suka ce za’a kawo lefe.”

“Da gaske?” Jidda ta tambaya tana zare idanunta akan Baddon.

“… Shine ba’a gaya min ba?”

“Yo ta ina? Tunda kika samu ma kika ji yanzu kafin a kawo ma ai sai ki godewa Allah.”

Baddon ta sake bata amsa. Sai ta sake kai abincin bakinta sannan tace.

“Su lefe manya, Ni Allah yayi ba zan taba samunsa ba.”

Jamila data fito daga kitchen ɗauke da plate zata zuba abincin da Jiddan tazo dasu daga wajen Hajja tace.

“Ke ina ruwanki da wani lefe ne yanzu, ina gaya miki idan kika kwantar hankalinki wallahi abinda yafi lefe sai kin samu kin ninka, don ko shi Madakin kansa bai fi lefe ba? ai kin riga kin kai matsayin da an lefe ba komai bane a wajenki yanzu don ni kaina yanzu su Na’ima baki ga wani girma da suke bani ba wai saboda kina auren ɗan Sarki.”

STORY CONTINUES BELOW

Jidda ta tamke lebbenta kawai bata ce komai ba, don duk abinda su Baddo suka gaya mata na asirin nan da suka tsinta har suka ƙona, ita sai bakinta yayi nauyi wajen gaya musu ƴar matsalar data fuskanta itama a farkon zamanta da Madakin, musamman lokacin da yasa aka kulle ta, saboda tun a baya ta taba ji Aunty Zainab na gayawa wata ƙawarta cewa.

Duk sanda wani ɗan sabani ya haɗa mace da mijinta, kuskure mafi girma da zata yi shine ta zayyano wa iyayenta, don a wajenta zata iya mantawa da komai su zo su shirya a tsakaninsu, amma a wajen ƴan gidansu har abada da abinda zasu dinga kallonsa dashi kenan…

Don haka ita a yanzu duk da bata sani ba, bata gama sanin manufar Madaki akanta ba, bata jin zata iya gaya musu wani aibunsa, koda kuwa zai zo ya rabu da itab ne daga baya.

Kuma kafin wani daga cikinsu ya sake cewa wani abun, sai kofar net ɗin ɗakin ta buɗe, Sadiya da tafi yin wanka ta dawo saye da dogon hijabi mai hannu bayan kayan data canja. Don haka tana ganinta ta miƙe daga cin abincin  da take yi ta ɗauki hijabin Baddo da tayi sallar azahar dashi.

“Baddo muna zuwa.” Ta fadi abinda take faɗa a Yawancin lokuta a baya idan Sadiyan tazo wajenta.

“Dan Allah Jidda ki gaya min ya zama matar mutumin nan yake?”

Safiya ta faɗa sanda ta sanda suka tsaya daga can k’arshen dogon tsakar gidan wajen da yake wajen tsaiwarsa a baya, kuma banbancin da da yanzu shine yadda mutanen tsakar gidan ke bin Jiddan da kallo  saɓanin a da da babu mai lura dasu.

“Wallahi ji zaki yi kamar ba gaske ba Sadiya, ni kin san har yanzu ina kalle shi sai inga kamar aiki ya dauke ni a gidan ba wani harkar aure ba.”

“Ai na sani wallahi, shi yasa ranar da muka je bakin kasuwa da Aunty Zainab, na hadu da Suraj ɗin nan yake tambayata ke, nima na rufe ido na gaya masa magana nace kin samu wanda yafi shi.”

“Shine kin gaya masa maganar? Ba kin ɗura masa zagi ba?” Jidda ta faɗa tana haɗe fuskarta.2

“In zage shi ya mare ni Jidda?”

“Shi ya isa ya taba ki a cikin kasuwa? Ai wallahi Sadiya bari kiki ba hakura nayi da zancensa ba, ke ko bashi ba sai nasa an kori wani nasa daga aiki watarana.”

“Eh lallai kice zama yayi zama, kun fahimci juna da masu gari har zaki sa a kori wani daga aiki?”

Sai ta ɗan saki ranta kaɗan.

“Wallahi Sadiya ni har yanzu ban gama fahimtar sa ba, yana dai min kirki sosai amma duk da haka gani nake yi kamar rabuwa zai yi dani wani lokacin tun kinga a yadda aka yi auren.”

“Babu wani zancen rabuwa wallahi, kaddararki da tasa ta riga ta hadu tunda kema tun baki sanshi ba kike koƙarin taimakawa rayuwarsa, kuma ma kina zaton zai rabu dake ne ko don Mai martaba?”

Wannan tambayar ta tsaya akan Jidda na wucewar wani ɗan lokaci.. Tabbas ko don kunyar idon Mai martaba ba lallai Madaki ya rabu da ita ba, musamman a yanzu da Sarkin ke cikin wani hali shi yasa yace mata kwana uku zasu yi su koma kenan, tunanin sake ganin kitchen din nan ya haskaka ranta a take, saboda haka ta sake sakin zuciyarta suka cigaba da hirarsu da Sadiyar, ta zayyana mata dukkan abubuwan da ta kudirce zata bata labari a cikin kanta, don hatta yanayin gidan nasu sai da ta fasalta mata da kuma kitchen ɗin nan.

Bayan sun koma ɗaki ma hirar bata kare ba, har da Aunty Zainab data dawo daga asibitin da take aiki a matsayin mai bada katin yamma, haka suka haɗu aka yi ta hirar yaushe gano, zuciyoyinsu na wankewa da kowacce dariya da suke yi, ba irin ma Baddo, da a kullum take kwana tana tashi da taraddadin kar alhakin marainiya ya kamata.

Har wajen la’asar Jidda nata tunanin meatpie ɗinta dake can cikin mota tana fatan kar wani abu ya same shi. Ilai kuwa ana yin sallar sai ga saƙo wata yarinya ta shigo dashi a leda tace daga wani wai sunusi yace ta kawo. Ledar meatpie ɗin ce da kuma kayan su Jamila data ware daga akwatin da Madaki ya haɗa kayansa, sai dai bayan kayan, daga can kasa idonta ya hango mata rafar kudi na ƴan dubu guda sababbi dal! A jikinsu kuwa wata ƴar ƙaramar takarda ce da wannan haɗaɗɗen rubutun na Madaki.

?? ???? ?????…1

Babu shiri wani faffadan murmushi ya tala ɗan leɓɓenta, ta tsirawa ƴar paper ido daga cikin ledar sai kuma ta tabbata da jikin kuɗin a hankali sannan ta ninke ta, kafin ta bawa Baddo kudin, ai kuwa dukkaninsu suka yi ta murna da godiya musamman Sadiya da ta gwada rigarta ta kasa cirewa, sai juyi take tana jin dadi.

Ran Jidda yayi fari ƙal da ganin irin farin cikin da suke yi na ganinta, har sai da taji kunyar kanta sanda take tunanin wai bata shirya dawowa ba, amma kuma duk da haka zuciyarta bata bar tunanin Madakin ba, tana ta hasashen in yaci abinci da kuma yadda ciwonsa yake a yanzu.

Har akayi sallar magriba akayi isha hirarsu bata tsaya ba, ita da Sadiya suka je suka siyo wata wainar fulawa da suke nacin ci a hanyar cikin gida, suka ci suka ƙoshi sannan Jiddan ta fara tunanin yadda zata sauko da katifarta daga saman wardrobe ta kwanta.

Saboda haka bayan Sadiya ta tafi sai ta dauko kayan baccinta a cikin kayanta dake jere har yanzu a cikin wardrobe ta sanya, tana mutukar jin daɗi na yaushe rabonta dasu sannan ta dawo kusa da Baddo tana saka safa a ƙafarta tana lissafo mata wajajen da zata je a gobe idan gari ya waye.

A lokacin ne kuma wani saƙo da bata tsara ba balle ta shirya masa ya iso, wannan baiwar data taki ta da kayan abinci ɗazu tayi sallama a bakin ɗakin, Baddo ta amsa mata suka shigo su biyu ita da wata, kuma ba ganin fuskarta ne ya sanya gaban Jidda faduwa ba illa ganin abinda yake hannunta… Wannan wayar ce mai ƙirar landline ta falon Hajja, baiwar ta tallafo ta da duka hannayenta biyu alamun duk da izinin mai wayar aka ɗauko ta, ba ƙaramin gargaɗi aka mata ba kafin a danƙa mata ita.

Kuma yadda wayar ke sheƙi a cikin hasken fitilar ɗakin dake dallare ta shine ya tabbatarwa da su Baddo sakon na waye tun kafin baiwar ma ta furta.

“Ranki ya daɗe, Madaki ne ke son magana dake, yace a kawo miki wayar.

Cewar baiwar tana ƙoƙarin danna nambobi data danna a ɗazu, Jidda kallonta kawai take da safa guda daya da bata gama sakawa ba yayin da take neman dukkan wani tunani a kanta yana zillewa…

Hannunta kusan rawa yake sanda ta karɓi wayar a hankali, kowa yayi shiru a ɗakin don daga Baddo har Jamilan dake can gefe tana waya sun juyo da hankalinsu kanta.

Kuma kafin tayi ƙoƙarin haɗa tunaninta waje guda, muryar Madaki da ta fito tar daga cikin speaker wayar ta sake tarwatsa dukkan tunaninta…

“Kin san masauki na ko? Kizo muyi dressing ɗin…”16

***

Cikin shirun ɗakin da rashin haskensa, Muryar Jidda ta fito a hankali tana sallama tsaye daga bakin ƙofar yayin da hannuta ke riƙe da handle ɗin, ƙafarta kuwa ɗaya a ciki take ɗaya a waje.+

Kuma kamar wancan lokacin, wannan daren da ya gifta da ƙaddarar rayuwarta, ko’ina tsit yake babu motsi balle ƙarar komai, yanayin daren ma kamar wancan ne, banbancin kawai a yanzu shine bata kutsa kai cikin ɗakin kai tsaye ba sannan sautin muryarta a hankali yake fita saɓanin wancan lokacin da take rangaɗa sallama kanta tsaye.

Sai ta juyo bayanta a hankali ta kalli Jamila dake shirin shan kwana a can harabar wajen, ita ta rako ta har nan ɗin bisa umarnin Baddo wadda tace ta tashi ta tafi bayan ita kanta taji muryar Madakin daga cikin wayar.
Allah ya sani zuciyarta bata so hakan ba saboda an ruguza mata shirinta, ta riga ta gama tsara yadda zata yi kwanciyarta a kusa da Baddo, yadda daren yau zai tuna mata da baya, wani lokaci da bai dade da shudewa a cikin rayuwarta ba, yadda Jamila zata tashe ta sallar asuba da yadda hasken alfijir zai ratso ta saman windon da take sa katifarta, so take ta tuna komai, komai ɗin da zai ɗan wanke tunainta daga rayuwar lagos ɗin nan ta yadda ko da Madaki zai zo ya rabu da ita daga baya, aƙalla dawowar tata zata zo mata da sauki. Don duk da maganar da Sadiya ta fada mata da kuma ta Jamila a yanzu da suke tahowa, har yanzu daitata zuciyar gama bata tabbacin cewa rayuwa zata doreata tare dashi.

‘A da naji tsoro Jidda, ƙwaƙwalwata kullum cikin lissafin halin da kike ciki take saboda yadda al’amura suka faru da kuma yadda yazo ya ya tafi dake ke din nan, amma ganinki a yau ya wanke komai, ba ni kadai ba kuma har su Baddo na san hankalinsu ya kwanta, wallahi ƙaddararki mai kyau ce Jidda ta kai ki wani matsayi da in ba al’amarin Allah ba babu ta yadda za’ayi ya faru, don haka a yanzu damarki ce, ya rage wa hankalinki ki san yadda zaki yi ki gyara rayuwarki.3

Wallahi bari kiji na rantse miki idan kika yi saken da wani abu zai raba ki da mutumin nan, wallahi ba zaki taba samun irinsa a rayuwarki ba! Shi yasa kika ga munyi iya koƙarin mu wajen tone asirin nan tun kafin mu bada wata hanyar da za’a gano mu ko mu gama tantance asirin na meye, tunda aka riga akayi auren nan kowa fatan alkhairi yake miki Jidda, ko masu nuna hassadarsu don dai kwai babu yadda zasu yi ne amma wallahi ko su baza su so miki rabuwa dashi ba, don haka dan Allah kiyi amfani da ɗan ragowar hankalinki Jidda, kiyi masa biyayya, ki kyautata zamanku sannan ki riƙe addu’a. In kika yi hakan wallahi kin rufe duk wata ƙofar da zai iya tunanin rabuwa dake.’2

Ta sani itama, har cikin zuciyarta ta san da hakan, ta san a matsayi da yanayinta baza ta taba samun wani miji kamar Madaki a gaba ba duk kuwa tsawon shekarun da zata ɗauka a duniya. Kawai matsalar shine daga Jamilan, Sadiyan dake bata wannan tabbacin na ba zai rabu da ita ba, don basu sanshi bane, basu taba ganinsa a kusa ba, basu san ɗimbin abubuwan da yake dashi wanda suka banbanta mutuka da rayuwarta ba, shi yasa suke ganin cewa ta dace da rayuwar tasa kuma ba lallai ne in tayi wasu abubuwan ya iya rabuwa da ita ba.  Amma bata son ta sawa zuciyarta gaibu, gwara tayi dukkan wani tanadi ta yadda duk ranar da hakan ta kasance, zuciyarta ba zata shiga cikin wani hali mara kyau sosai ba, tunda ance sa rai da koshi shi ke kawo yunwa.

Saboda haka ta haɗiye yawu a hankali sannan ta sake juyowa ga barin kallon hanyar da Jamilar ta ɓace, idanunta suka sauka a cikin ɗakin data buɗe ƙofarsa kaɗan, yawu ya wuce ta maƙogwaronta, taji kamar ba zata iya ƙarasawa ciki ba, kamar ta juya kawai tabi bayan Jamilar da cewar baya nan  amma sai zuciyarta ta bata shawarar cewa ta daure kawai ta shiga ɗin, don ko ba komai tana son ganinsa ma, kuma idan  taji cewar akan dressing ɗin ne kaɗai ya kirata saita a gaya masa cewar ita bata iya wani dressing ɗin ciwo ba, ta gaya masa cewa kwata-kwata karatunta iyakarsa secondary kuma ko jarabawar waec ma bata ci ba, watakila idan yaji hakan yayi tunanin kiran likita ita ta koma, ai dare baiyi ba tsaf zata iya juyawa tunda a wancan ranar da tazo ma kusan i-yanzu ne.

STORY CONTINUES BELOW
Saboda haka sai ta sa jikinta ciki sannan ta maida ƙofar ta rufe a hankali, komai yana nan a ɗakin yadda yake babu abinda aka canja sai ma gyara da wajen yasha da alama, don bayan rashin ƙura akan tiles ɗin wani ƙamshi kuma na airfreshner na tashi a iska, ƙamshin da ya haɗu ya tuna mata da abubuwan da suka faru ƴan watanni kaɗan da suka wuce, zuwanta ɗakin cikin rashin sanin canjin da hakan zai kawo a rayuwarta, komai ya shiga haskawa a idanunta, tana ganin kamar zata ganta ne a lokacin da take bincike jakunkunan nasa ko lokacin da ta fito daga banɗaki bayan ta kasa fita jini na diga daga jikinta. Sai kuma ta juya wajen window nan ta kalli labulen da ta ɓoye a bayansa.. inda Mai martaba ya shigo ya gansu har ya yanke hukuncin da a yanzu ya zama sanadiyar dawowarta ɗakin da wani suna na daban… ‘Matar Madaki’

“Are you telling me basu kawo ba? Bayan tun jiya muka yi zancen da Habibu..”

Kafin ta fahimci motsin fitowar mutum daga hanyar koridon da tun a baya ta fahimci ɗaki ne, muryar Madaki ta amsa cikin shirun ɗakin, hakan yasa ba shiri idanunta suka kai wajen, kuma suka sauka cikin kyakkyawan gani, don shima ganin nata ne yasa yaja ya tsaya daga bakin koridon, kamar yadda suka rabu da safe, hannunsa mara lafiyan na sanye cikin aljihun wandonsa yayin da ɗayan je riƙe dacwayar da yake yi, sai dai bai kara ta a kunnensa ba sakamakon wani ɗan guntun earpiece dake makale a kunnensa na dama, wandon wannan farar shaddar dake jikinsa tun safe ne kawai a jikinsa ba tare da rigar kayan ba, illa wata farar singlet mai kauri da ta ɗame ɗam akan fatarsa.

“So through out yau baki ganshi ba kenan?”

Ya sake faɗa directly yana kallon Jiddan dake ƙoƙarin janye idonta tana sake sallama, sai dai bai amsa sallamar ba da alamun sauraren bayanin na cikin wayar yake yi, amma kuma sai ya tako a hankali ya cigaba da tahowa gabanta.4

“Kuma bashi da waya..?”

Sautin muryarsa tasa a yanzu ya fito tare da wani abu kamar ɓaci rai.

“Then me kike so ki min proving? From 7am to now kusan awa goma sha biyar baki samu hanyar da zaki ga Habibu a cikin Lagos ba? What are you worth of kenan? (Amfanin me kike dashi kenan?)

A yanzu ƙarara fushin muryar tasa ya fito yayin daya tsaya a gabanta kuma kafin tayi wani motsi ya sanya wayar hannunsa cikin daya aljihun sannan ya kamo hannunta na dama, yatsunsa suka ratsa cikin nata, wani abu da a yanzu daga zuciyarta har hannun nata ya riga ya saba dashi.

“Look Toyin, I’m staying here for only three days and I’m resuming office early Monday morning, so I don’t care what it takes you to get this done, all I know is I want everything nice and clean on my desk before I even arrived, else that day will be the last time you will ever see my face.”

(Ki saurare ni Toyin, kwana uku kawai zanyi a garin nan don haka zan dawo office ne da sanyin safiyar Litinin, kuma ban damu da duk abinda zaki yi kafin ki kammala wanban aikin ba, kawai abinda na sani shine in ga komai yayi daidai ajiye akan teburina kafin ma in iso, in ba haka ba  wannan ranar zata zama rana ta karshe da zaki sake ganin fuskata.)

Ya sake faɗin hakan cikin fushin da yake koƙarin dannewa wanda ya san ko kaɗan Toyin ɗin bata da wani kamasho a cikinsa, laifin na Habibu ne, don me yasa zai ki shiga office ɗin ba tare da wani dalili ba alhalin sunyi maganar aikin nan a daren jiya kafin tahowarsa, don haka laifin nasa ne ya shafi Toyin har yake mata faɗa haka, sannan da kuma ƙarin cewa tun safe zuciyar tasa ba dadi, Allah kadai ya san tarin abubuwan da ya wassafa ya kwance a cikinta don nemawa kansa mafita.

“Barka da yamma, ya karin hakuri?”

Muryar Jidda ta fito bayan ya sauke wayar kuma ba tare da ya saki hannunta ba. Idanunsa ita suke kallo shima da dukkan attention ɗinsa yana son ya tsinto ainihin halin da take ciki don ya fassara wani abun, saboda haka yanzu ma bai amsa gaisuwar ba sai yace.

STORY CONTINUES BELOW
“I’m sorry dare yayi, na fito dake ko?”
Muryar tasa ta fito cikin ƙoƙarin saita kansa, don haka ya tattaro dukkan kulawar da zai iya a cikin amonta.

Sai ta girgiza kanta.

“Tare da Jamila muke ai, kuma hanyar akwai haske.”

Jidda ta faɗa a lokacin da  zuciyarta ke yaki da idanunta akan kar ta kalle shi, don Allah ya sani bata taba haskowa kanta tsayawa a kusa da namiji cikin irin wannan shigar ba, sai dai bata isa ta yaudari zuciyar tata ba, ita ta san ta danyi kewar ganinsa tsawon yinin kuma saboda hakan ne ma ta shigo, ko ta manta ne har barin aiki kawai take a gida don in ya dawo ta ganshi?
Saboda haka duk iya ƙokarinta sai da idanun nata suka bijire mata, ta ɗago ta kalle shin a lokacin da yake tambayarta ‘Jamilan ta koma?’

Ta ɗaga kanta tana ganin yadda tsawonsa daya ƙara bayyana a gabanta. Sai dai ba abinda tafi lura dashi ba kenan.

Idanunsa take kallo da suka canja, sun faɗa ciki sosai suna ƙara lumshewa, sannan bayan haka kuma samansu ya ɗan yi ja kamar na mara lafiya, a lokaci guda sai ta manta komai, ta manta zancen data shigo da niyyar gaya masa cewar bata iya dressing ɗin ba balle har ma ta sake tunanin komawarta wajen su Baddo, ta manta ma yanayin da yake tsaye a gabanta dashi, taji kamar sun koma Lagos ne wani waje da daga shi sai ita, inda take kula dashi, inda hankalinta baya kwanciya idan bashi da lafiya.

“Me ya same ka?” Muryarta ta fito ba tare da tayi shawara ba, sannan a sake ba kamar yadda ta amsa tambayarsa da farko ba.2

A lokaci guda kalamanta suka ratsa tun daga kan fata har zuwa wani saƙo a cikin zuciyar Madaki, suka taɓo wani abu mai laushi da bai san dashi ba, suka gaya masa cewa dole ne ma yana buƙatar yarinyar nan a rayuwarsa, don tana da dukkanin wani abu da yake buƙata ko ma ace bai san dasu ba a rayuwar tasa, a kodayaushe tana cike duk wasu tarin guraben da suke giɓi a tare dashi, tana ƙara nuna masa cewa kulawarta da halayyarta sune daidai da abinda yake nema a rayuwarsa, don haka zuciyarsa ma ba zata taɓa son wani abun da zai fi ta ba ko kuma yayi ƙasa da ita ba.
Ita ɗin dai zuciyarsa ke so kuma take buƙata, ya san cewa ya taɓa faɗar makamanciyar wannan maganar a can baya, ranar da ƙaddara ta shigo da ita cikin rayuwarsa, sai dai a wancan lokacin da wata ma’anar daban, don abinda bai sani ba a sannan shine kalmar bukatar suna ta tara!

Saboda haka sai ya murza yatsunta da yake rike dasu a hankali sannan ya ƙara lumshe idanun nasa yana kallonta kafin sautin muryarsa ya fito da zurfi.

“Gajiya, tunani, lissafi, aiki, alhini, damuwa sannan ga yunwa ma, su suka dame ni.”2

A cikin zuciyarsa Madaki zai iya rantsewa itace halitta ta farko da ya fara gayawa damuwarsa kai tsaye haka, don ko a wajen likitansa ya kan sakaya wani abun ne don kar ya fito da rauninsa a fili, balle kuma Mubarak da baya taɓa furta masa damuwarsa sai dai shi ya fahimta ya tambaya. Amma a yanzu tare da wannan ƴar yarinyar dake tsaye a gabansa, yana jin zai iya narkewa ma ba tare da ya damu ba, don yana ain yadda zuciyarta ke manta dukkan wani abu dake tsakaninsu in har ta fahimci bashi da lafiya.

Amsar da ya faɗa tasa Jidda ta ɗago hannunta da bai riƙe ba ta ɗora shi a wuyansa har yatsunta suka yi kwana kaɗan kamar masu son zagayowa.
“Amma kuma baka zazzaɓi?”

Muryarta ta faɗa tana cigaba da kallonsa, sai ya saki ɗaya hannun nata ya riƙo ɗayan, ya jawo shi a hankali zuwa ƙirjinsa daidai inda saitin zuciyarsa yake, ɗan nesa kaɗan da bandejin ciwonsa.

“Ina tunanin anan zazzabin yake, don duk abubuwan dana fada miki a cikin nan suke.”

“Har da yunwa?”

STORY CONTINUES BELOW
Ya ɗaga kansa.

“Ina ga har ita ɗin ma, sai dai ba lallai nata na abinci bane. Beside, me kika ci yau?”

Ta nemi janye hannunta kafin ta amsa amma ya sake riƙe shi.

“Naci dambu da rana, yanzu kuma wainar fulawa muka siyo ni da Sadiya.”

Sai da wasu ƴan sakanni suka wuce kafin Madaki ya iya hango abinda yake wainar fulawar, don rabonsa da ya ganta tun sanda suka zauna a Kaduna, a lokacin yana makarantar secondary wata mata ke yi a kitchen ɗin makarantarsu tana siyarwa, kuma tun daga wancan lokacin ba zai iya tuna cewa yaji an ambaci sunanta ba ma balle har ya ganta. Saboda haka ya gyada kansa yana kallon dogon hijabin dake jikinta kafin yace.

“Kin ci dadi kenan da alama.”

Kuma bai bata damar amsawa ba, sai ji tayi kawai ya saki hannun nata sannan ya kamo saman hular dogon hijabin ya zare shi daga fuskarta gaba ɗaya.

“Akwai zafi, ki cire wannan.”

Wani abu da ya shammaci Jidda kenan, zuciyarta ta buga tare da ɗaukewar numfashinta a lokaci guda, saboda bayan hijabin hula ce kawai akanta sai doguwar rigar bacci.

Kuma ƙarin abun shine rigar ta cotton ce mai laushi don haka ta kwanta a jikinta sosai saboda ɗinkin da aka mata, ba sabuwa bace amma kuma bata tsufa sosai ba, irin gumaman kayan nan ne na Makka su Aunty Zainab suka siyo musu ita da Sadiya kasuwa, su kuma sai suka kai aka rage musu faɗin akayi shaping ɗinsu sosai suka tashi daga bunbula-bunbula irin na lukutayen matan larabawa nan, a lokacin har Baddon na faɗan cewar an matse su da yawa don in dai ita tasa ta kwana da ita, to ko ɗebo ruwa zata fita da safe sai Baddo tace ta canja ta ko kuma tasa dogon hijabi mai hannu. Amma yau sai gata a tsaye a kusa da wani namiji daga ita sai rigar da kuma hula kawai akanta.

Don haka bayan kunyar da ta ratsa ta, ruɗani ya haska a cikin idonta sanda yake kallonta tun daga gashinta da ya fito ta farkon hular har jikin nata da idanunsa wanda suka ƙara ƙanƙancewa, sai dai jin baice komai ba yasa wani dunƙulen abu ya wuce a maƙogwaronta kafin yaja hannunta zuwa hanyar ɗakin dashi kaɗai ne baƙo a wajenta.

Kamar falon, a cikin ɗakin ma hasken fitila ɗaya ne kawai ke ci, sai na labtop dinsa dake kunne akan gado alamun wani abin yake yi da ita, screen ɗin labtop ɗin na kallo ƙofa don haka haskenta ya sauka an wasu foodflask dake ajiye akan wani dogon tebur ɗan siriri a gaban gadon, kuma ko bata tsaya kallo ba ta san cewa kayan ɗakin sun haɗu don tun daga tun daga falo ƙamshin iskar ciki ma ba ɗaya ce data ɗakin Baddo ba.

“Bismillah ki zuba mana abinci ni tun safe ban ci komai ba.”

Muryarsa ta faɗa yana kallonta sanda ya saki hannunta a gefen gadon, Jidda ta haɗiye yawu a cikin maƙogwaronta, bayan sanyin A.cn ɗakin da ya shiga ratsa ta, sai kuma wani ɗan nauyi ya biyo baya saboda fahimtar cewa ba zancen dressing ɗin ne kaɗai dalilin kiranta ba, ta manta be  tun da al’amarin ya faru ita ke taya shi bashi abinci saboda hannun nasa baya ɗagowa sosai, kuma a dai cikin masarautar da hayaniyar zaman makokin ba lallai ne dama ya samu mai taya shi, amma ganinsu Baddo sai yasa ta manta hakan kwata-kwata.

Saboda haka ta matsa wajen flask ɗin abincin guda biyu da niyyar zubowa yayin da shi kuma ya juya ya koma kan labtop dinsa. Akwai plates masu kyau da tarin cokula da fork kusan guda biyar a gefe kamar wasu mutane ne da yawa zasu ci, ta dauko gudadaya a cikinsu da kuma cokula biyu sannan ta buɗe flask na farko inda wata jollof ɗin shinkafa ke tashin ƙamshi tasha vegetables da kuma yankan hanta manya manya, zuciyarta ta tabbatar mata cewa duk wanda yayi girkin ba karamin kwararre bane, a ɗaya flask ɗin kuma romon kifi ne na tarwaɗa fari tas dashi sai kamshin kayan girki yake da kuma garlic ba mai yawa ba.

“Abincin kawai ni nake so.”

Muryarsa ta faɗa tun kafin ma ta taba kifin, don haka ta hadiye yawun daya taru a bakinta sannan ta rufe shi ta taso, idan yace shi ba zai ci ba, ita gwana ta gwanaye ta isa ta zuba ne ta koma gefe ta fara vi? Daga an kirawo ta taimako? Saboda haka duk sonta da kifin sai ta ture shi a cikin kanta sannan ƙaraso ta zauna a gefen gadon da yake zaune.

STORY CONTINUES BELOW
“Minti daya kawai bari in rufe wannan.”

Muryarsa ta sake faɗa ba tare da ya kalle ta ba, hankalinsa na kan labtop ɗin da ya dora akan cinyarsa yana danna ta da hannu ɗayan, hasken screen dinta na haskawa a fuskarsa.

Zuciyar Jidda ta matse a take, wata irin matsewa da taji kamar ansa igiya ne an daure zuciyar, Allah ya sani tun sanda alakarsu ta fara gyaruwa, idan tana kusa dashi haka tana kallon fuskarsa… Manta komai take ta manta dukkan wasu matsaloli dake gabansu dama abinda take hasashen zai biyo baya. Sai taji ta kawai a wata sabuwar duniya daban, taji kamar wani ya tsayar mata da lokaci ne ya bata tabbacin cewa abada mai wanzuwa ce.

Zuciyarta na cika da tsananin tasusayinsa da kuma wasu abubuwan da bata san sunansu ba, abu biyu kawai ta sani a cikinsu cewar tana tausayinsa ne saboda ciwonsa, don tana ji masa irin abinda taji game da mamanta a baya… Tana jin kamar ta ƙarasa ta buɗe zuciyarsa gabadaya ta gyara abinda yake ba daidai ba, ta cire ciwon da yake ji a rayuwarsa ta maida shi mutum kamar kowa.

Sannan a yanzu kuma da ta san wani abu game da tarihinsa ta kan hasaso cewa dama zata iya maida lokaci baya ma, ta sami wata hanya da zata nemo masa iyayensa da ƴanuwansa, ta cire kowanne bakin ciki da ya fuskanta a rayuwarsa, farin ciki da dariya su maye gurbin dukkan ƙunci da kukansa. Komai ya dawo daidai ta yadda za’a sami dauwamammen murmushi a gefen kumatunsa sabanin koƙarin boye damuwarsa da yake yi a kullum, sannan bayan haka ma a samu wasu tarin ƴan ƙananan abubuwan da zasu haɗu su maida shi wani Ibrahim ɗin da bai san wani abu ƙunci ba.

Kuma har ta taimaka masa ya cinye abincin nan tunaninta kenan, don ita kaɗan taci tana ƙoƙarin amsa tambayoyin da yake mata game da gaisawarsu da Hajja. Bayan abincin ya ƙare ne kuma dalilin kiran ya taso, yace ta ɗauko wani ɗan ƙaramin akwati dake saman wata chess drawer a gefe wanda da alama daga asibitin aka bashi.

Shi ya nuna mata dukkan yadda zata yi tun kafin ma ta kare kanta da cewar bata iya din ba, yace da ita ya buge ne da ƙofa don haka wataƙila jini ya fito kadan idan tasa au duga ta goge shi sai ta sake sabon bandeji ta rufe wajen. Da farko hannunta rawa ya fara yi don sai a lokacin idonta ya tuna mata da kayan da yake sanye dashi saboda a yanzu tana zaune ne dab dashi har tana taba wani bangare na jikin nasa, wani abu sabo, wani abu daban, wani abu da bata taba hasashensa ba balle har tayi tunanin zata iya.

Ta cire bandejin a hankali yayin da ciwon wajen ya shiga idanunta, bashi da fadi sosai amma karara ake ganin ɗinkin da akayi wa zurfinsa, wani irin ɗinki da yasa tsigar jikinta tashi bakiɗaya sabida tunanin zafin da wajen zai yi, kuma da gaske ne cewar ya buge ɗon don shatin jini nan ya fito bushe a wajen, a cikin ƙwaƙwalwarta sai ta kasa hasko irin zafin da yaji a lokacin da ya buge ɗin, sai dai ba lallai shi ya damu ba, don ko yanzu gashi nan kishingiɗe a gabanta ba alamun ma tana taba wajen a fuskarsa balle har ace yana jin zafi, yana kwance kawai da filo a bayansa yana kallonta kamar a fuskar tata yake gane cewa daidai take yi.

Wani kallo da taji yana neman rikita ƴar nutsuwarta, don tana jinsa har can ƙasan zuciyarta wadda sautin bugawarta ya karu fiye da daidaj, kuma Allah ya sani ta takura ba kaɗan ba, kawai dai anzo gabar da ta san ba zata iya musu bane, don tun a mkarantar dare ta riga ta haddace kowanne hakkin miji akan matarsa, don haka ko ba ba Madaki bane mijinta ta san idan ya sata abu bai dace tayi musu ba. Me Jamila ta gama cewa ne ma yanzu? ‘… Idan tayi masa biyayya ba lallai ya rabu da ita ba..’

“Babu zafi fa.”

A lokaci guda ta tsinto amon muryarsa ya fito a hankali daga can ƙasan maƙogwaronsa wanda ba don tana kusa saahi ba ba zata ji ba, sai tayi ƙoƙarin janyo idonta daga kan ciwon itama ta kalle shi, cikin son nuna cewar aikinta kawai take yi.

“Babu zafi ciwon?”

Ta tambaya da alamun bata gane ba. Sai ya girgiza kansa.

“Kallonki da nake ba zafi, naga kamar kin takura ne.”

STORY CONTINUES BELOW
Wannan karon muryar da tsananin taushi ta fito directly a saitin fuskar tata, don zata iya rantsewa ma taji ɗumin iskar harafan akan fatarta, don haka sai kawai tayi ƙoƙarin cije ƙasan lebbenta a hankali sannan ta karbi shawara mai kyau a cikin kanta… Ta maida idonta kan ciwon da ta gama gogewa ba tare da tace komai ba, don in har zata yi magana ce masa zata yi, ‘Gwara taji zafin kallon da wannan abinda yake ji kamar yana bin fatarta kotawanne ɓangare…’

Hannunta ya ɗauko wani sabon bandejin tare da roll ɗin plaster a cikin akwaitin, kuma wannan karon ba sai ta tambaye shi ba ta riga ta san rufe ciwon kawai zata yi sannan ta manne da plaster kamar yadda yace da farko.

Don haka a hankali yatsunta suka sake sauka akan fatarsa daidai lokacin da nasa ma suka sauka akan tata fatar, don bata lura ko kadan da sanda ya miƙo hannunsa ba, sai kawai ji tayi yatsunsa biyu sun sauka akan wuyanta suna jan wani layi zuwa ƙasa a hankali, babu shiri wani sanyi da bata san daga ina yake ba ya shiga ratsawa jikinta sannan ƙarar bugun zuciyarta kuma ya ƙaru ma fiye da ƙima.

“Baki fada min ba, me su Baddo suka ce da suka ganki?”

Daga can ƙasa, yatsun ƙafarta suka tanƙwashe saboda yadda komai ya sake ninkuwa da fitowar muryarsa dama abinda ya fada ɗin, taji kamar ta yiwa duniyar mutane nisa ne, ta tafi wata sabuwa dashi ɗin ma bai kai ga biyo ta ba.

“Mhm…?” Ya sake tambaya jin ba tace komai ba.
Sai tayi saurin tatattaro ƴar nutsuwar data rage mata sannan ta lalubo muryarta, idanunta na kan yatsunta da suka shimfiɗa bandejin nan a jikinsa kamar tana so ne ya fito da gum da ya mannu a wurin.

“Ban san me suka gani ba, amma suna ta cewa dai na canja.”

Sai ya gyada kansa a hankali har a lokacin yatsunsa biyu na tafiya da dawowa a jikin fatar wuyanta.

“Saboda me suka ga kin canja?”

“Watakila saboda kawai sun daɗe basu ganni bane.” Ta faɗa tana da manne cowon.

“Ba don saboda ina kula dake bane?”

Kalaman suka sake ratsa ƴar nutsuwar ta, suka wargazata kamar yadda yatsun kafafunta da suka dunƙule suka wargaje suma.

Sai kawai tayi haɗiye wani dunƙulen abu a maƙogwaronta sannan ta manna plaster ta ƙarshe a wajen, zuciyarta zata haukace ne, watakila a yau Madaki so yake ya ruguza dukkan wani sauran hankalinta idan ta cigaba da zama a wajen don haka bata bashi amsar da bata sani ba har tayi yunƙurin miƙewa amma sai yayi saurin riƙo hannunta tun kafin ma ta tashin.

“Maijidda…”

Karo na farko a tarihin zamansu, Madaki ya kira ta da sunanta ba inkiya ba, muryarsa can ƙasa yayin da yake murza yatsunta gabadaya cikin nasa, wani abu da yasa Jidda taji watakila abinda take ji ma yafi ƙarfin shirin hauka, bashi da suna ma balle har a samo masa fassara, don har wani abu ne kanar gumi ke tsatstsafowa daga tsakanin yatsunta, musamman wanda yake rike dasu.

“Ina son muyi wata magana ne, dan Allah.”

Sauran kadan yawun dake zarcewa cikin maƙogwaronta ya haɗo da zuciyarta a lokacin nan, ta dago ta kalle shi, don Allah yace? Ko dai bata ji daidai bane? Ta yaya Madaki zai mata wa magiya? Sai ta cigaba da kallonsa kawai da dukkan wani mamaki tana fatan kuma ba laifi tayi ba. Tana jin yadda hannunsa ke motsi a cikin nata kafin muryarsa ta fara magana a hankali.

“Na sani a yanayin yadda al’amura suka kasance tsakaninmu akwai tarin rashin fahimta daga kowanenmu, tun daga ranar dana tafi dake lagos har zuwa yanzu na san akwai wani tunani daban da kike yi a kaina, haka zalika tun daga lokacin nima zuciyata ta wassafa min tarin abubuwa akanki wanda a baya na dauke su a baibai da tunanin wani abun daban.

STORY CONTINUES BELOW
Amma a hankali sai halayya da kulawarki suka yi tasiri wajen canja dukkan rashin fahimtar dana samu akanki, na fahimci ainihin halinki da kuma cewar abinda nake zarginki dashi a farko ba haka yake ba, kuma hakan ya fara ne tun daga maganganun da kika gaya min a ranar dana fara tambayarki har zuwa kan ƴan kananun abubuwan da zuciyata ke tace su tana aunawa da dukkan bayanan dana samu akanki daga waje…”

Jidda bata gama fahimtarsa ba, don mamakin daje cinye ta ya kasa bari ta fahimci ma’anar kalamansa a lokaci guda, sai ya fadi kowacce ya matsa ta gaba sannan take jin ma’anarsu a ƙwaƙwalwarta, shima kuma sai yayi shiru bai cigaba ba, kamar mai bata damar da zata kamo  shi, don yana iya karantar mamakin nata ƙarara a cikin idanunta. A hankali ya saki hannunta sannan ya riƙo gefen fuskata, ya tallafe shi cikin tafinsa yayin da ya shiga shafa gefen fuskar tata da yatsunsa, a hankali kamar hakan ne zai ƙara share masa hanyar da zata fahimci maganganunsa.
“Jidda abubuwa da yawa sun rikice min a yanzu, ina cikin wani halin da ni kaina ban gama sanin abinda ya dace nayi ba, amma duk da haka a cikin zuciyata na sani cewa har ga Allah ina son gyara rayuwarmu tare, domin kin inganta ni ta hanyoyi da dama, na samu tarin abubuwan da ban taba sanin yaya suke ba ta dalilinki.

Don haka na yanke shawarar gaya miki hakan ne don in irin naki tunanin akaina, anan muka faro komai a cikin wannan wajen ƙaddara  ta haɗa mu, shi yasa na ture komai na kira ki zuwa nan ɗin, na rufe idona daga duk tarin idanun mutanen da zasu iya cewa wani abu, nake son mu tsayar da magana guda daya mai ɗorewa, don wallahi ban iya ƙumbiya-ƙumbiya ba Jidda, idan nace zanyi abu komai rintsi da wuya bana taba ja da baya sai dai in har daga abun aka sami matsala, haka na taso naga mahaifina yana yi kuma ban taba canjawa ba…”

A wannan gaɓar sai ya sake yin shiru sannan ya janye hannunsa daga yadda ya tallafi fuskarta, ya dawo dashi zuwa jikinsa, ya zura shi cikin aljihun wandon shaddarsa, a hankali ya fito dashi a dunƙule alamun ya riko wani abin sannan ya janyo hannunta dake riƙe da roll ɗin plaster nan da bata mayar ba ya bude shi ya ɗora abinda ya dauko ɗin a tsakiyar tafinsa… Wani abu ƙarfe, wani abu daya ɗauki sanyin ɗakin ya ratsa har cikin jijiyoyinta, sannan wani abu da ya haddasa bugun zuciyarta tun kafin zuciyar ta gana tantance mene ne.

Yana kallon yadda gashin idanunta suka sauka akan hannayen nasu tun kafin ya janye nasa, alamun tana son tabbatar da abinda take tunanin shine, kuma yadda gashin idon ya hade dana ƙasansa kamar ta rufe idanun ne ya ƙara masa jin wani abu tamkar kasala a jikinsa, yaji ɗimin numfashinta na sauka akan hannunsa yayin da wani abu tamkar wutar lantarki ke harbawa tsakanin hannnusa da nata, a dole yayi saurin janye hannun nasa kafin ya cigaba da magana.

“… Kin gaya min cewa kin shigo dakin nan ne don neman abinda kika yar a cikin kayana, kuma tun wancan lokacin da na duba na ganshi zuciyata ta fara yarda dake ba tare da nayi la’akari ba, wata irin yarda da ta mamaye dukkan tunani na ta hana ni sukuni tun kafin ma in fara samun kulawarki, ban san menene wannan abin ba Jidda, amma na san cewa yana da mutukar muhimmanci a rayuwarki tunda har kika iya zuwa har nan wajen nemansa, kuma nima a yanzu zan iya cewa ya zama abu mai muhimanci a wajena, tunda har ta sanadinsa ƙadarar haduwata dake ta faru.”

A lokaci guda jijiyoyin cikin idon Jidda suka ɗauko mata hoton abinda ya ajiye a cikin hannun nata.

Fullo.5

Ɗan zagayayyen dunk’ulen zinaren da mahaifyarta ta bata.

Ɗan zagayayyen dunk’ulen zinaren da a baya yake tare da ita kodayaushe kamar mutum da inuwarsa.

Fullon da Suraj ya fizge shi a ranar da rayuwarta ta fara canjawa zuwa ƙaddarar da ubangiji ya halitta a rayuwarta, wata ƙaddara data fara da wani abu mara kyau, mai tsananin duhun da zai iya tarwatsa duk wani ragowar farin ciki a rayuwarta zuwa wani abu kuma mafi kyawu da koda ubangiji zai barta da zaɓi ba lallai ta zaɓo kamar shi ba, don bayan ma’anar da mutane ke danganta ƙaddara da ita, tabbas ne cewar ƙaddarar tana iya daukar siffar alkhairi ma…

STORY CONTINUES BELOW
Don a yanzu ta tabbata ta sami amsar dukkan tambayoyin dake yawo a cikin kanta.

Ta san irin tata k’addarar…
Ta san daga sanda ta fuskance ta…
sannan ta san a yanayin da tazo ma..
Mai kyau ce, ba akasin hakan ba.

Kuma a yanzu da take sauraron wadannan maganganun daga bakin Madaki, ƙwaƙwalwarta ta riga ta gama cakudewa da mabanbantan tunanin, don da farko ma da kyar iya nemo iska a ƙirjinta saboda tsabar mamaki da kaɗuwa, don tabbas da ace wani ya aiko ya gaya mata hakan to kuwa ba zata taba yarda ba, ba zata taba yarda cewa kamar ita wai a dan zamansu ta kyautata rayuwarsa kamar yadda yake fada ba, ita da take ganin yana da komai, yana da dukkan wata hanyar jin dadin rayuwa ita me ta isa ta gyara a tare dashi.

Amma kuma sai zuciyarta ta yarda din, sai taji ta ture dukkan wani kokwanton ta a lokacin, ta yarda da abinda shi da kowa ma ke faɗa cewa aurenta dashi wani rubutaccen al’amari ne daga Allah kuma ƙaddarar data hada rayuwarsu tamkar zanen dutse ce… Babu wani abu da ya isa ya canja ta.

Sai dai ita ba zata iya irin wannan bayanin nasa ba, tsananin kwarjininsa ba zai barta ba don duk iya surutunta ta san cewa tana da iyaka a wasu wajajen, wajaje irin wannan lokacin da take ganin ko yatsanta ba zata iya ɗagawa ba sai an bata umarni, to har yaushe kuma zata iya kallon idanunsa ta gaya masa cewa dukkan abinda ya zayyano akanta itama tana jinsu game dashi? Ta yaya zata iya gaya masa irin canjin da ta samu a rayuwarta da kuma wani matsayi da farin ciki saboda dalilinsa? Ta yaya zata gaya masa cewa a kullum tana kwana ne da taraddadin ranar da zai iya rabuwa da ita… Idan ta tashi da safe ta ganshi kuma tana jin kamar kasusuwanta zasu kakkarye ne saboda wani irin abu dake ratsa cikinsu, idan kuwa ya riƙe ta manta komai take ta manta kowa sai ƙoƙarin yadda zata yi numfashi kawai.

Kuma idan har wannan amsar yake nema, to zata iya cewa bayan yarda dashi tana sonsa ma, don ko lokacin da take cewa tana son Suraj gani take kawai waƙa ce a baki, saboda a yanzu ko magana Madaki ya mata, da wannan muryar tasa da ta fita daban a cikin ta mutane, mai tsananin zurfi da taushi, zuciyarta kan cika da wani irin abu ne mara misaltuwa…

A cikin shirunta da wannan tunanin, babu abinda zuciyarta keyi sai hamdala, don ta yarda cewa Allah ya daraja rayuwarta, ya bata kaso mai yawa daga cikin ni’imomin duniya, tunda ta rabu da iyayenta lafiya sannan ta sami miji nagartacce mai ɗauke da abubuwan da kowacce mace zata so a rayuwarta. To meye riba a cikin rayuwar macen dama? Ta yiwa iyayenta biyayya, ta kyautata zamanta da mijinta sannan ta tarbiyanci ƴaƴan da zata haifa… Kuma idan har Allah ya bata damar biyu daga cikin wadannan abubuwan to kuwa dole ta gode masa, tsananin godiya ta hanyar sake kyautata ibadarta da kuma kaucewa duk wata hanya ta saɓa masa.

A lokacin ne kuma, sanda take wannan tunanin Madaki yayi abinda bata yi tsammani ba,abinda ya kara tabbatar mata babu wasa a ciki, da hannunsa ɗaya dake riƙe da nata ya jawo ta a hankali zuwa kan gadon, kusa dashi koma tace cikin jikinsa bakiɗaya, kanta ya sauka a gefen kafaɗarsa mara ciwon yayin da kafafunsu suka hade wuri guda, wani kusanci fiye da na asibitin nan.

Jidda taji kamar numfashinta ya yanke gabadaya yayin da bugun zuciyarta ya ɗauke ta zuwa wannan duniyar ta gaba, ta can gaban wadda ta saba shiga a duk lokacin da suke tare, har taji ta ma tana shawagi a iska kafin ta isa, don haka sai ta runtse idanunta duka biyu a yayin da wata irin kunya da taraddadi suka zagaye ta.

“Allah zai ara mana isashshen lokacin da zaki yi ta tunani kina auna ni a mizaninki, don haka kar ki takura kanki a yanzu, let’s sleep na san kema kin gaji da yawa.”

Ya faɗi hakan a lokacin da hannunsa mai lafiyar ke shiga cikin hularta, dogwayen yatsunsa suka zurma cikin gashinta dake tsefe, wani abu mafarkinsa, wani abu daya daɗe yana son yi, fuskarta ta sake mannuwa da faffadan ƙirjinsa yayin da ya kwantar da fuskarsa a saman hular tata, hancinsa na shaƙar ƙamshin turaren dake jikin hular.va hankali ya sauke muryarsa zuwa ga raɗa-raɗa sannan yace.3

STORY CONTINUES BELOW
“Na sha addu’ar Allah ya bani wani sabon fata a rayuwata Jidda, wani sabin abu daban da inganta rayuwata kuma sai a yanzu nake ganin cewa Allah ya amsa addu’ata, zuwanki ya bani tarin abubuwan dana dade ina nema a rayuwata, kin maida ni cikakken mutum sannan ki mamaye zuciyata ta yadda ban ma san ina sonki ba sai dai in tashi a kowacce rana with the thought that I’m going crazy.” (Da tunanin cewa haukacewa nake.)1

A hankali ya shiga motsa yatsunsa a cikin gashin nata, taushinsu na ratsa fatarsa yayin da hakan yasa ta kara matsawa cikin jikinsa hannayenta dunƙule a ƙirjinsa sannan fuskarta manne da wuyansa yana jin ɗumin fitar kowanne numfashinta, wani abu da ya ƙara masa shsuƙin kaunarta kenan.

Yana da tsari kuma baya tab’a gaggawa a al’amuransa, don haka zai bita a hankali zai bari tayi nazarin maganganunsa ta fahimce shi har ta yankewa kanta shawara ba tare da ya ingiza ta ba, sai dai kawai zai bi duk hanyar da zai sa ta bude masa ƙofar shiga zuciyarta don ya tabbatar mata da cewar duk abinda ya fada da gaske yake kuma baya taba ja da baya a maganganunsa.

A hankali ya cigaba da motsa yatsunsa cikin gashinta yayin da yake jin kamar tana narkewa ne a jikinsa.

A wannan lokacin, a cikin zuciyarsa, sai addu’arsa ta canja…

Ya Allah!
Ya Rabbi!
Nagode da taimakonka,
Nagode da addu’ata daka amsa,
Nagode da ka tserar da rayuwata daga ƙalubalen dana ke ciki,
Nagode daka azurta ni da rahamarka,
Nagode da ka bani wani sabon fatan a rayuwata ya Allah!

***

Washegari.
Murtala Muhammed International Airport, Lagos.
09:08Am

“Ina jinka Donnovan…”

Muryar Mubarak ta faɗa a lokacin da yake nufar hanyar terminal don shiga jirgin da zai kaishi Kano, daga nan zai ƙarasa Kiyari inda zai je yiwa Madaki da Mai martaba gaisuwa. Donnovan shine ɗan sandan daya danƙawa case din Salwa a ranar daya kaita police station din nan.

“Yallaɓai mun gama tambayarta, da farko da tayi taurin kai amma bayan an tambaye ta, ta fada mana komai dalla-dalla.”

“Ina jinka.”

Ya kara faɗa a lokacin da wani security a kofar terminal ɗin ya karbi ticket ɗin hannunsa yana dubawa.

“Tace ita da wata kawarta ne mai suna Naja’atu suka hayo wasu ƴan bindiga anan cikin lagos ɗinvda zummar cewar su kashe yarinyar da zasu ganivtare da wanda aka harba ɗin, to shine sai su ƴan bindigan suka yi kuskure suka sami namijin a maimakon macen. Yanzu haka kuma ta kwatanta mana inda kawar tata take a can Abuja, har an aika da jami’an tsaro za’a kamo ta, saboda tace ita ta san inda su ƴan bindigan suke don ita ta hayo su.”

Mubarak ya karɓi ticket dinsa da securityn ke bashi bayan ya gama dubawa sannan yayi gaba yana gyara zaman ƴar ƙaramar jakar matafiyan dake saƙale a hannunsa. Wani irin huci ne ke fitowa tun daga ƙasan zuciyarsa har zuwa iskar da yake fitarwa.

Salwa ta riga ta jawo masa abinda yake jin har ya bar duniya ba zai daina jin zafinsa ba, don a yanzu babu yadda ya iya dole ne Madaki ya san da zancen nan tunda aikin ya zama na hukuma sai sun tuntuɓe shi, kuma ya kasa wassafa yadda hakan zai kasance, ya kasa hango ta yadda zai iya cigaba da rayuwa a gefen Madaki da wannan nauyin abun kunyar? Yaya ma shi ɗin zai ji idan har yaji Salwan da take ƙanwarsa ce mai aikata wannan ɗanyen aikin?

Shi yasa ko a shekaranjiya da suka hadu bayan yaje gidansa yi masa sallama, babu yadda Madakin bai yi ba akan sanin damuwarsa amma ya kare kansa da cewar bashi da lafiya ne kawai, Allah yaso ma bai ga yarinyar ba, da bai san wane irin dakon kunya zai ɗauko ya dawo ba, sauƙin abun kawai shine bakinsa bai riga ya furta zarginsa a wancan lokacin ba, zuciyarsa ta gargade shi bai yi abinda zai zamo silar rabuwarsa da Madakin kwata-kwata ba, don idan har da ya furta cewa ita yake zargi a yanzu kuma aka gano kanwarsa ce, baya jin shi kansa zai taba yafewa kansa balle kuma wani a gefe.

A yanzu so yake ya koyawa Salwa hankali, so yake ya dauki mataki mai tsauri akanta, ya tsoratar da zuciyarta da wata irin razanarwar da zata san cewa bai ɗaga mata kafa tun farko don ba zai iya ba, sai don ya bata ɗimbin damar da zata gyara kurakuranta da kanta, amma tayi sake wannan damar ta subuce don haka yanzu filin nasa ne, shi zai koya mata hankali ta wata hanyar da ko mahaifiyarsu data rasu baza ta iya ba. Shi yasa ya nemi da ƴansandan su boye sunanta wajen gayawa Madaki ainihin wacece mai laifin, don baya so ko kaɗan a sami wani akasi wajen abinda yake son aiwatarwa. Yace maimakon ‘Salwa Umar’ a maida sunan ‘Salma Umar.’

“Yanzu what’s next kenan Donnovan?”

Ya tambaya a cikin wayar bayan wannan ɗan gajeren tunanin.

“Zamu kira shi victim ɗin ne mu gaya masa dukkan abinda yake faruwa, saboda ba zamu iya moving case ɗin zuwa kotu ba sai da izininsa.”

Mubarak ya gyada kansa.

“Shikenan ka kira shi ɗin.”

“Okay yallaɓai, kuma zamu canja sunan kamar yadda kace, sannan kamar yadda ka nema kuma na turo maka hotunan nata ta whatapp.”

Sai ya sake gyada kansa.

“Shikenan, nagode zan duba.”

Da haka wayar ta ƙare kuma kafin ya karasa wajen da za’a sake duba tikitinsa, sai kawai ya tsaya a tsajiyar wajen ya buɗe cikin wayar tasa ya nemo application ɗin whatapp, yana shiga cikinsa kuwa messages suka shiga tunkoɗowa kamar ruwa, wani akan wani, sai dai yana gano nambar Donnovan ɗin ya ture duk sauran ya bude nasa saƙon.

Hotunan guda biyu ne wanda suka bude a take, kuma yana shiga cikinsu zuciyarsa ta karye a taken.

Saboda ba don kayan da yasan ya kaita police station din nan ne a jikinta ba, zai iya rantsewa da Allah cewa wannan ba kanwarsa bace… Babu kammanin Salwan daya sani ko kadan a fuskarta wadda ta kumbura suntum! Idanunta ma sun kumbura sun koma kanana, gefen bakinta ya fashe har jini na zuba sannan kumatunta ta kowanne ɓangare yayi baƙi alamun duka. Ɗaya ita ƙadai ce a tsugunne, yayin da ɗayan kuma take gaban wata mace ƴar sanda dake riƙe da wani katako a hannunta…

A lokaci guda sai wata kwalla mai ɗumi ta cika idanunsa, me yake tunani ne? Me ya same shi? Komai lalacewar Salwa fa kanwarsa ce, uwa ɗaya uba ɗaya, irin jinin dake yawo a jikinta shine a nasa, shin duk lalacewarta ya dace da hannunsa ya kaita inda za’a lahanta ta haka? Me ƴanuwansa zasu ce idan suka ga hakan? Ko kuwa inda iyayensu zasu dawo duniya a yau zasu goyi bayansa akan hakan ne?6

Ina imaninsa da tausayinsa suka tafi? Itace fa ƴar kanwarsa guda jal a duniya, wannan ƴar ƙanwar tasa da mahaifiyarsu ta rasu a wajen haihuwarta, wajen kokarin kawo ta duniya… shin inda za’a haska mata komai a kabarinta yanzu zata yi alfahari dashi? Zata goya masa ba tace abinda yayi daidai ne? Zata ce ya kyauta daya azabtar da halittar data ransa ranta wajen ƙoƙarin kawo ta duniya?

Babu shiri sai kwalkar data cika a idanunsa ta gangaro kan kumatunsa, don haka bai san lokacin da hannunsa ya fita daga cikin hotunan ba, ya koma wajen kira, hannunsa ya sake nemo nambar Donnovan ya kira a take, kuma bugu daya biyu sai aka ɗauka.

“Donnovan, kar ka canja sunan, kace masa Salwa Umar ce, ƙanwar Mubarak!”15

***Jidda ta buɗe idanunta a hankali cikin madaidaicin hasken ɗakin daya baje a iska, ta fahimci cewa lokacin safiya ne amma kuma a cikin sakannin da suka biyo baya sai ƙwaƙwalwarta ta kasa tantance wajen da take, idanunta kaɗan suke a buɗe alamun bata gama wartsakewa sosai ba amma duk da haka tana iya ganin dishi-dishin abubuwan dake zagaye da ita.+

Gadon ƙato ne, filon mai laushi sannan ga hoton wasu labulaye masu kyau da take hangowa daga ɗan nesa kaɗan, kuma ba kalar labulayen ɗakin Baddo bane balle inda ta saba kwana a lagos, saboda haka ta sake ƙifta idanunta a hankali tana jin yadda jikinta yake a dunƙule, ƙafafunta haɗe da cinyoyinta sannan cinyoyinta haɗe da cikinta, kamar da wani abu ya tare ta ne a yanzu kuma da babu shi sai take jinta sakayau.2

A hankali ta ƙara maida idonta ta rufe sannan ta gyara kwanciyarta tana ƙara duƙunƙunewa cikin bargon da take lulube dashi, baccin ya tafi a idanunta amma duk da haka bata son tashi, yanayin hasken ɗakin da kuma iskar ciki data dauki wani sanyi ba mai yawa ba ya mata dadi sosai, don haka ta sake gyara kwanciyarta hancincinta na ƙara shiga cikin filon yayin da wani sassanyan ƙamshi ya shiga kurɗawa cikinsa.

Sakan daya, biyu, uku… Kafin ta fahimci ƙamshin na menene da kuma inda ta sanshi, don haka lokaci guda ta miƙe da wani irin sauri a tana yaye bargon, kuma babu wata kwana-kwana ƙwaƙwalwarta ta fahimci inda take da kuma yadda akayi tazo ɗin, idanunta suka shiga wulgawa koina na bangaren ɗakin sai dai babu wanda take nema din, fita yayi kenan? Ya barta ita kadai? Ina ya tafi? Karfe nawa ma? Tambayoyin suka ɗarsu a ranta sanda idonta ya kai kan bedside drawer inda labtop dinsa ke kunne a jone jikin charger, daga gefe kuma wayoyinsa ne guda biyu.2

Yana nan kenan, tunda dai ai ba zai fita ya bar wayoyinsa a ɗaki ba, don haka da sauri ta matsa ta danna wadda hannunta ya fara kaiwa don ganin lokaci. Ƙarfe tara har da ƴan mintina na safiya… Innalillahi wa’inna ilahir raji’un! Ita mai cewa ƙarfe bakwai daidai zata tafi? A wajensu Baddo ai yanzu rana ta take har ta kai tsakiya ma, ba shiri ta sauko da ƙafafunta ƙasa kuma saura kadan tayi ball da flask ɗin abincin nan na jiya tsabar sauri, har ta nufi hanyar ƙofa sai kuma ta tuna babu ko ɗankwali akanta, don tun bayan sanda Madaki ya zame ta da kanta bayan dun idar da sallar asuba bata ƙara ganinta ba.

Wani abu ya ratsa cikin kanta da ta tuno yadda ya sake rike ta a jikinsa yana saka hannunsa cikin gashinta, wani abu daya hargitsa tunaninta kenan ta manta komai balle har tayi tunanin tafiya a wannan lokacin, don a yadda ta tsara tana yin sallar asubar zata kama hanya tun kafin ma haske ya bayyana mutane su fito, amma yadda ya sake rungumeta suka koma gadon nan sai ta nemi wani sauran tunaninta ma ta rasa. Kuma saukinta ɗaya shine har a lokacin bai nemi amsar tambayoyin abinda ya gama gaya mata jiya ba, don Allah ya sani har a yanzu bata gama jin nauyinsu a kanta ba ma balle har ta fitar da amsar da zata iya bashi.3

Kuma un tana tunanin zai ce da ita wani abu har ta daina, ta tsaida zuciyarta kan yadda hannayensa ke ratsa gashinta da kuma sautin fitar numfashinsa kawai, a haka har bacci ɓarawo ya ɗauke ta wanda bata farka ba sai yanzu… Yanzun da take ƙarfe tara har da mintuna na safiya.

Babu shiri ta juyo ta koma can wajen mudubi inda dardumar da suka yi sallah take, daga hijabin sallar kuwa har hular suna nan, sai dai kafin ta sunkuya hankalinta ya kai kan mudubin dake gabanta kuma take idanunta suka zare a lokaci guda, ba wai don ganin fuskarta ba sai don ganin gashin kanta wanda ɗan laushin da yake dashi ya taimaka wajen sawa bai hargitse sosai ba, amma ba abinda ta lura dashi din ba kenan, jelolin kitsonta na gefe gabadaya babu kitso ba alamarsa a jiki sai gashi kawai buzu-buzu wanda yawansa da yafi tsawonsa yasa ya tashi sosai…4

STORY CONTINUES BELOW

Kamar mai son ƙara tabbatar da abinda ta gani, sai ta karkata ta sake kallon mudubin, ai kuwa hoton bai canja ɗin ba, an tsefe kowacce jela zuwa daidai inda kitso ke hawa kan fata, amamaki ya shiga cinye ta daga inda take tsaye, ita bata son meye damuwarsa da gashi ba amma ashe kenan har tsifa ya iya? amma sanda ta tambaye shi kitso ya bita wani mugun kallo kamar tayi sabon da zai halakar dasu.2

Sai kawai tasa hannu ta tufke gashin gabadaya cikin ƴar jela ɗaya sannan ta sunkuya ta ɗauki hularta da hijabinta, ko bata ganshi ba tafiyarta zata yi, ai duk rashin hankalinta ta san nauyin ido da kawaici, don Baddo tace tazo ta kwana ai hakan yana nufin ba ta kwana ta yini bane, don jiya har ƴanuwanta na cikin gari ta kira a waya duk sun ce zasu shigo a yau don su ganta, to kuwa ai ba zata ji dadi su fara zuwa bata nan ba, sai ace musu me? Ta taho wajensa? Wannan abin kunya har ina?1

Ta sanya hularta a lokacin da take wannan tunanin, kuma nauyin tunanin ya dawo mata da zagayen halin da take ciki, ya taso mata da wani dunƙule farin ciki ya taso daga can ƙasan zuciyarta, wani farin ciki da ya tabbata a jiya kawai amma ya bude idanunta ga tarin abubuwa, yasa sai yanzu take gane wasu abubuwan da ta dauka shirme a baya ko kuma wanda bata taba maida hankali akansu ba.

Misali wani lokaci da Baddo ke gaya mata cewa idan yaro ko yarinya sun addabi mutane da rashin ji ko ba hankali, to aure ake ayi musu nan da nan sai kaga sun nutsu, a wancan lokacin kawai alaƙanta wannan zancen kuwa tayi da camfi irin na tsofaffi, don a lissafinta ta yaya za’ace iyaye su raini mutum tsawon shekaru baiyi hankali ba sai don rana tsaka anyi masa aure kawai?

Soyayya tana daya daga cikin abubuwan dake juya duniya…. wannan yardar kuma ta Aunty Zainab ce a wani lokaci da take basu labarin wani malamin darasin Hausa a makarantar sakandiren da tayi, tace sun karanta hakan ne a cikin wani labari daga littafin ‘Dare dubu da ɗaya’ sai aka dinga jayayya har wasu daga cikin ƴan ajin nasu suka ce basu yarda ba, saboda haka sai malamin ya sanya gasar muhawara a tsakaninsu suka yi ta a cikin ajin, wanda daga ƙarshe masu goyon bayan hakan ne suka lashe… Sai dai a lokacin da Aunty Zainab din ke basu wannan labarin itama tayi shiru ne kawai don kar tayi musu da ita, amma tana layin masu ganin cewa hakan zance ne kawai na bogi.

Amma wai a yanzu, tsakani jiya da yau, cikin ƴan awanni kawai sai gashi tasirin wasu kalamai ya wanke zuciyarta bakiɗaya, yasa tana jin ƙamshin gaskiya a ire-iren wannan zantukan, saboda a yanzu abinda take ji a zuciyarta bashi da suna balle ya misaltu, kawai dai ta san cewa watakila babu abinda ya kai daɗi a duniyar nan ace ka faɗa soyayyar wanda zuciyarka ta aminta dashi kuma wanda ya fito ƙarara shima ya furta tasa ƙaunar gare ka.1

Cewa yayi yana sonta, tun shi kansa bai ma sani ba, tun yana jin kanar haukacewa yake…

Ba shiri wani faffadan murmushi ya sauka a leɓɓenta, me yafi wannan daɗi ne wai? Me yafi kaji zuciyarka ta dagargaje da shauƙin kan wani halittar da shima tasa zuciyar ke gaya masa alkhairi akanka?1

Kawai matsalar daya ce, har yanzu zuciyarta tsoro take ɗan yi, tana gargadinta cewa wannan matsayi ne da yafi ƙarfinta, kamar labari ne ko kuma ma tatsuniya wadda ake cewa ƴar bora ta auri ɗan sarkin nan, don Allah ya sani duk rashin hankalinta ta riga ta san cewa Madaki yafi ƙarfinta ta kowanne ɓangare, ba ma ita ba yafi tarin mata a samanta da yawa wanda suka fi ta komai, don banda zancen ciwonsa babu wata tawaya tare dashi balle ace ai don hakan zata iya samunsa.1

Kamar a lokacin da tana makaranta, akwai wani mai tireda dake siyar musu da irin biscuits da chocolates din nan na ƙasar turawa da larabawa, sai dai duk sun wuce kwanakin da ake sa ran cewa suna da inganci, sunyi expire daga kamfani amma tunda dai ɗanɗanonsu bai gama canjawa ba, sai yazo ya siyar musu da arha da cewar saboda wannan tawayar su ƴaƴan talakawa sa samu. Amma duk da haka ba zata iya kwatanta hakan da Madaki ba, don tayi imanin ko ciwon hauka ne dashi mata fiye da ɗari zasu zo su tsugunna suna roƙonsa ya aure su.

STORY CONTINUES BELOW

Shi yasa tun a baya take gargaɗin kanta da cewar abu ne mai sauki ya rabu da ita, kuma a yanzu ma duk da cewar ta yarda da maganganunsa ta cire dukkan kokwanto a zuciyarta, tsoron da take ji bai barta ba, ta kasa yarda cewar wai yana roƙonta ne da su ƙare rayuwarsu tare, tana jin kamar ba gaske ba, don ko bahaushe ai yace ‘kwarya tabi kwarya…!’

Wannan hasashen wasu mutane ne kawai Jidda, Allah baya dorawa bawa abinda ba zai iya ba, tunda har ƙaddara ta hada ki da mutumin nan to kuwa ba abinda zai gagare ki, ki murje idonki kawai ki karbi abinda ƙaddara ta baki ki inganta rayuwarki ki zama matar gida, ai kowa da haka ya fara don haka kema baza ki kasa ba… Wannan barin zuciyar tata wanda yake madugu uban tafiya a komai ya bata wannan shawarar.2

Daidai lokacin da ta juyo ga barin kallon mudubin don fita daga ɗakin, kuma a daidai lokacin da ƙofar ɗakin ta buɗe, Madaki ya sanyo ƙafafunsa sanye daxwasu kwyan da bata taba ganinsa dasu ba, iri-iren dai yadikan da yake sanyawa ne, masu laushi ko a ido, dinkin fitted rigar bata kai gwuiwa ba, sannan kalar yadin light brown sosai mai haske, hasken da ya tafi daidai da fatar jikinsa da kuma fuskarsa da ko makaho zai shaida cewa yayi wanka.

Kuma kallonta yake kallo irin wanda ake cewa kallon tsaf ɗin nan, tana jin saukar idanun nasa koina a jikinta kamar wani ruwa mai zafi, saboda haka sai kawai ta haɗiye wani abu a maƙogwaronta sannan ta sunkuyar kanta kaɗan hijabin nan na riƙe a hannunta.

A hankali Madaki ke nazarinta daga inda yake tsaye yayin da a cikin zuciyarsa yake jin kamar a yanzu yake ganinta ko kuma ba tare suka kwana ba, sannan daga gefen zuciyarsa kuma wani abu ne ɗan mitsitsi kamar taraddadi na tunanin irin amsar da zai samu daga gare ta akan maganganun da ya gaya mata jiya, gani yake kanar wannan ƙanwar Habibun itama zata iya kin yarda dashi duk da cewar waccan tana da dalilin ta na cewar dama auren kudi take da niyyar yi, don ta samu wanda yafi shi kuwa babu dalilin da zai sa ba zata ajiye shi a gefe ba. Don haka abinda zuciyarsa ke taraddadi shine dalilin da ita kuma zata kafa idan har tunaninta bai ba ta goyon baya akansa ba.

Shi yasa yaji baya son ya matsa wajen sanin amsarta da wuri, so yake sai yayi dukkan iya kokarinsa wajen cusa kansa a zuciyarta, ya koya mata yadda zata so shi dama yadda zata wahala in har basa tare da juna, ta yadda zuciyarta zata fi ƙarfin kowanne irin abu ma da tunaninta zai bata akansa. Don Allah ya sani a yanzu da ya samu aka gurguɗa aka yi wannan auren, baya jin yana da lokacin sake ɓata lokacinsa akan wata mace balle har yayi tunanin sake ɗawainiyar aure. Jiddan dai da ya samu a yanzu ita zai shimfida ƴar duniyarsarsa da ita har zuwa yadda Allah ya ƙadarto rayuwarsa a gaba kuma zata kasance.

Don haka a lokacin da yaga ta sunkuyar da kanta, sai ya ajiye takardun dake riƙe a hannunsa kan wani ɗan tebur a gefe sannan ya ƙarasa gabanta a hankali.

“Kin tashi?”

Muryarsa ta fito ƙasa-ƙasa yana kallon fuskarta da bata kallonsa.

Kuma amon muryar tasa yasa Jidda ambato salati tun daga farko har ƙarshe a cikin ranta, wai har yanzu bai fahimci yadda kwarjininsa ke cika dukkan tunaninta bane? Bai san cewa dukkan wata dauriyarta akansa rauni take da wannan freshness din da fuskarsa keyi da safe bane? To me yasa kuma zai sassauta muryarsa haka? Ko dai so yake su raba irin nasa ciwon zuciyar tare ne? Ba shiri ta sake haɗiye yawu a hankali sannan ta tattaro ƴar nutsuwarta.1

“Barka da safiya…”

“Mun gaisa, mu ƙara?”

Ya sake tambaya yana ɗan leƙo da kansa kaɗan kamar mai son lalubo idanunta dake kallon yadda ƙafarsa ke tsaye dab da tata.

“Yaya jikin naka?” Ta wayance da tambayar tana jin sanyin turarensa a hancinta.

Kuma watakila ganin ba zata ɗago bane yasa kawai ya ƙaraso da kansa ya jingina shi da saman goshinta sannan ya fitar da iska daga cikin hancinsa a hankali har hakan ya nuna akan maƙogwaronsa, sannan kuma kamar koyaushe ya lalubi yatsunta wanda bata rike hijabin dasu ba.

STORY CONTINUES BELOW

“Hannunki mai albarka ne Babydoll, tunda kika taɓa ni komai ya daina ciwo.”12

Babu shiri Jidda ta gyara tsayuwarta saboda ƙafafunta da taji na neman gagarar ɗaukarta, wanda hakan ya daɗa sanyawa goshinta ya gogu da nasa.

Babydoll… Babydoll… Sunan ya amsa amo a cikin kanta, ya sauka a wata kwana can sannan yayi zaman daɓaro kamar dama an ƙirƙire shi ne saboda ita ɗin, don a yadda gabanshi a lokacin ma bata ga banbancinta da ƴar tsanar ba, amma duk da haka sai tayi ƙoƙarin finciko hankalinta daga wannan kwanar ta dawo shi gabansa.

“Allah ya ƙara sauki, dama zan tafi ne.”

“Ina?”

Ya tambaya a lokaci guda, sai kuma ta rasa me zata ce, don ta sani a ƙaidar hankali kamata yayi ta tambaye shi ba ta yanke hukunci ba.

“Naga rana tayi ne, to shine nake son inje in shirya.”

Taji alamun ya fahimci me take nufi, saboda haka sai yayi baya da fuskarsa sannan ya saki hannayenta, yatsunsa na hagun suka lalubo ƙasan haɓarta a hankali sannan yayi nasarar ɗago da fuskarta ta kalle shi.

“Kin manta ne kayanki suna nan?”

“Wai anan zan shirya?”

Ta ture komai, ta ture abinda ke ratsawa daga yatsunsa zuwa fatar tata ta tambaya.

“Ko zaki ɗebi kayan ki tafi dasu can?”

Bata fahimci shaguɓe a cikin tambayar ba sai ta cire fuskarta daga hannunsa sannan ta ɗaga kai.

“Eh zai fi dan Allah, kaga rana tayi, yanzu idan na koma wajensu Baddo me zan ce?”

Yadda take maganar so innocent, yadda lebbenta ke motsawa yana haɗuwa dana samansa, yadda idanunta ke haskawa da wani abu kamar roƙo yayi barazanar tsaida bugun zuciyar Madaki, yaji kansa ya kulle babu wani abu mai muhimmanci dake gudana a tunaninsa, yaji shi free! Kamar ya sauke dukkan wani nauyi na duniya a kansa Jiddan ce kaɗai a gabansa, daga ita sai buƙatun zuciyarsa… Saboda haka sai kawai ya sunkuyo a hankali ya ya sake haɗa fuskarsa da tata, goshinsa ya sauka a tsakanin girarta kuma kafin tayi wani motsi ya sanya bakinsa a daidai gefen leɓɓenta, wani waje dab kuma can ƙarshe…

“Gaya musu zaki yi kice Madaki ne ya tsare ki, ke kuma sai ki kasa yi masa musu saboda mijinki ne…”3

Yatsun ƙafar Jidda suka dunƙule waje guda, shaukin data ji fiye da lokutan baya ya kama ta, don wannan abin sabo ne, sabo fil a cikin ƙwaƙwalwarta, taji komai na canja mazauni a cikin kanta, taji tarin abubuwa na sabunta kansu a ƙwaƙwalwarta, kamar ana sake haifarta ne, kamar kowacce jijiya tana warewa cikin ƴancinta.

Kuma bai matsar da fuskarsa ba sai ya cigaba da kallon idanunta dake rufe, nasa na haskawa da wani abu kamar roƙon da bai san ta yaya zai furta ba, kuma a lokacin ne Jidda ta yanke shawarar buɗe baki ta roke shi cewar ya daina hukunta zuciyarta da wannan sabon al’amarin, sai dai watakila shi ya ɗauki hakan ne a matsayin amsar rokon da bai furta ba…

A hankali ya haɗe lips ɗinsa da nata cikin wani irin salo, wani irin abu da yasa ba shiri Jidda ta miƙe kan yatsunta sannan ta riƙo gaban rigarsa, ta cukwuikuyeta cikin hannayenta yayin da ƙarar bugun zuciyarsa ke amsawa akan hannayen nata, wanda bayan shi kuma babu abinda take fahimta a wannan lokacin sai cewar leɓɓensa masu taushi ne haɗe kuma da zaƙin toothpaste, sannan maimakon carpet ɗin dake ƙasa, tana jin kamar ƙafafunta na nutsewa ne a cikin wani gajimare mai laushi. Madaki ya sake tallabo fuskarta yana kara dulmiyar da ita cikin duniyarsa, wadda taji bata son ta tsaya balle har ace ta ƙare, ta wanzu kawai ta cigaba da wanzuwa har abada!

Sai dai ba kowanne fata ne yake kasancewa karɓaɓɓe ba, don a lokacin ne wata murya ta kwaɗo sallama daga can ƙofar falon ɗakin…

Wata zankaɗeɗiyar murya mai kama da alkamashi!

STORY CONTINUES BELOW

***

01:40 PM

Ɗakin Baddo.

“Wani ne yayi sallama ya kawo abincin, kusan kala huɗu ne ina jin, to shine yace kawai in ajiye masa jollof din shinkafar da wani nama in taho da sauran, amma farfesu kifin nan ma tun jiya yake bai ko taba shi ba.”

Cewar Jidda a lokacin da take zaune a gefen Baddon tana taune ƙayar tsakiya ta farfesun kifin da take ci, wannan kifin dai tun na jiya da ranta ya biya akansa, ashe Allah yayi rabonta ne.4

“Yo Jidda ko don irin wannan abincin da kuke ci ba kya canja ba, komai nasha-nasha su basu san ana wani tsadar abinci ba.”

Cewar Baddon tana ƙarewa sauran flask ukun dake gabanta kallo, kowanne ɗauke da abincin da sai tashin ƙamshi yake.

“Baddo ni fa nake girki na, wannan abincin da kike gani kawai anan ne ake kawo masa, amma acan wallahi abinda na iya kawai nake dafawa, sai dai kawai akwai kayan abinci a gidan don ina ga a irin girkin dai dana iya, garin semovita ne kawai babu a kitchen ɗin nan.”

Jidda ta faɗa ranta fes, don tun bayan sanda ta shigo tana ƙoƙarin bin bango data ga ba wanda ke shirin tuhumarta sai ta saki jikinta ta shiga harkokin ta, zuciyarta na zugin daɗi da kowanne bugu da take yi, tana ganin komai mai kyau a idununta, duniyar tayi wani haske da kyalli sannan iska ta ƙara sanyi, komai ya kara kala.

A ɗazu bayan komai ya katse yaje don ganin mai amsa sallamar nan, akwatin dake can ƙasan gado taje ta lalubo ta fito da duka kayanta, har ƴan undies ɗinta dasu sabulu data haɗa cikin wata ƴar ƙaramar jaka, sannan ba shiri ta nufi bandaki, acan ta gama wankanta ta shirya sannan ta fito, kums sai hankalinta ya ɗan kwanciya kuma ganin baya nan, don haka ta lalubo leda a dakin data gani jiya sannan ta ƙulle kayanta masu datti wanda ta cire.

Ita kaɗai ce amma wata irin kunya ce ke ratsa ta da zarar ta tuno abinda ya faru, ta dinga kallon fuskarta a mudubin banɗaki tana ƙifta ido irin na mara sa gaskiya, don tun daga cikin yatsun ƙafarta take jin kunyar na ratsa ta yayin da hoton komai ke maimaitawa a kanta, sai kawai ta shiga jan istigfari tana gayawa kanta cewa ba laifi tayi ba, kowacce mace ma haka rayuwarta take.

Kuma haka zuciyarta tayi ta sake-sake tana tunanin inya dace ta fita a lokacin tunda basu yi sallama, ai kuwa bata wani dade a haka ba sai gashi ya shigo, kuma inda Allah ya taimake ta tare da wani yake wanda ya kira da Sunusi, sannan yana ta wayarsa da tarin mutane kala-kala don haka basket din abincin nan da aka kawo kawai yace ta ɗauka sannan ya nuna mata wanda zata ajiye masa ya bata muƙullin ɗakin, yace in ta gama abinda zata yi ta fito ta ƙulle. Da haka suka sake fita shi da Sunusin ya barta da sake jin ƙamshin turarensa da kuma tunanin ana yin sallar magriba zata dawo. Tunaninta kenan!1

A yanzu idonta ya kai kan mukullin dake ajiye a saman wata ƴar drawer daga gefenta, wai yau itace da muƙullin masaukin Madaki gabaɗaya, wani mutum mai aji, shalelen Mai martaba da ba wanda ke ganinsa kuma mutum guda da sarki ya taɓa takawa Fulani birki akansa, amma me akace ne? matsayi, matsayi ne.

“Kiga itama taje ta zauna, ni wallahi matsalata da aiken Sadiya kenan, ba tafiyar ba dawowar.”

Cewar Baddo tana ƙoƙarin miƙewa sai dafa bango take tana laluben duk abinda hannunta zai kamo.

“Watakila data jira ni mun tafi tare da watakila tuni mun dawo, don Allah yanzu Baddo nayi hankali ba zan wani biye mata muyi tsaye-tsaye.”

“Ni ko na san kinyi hankali Jidda, kuma ai tsabar sanin hankalin naki ne yasa ba zan aike ki siyen goro yanzu ba ko da kuwa kina nan ɗin.”

Jidda ta tamke lebbenta kawai ba tare da tace komai, don tsaf ta fahimci harshen damon dake cikin maganar. A lokacin ne kuma ƙofar net ɗin ɗakin ta buɗe, Jamila ta shigo tare da wasu ƴan uwan Baddo guda biyu, wanda taje ta taho dasu daga can hanyar cikin gida wai sun kasa gane hanyar da zasu ƙaraso.

STORY CONTINUES BELOW

“Eh lallai ai kuwa ga amarya nan, dole Baddo ki sa a kira mu, muzo mu ganewa idonmu…”

“Yo wai Jiddan ce a zaune? Ai ni wallahi na zata baƙuwa akayi… Cancaɗi!”

“Ina zaki gane ta kuwa yarinya ta zama matar aure, matar manya… Ah lallai kuwa su Murja su ƙaraso suna su ga abin arziki…”

“Ai wallahi Baddo baki ji raina ba da kika ce ƴar nan tazo, ice dai kuma an taho mana da guzurin ɗan saurayi ko budurwar ikko?”

Su biyu kaɗai amma kauɗinsu ya cika ɗakin kamar na muyane goma, Jidda sai zumɓuro baki take tana basu amsar cewa ita babu abinda ta canja, yadda take haka take. Bayan an gaisa kuma sai hira ta ɓalle, Baddo ta manta da zancen goronta suka nitsa hirarsu ta ƴanuwa.

Sadiya da ta dawo bayan wani lokaci suka ɗora hirarsu ita da Jiddan daga inda suka tsaya. Bayan haka ne kuma Jidda tayi magiyar duniya amma Baddo ta hana ta zuwa duk wajajen da ta gama lissafawa a jiya, tace data tambayi wanda take karƙashinsa a yanzu ita ba zata ƙi ba, amma babu yawunta ta tafi tana zagaye lunguna tana bi kwararo-kwararo da sunan yawo.

Sai ƴan uwan Baddon ma da suka zo suka rufar mata, kowa na fadin albarkacin bakinsa cewa ita yanzu matar manya ce, don haka ta riƙe girmanta da matsayinta, daga haka sai zancen kuma ya koma kan nasiha akan zamantakewar aurenta, nasihar da bata samu a lokacin da amare ke samu ba ranar tafiya gidajensu, wata nasiha kamar ta gado, mai dauke da kalaman da duk tsananin dauriyar mace sai zuciyarta ta karye ko da kuwa bata fidda kwalla ba.

“Kenan ni duk ƴar nasihar dana miki jiya baki fahimci komai ba sai yanzu?”

Cewar Jamila a lokacin da Jidda ta fito waje don wanke hannu idanunta sun kaɗa kaɗan. Tayi shiru kamar ba zata ce komai na sai kuma ta cije leɓɓenta kaɗan.

“Baki ji me kika ce bane, ‘ƴar nasiha’ Su Baddo kuwa yanzu ai ‘uwar nasihar’ suka min.”2

“Koma meye dai yanzu girma ya hau kanki, in kuma baza ki karba ba sai ki bari duk ranar dana shiga ni zan biya miki ta hanyar da zaki gane.”

Har Jidda ta buɗe baki zata bata amsa sai kuma ta tuna da kitson da take so tayi mata, don a ɗazu Sadiya ta taya ta sun tsefe ragowar kitson nan baki ɗaya, har tana tsokanarta wai kyuyar tsifa yasa ta fara jelar ta bar sauran, kuma haka kurum sai bakinta yayi nauyi ba tace mata komai. To a yanzu ta tabbata idan ta tankawa Jamilan to kuwa ruwa tasha da kitsonta, don haka sai ta danne komai kawai tayi shiru da kuɗirin da ta gama yi mata kitson zata bata amsar da zata shayar da ita mamaki.2

Abinda bata sani ba shine ba lallai hakan ta faru ba.

***

02:10 PM

Bayan Fada, Rumfa ta farko.

“Zaka iya sallamarsu.”

Madaki ya faɗa cikin amo mai zurfi yana kallon Saifudeen dake zaune a gabansa, kan tattausan carpet ɗin dake baje a falon da ya nemi ganinsa daga can inda suke karɓar gaisuwa. Sai dai bayan yazo ya same shin ne sai ga dogarawa har biyu tare dashi wanda suka nemi guri suka tsaya ba alamun tafiya.

“Maganar ta sirri ce?”

Maimakon umarni, tambayar ta fito daga bakin Saifudeen shima yana kallonsa.

“Kwarai kuwa.” Ya bashi amsa yana cikin cigaba da kallonsa

Babu wani musu Saifudeen ya juya ya kalli dogari mafi kusa dashi sannan yace.

“Barde, a bamu wuri.”

“An gama ranka ya dade, an gama kurar yaƙi, a fito lafiya shakakin maza jikan sidi.”

Wanda aka kira da Barden ya fada yain da su duka biyun ke durƙusawa a gabansa, sannan kuma suka juyo kan Madaki da wani durƙusun, gajere.

“A fito lafiya ranka ya daɗe.”

STORY CONTINUES BELOW

Da ka kawai Madaki ya amsa musu saboda danna tab ɗin hannunsa da yake yi, kuma da haka suka nufi hanyar ƙofa suka fita.

“Yaya hannun naka?” Muryar Saifudeen ta katse maganar da Madaki ya bude baki zai yi, sai ya maida bakin nasa ya rufe kamar yana mamakin tambayar kafin ya amsa.

“Alhamdlilah.”

Ya faɗi hakan kuma ya dan tsaya ana cigaba da juya zancen, a hankali kuma sai ya ƙara da kalmar ‘Nagode’ kafin ya miƙo masa tab din dake hannunsa.

Saifudeen ya miƙo nasa hannunsa ta cikin farar alkyabbar da yake sanye da ita ya karɓa, Idonsa ya sauka akan screen ɗinta yayin da a lokaci guda ya fahimci cewa cikin email din Madakin take nunawa don ga messages nan a jere rututu-rututu, sababbi ma na ƙara shigowa.

“I’m sorry, akwai wani message daga ‘Sheppard pratt hospital’ cikinsa zaka shiga.”

Idon Saifudden ya kai kan sunan daya ambata don haka sai ya janye idonsa daga kan kowanne ya danna shi.

A saman sakon kuwa sunan asibitin daya faɗa ne, sai ƴan bayanai game da sashen asibitin da suka aiko da saƙon da kuma na email din Madaki da kwanan wata da lokaci, sai dai duk ba wannan ne ya ɗaurewa Saifudden kai ba illa bayanin dake ƙasan waɗannan bayanan, inda heading ɗin dake can sama ya dunƙule dukkan bayanin cikin kalma biyar kawai.

CONFIRMATION LETTER FOR YOUR APPOINTMENT.

Ya karanta hakan sannan idanunsa suka bi cikin layukan dake kasa don ƙara tabbatarwa. A lokacin ne kuma Madaki ya shiga yi masa ƙarin bayani.

“Wannan asibitin yana ɗaya daga cikin manyan asibitoci dake kula da harkar ƙwaƙwalwa, so nasa likitocin da suka duba Fulani ne sun rubuta min refferal letter daga asibitin su sai na turawa wa asibitin, and luckly a yau da safe suka turo min da wannan takardar ta tabbatarwa, duk da dai basu aiko da date ɗin da za’a je a ga likitan ba amma ina ga kamata yayi a fara shirye-shirye tun yanzu saboda gudun ɓata lokacin tunda har sun yarda sun karɓi case din nata.

So, shi yasa na sanar da kai, saboda harkar visa da za’a mata da sauransu sannan kuma za’a iya tafiya da mutum biyu wanda zasu kula da ita kuma a cikinsu ya zama an sami ɗaya wanda zaiyi representing ɗinta idan an je asibitin.”

Saifudeen ya ɗago da kansa a hankali daga kallon screen ɗin wayar ya kalle shi a lokacin da yake wannan bayanin. Me ƙwaƙwalwarsa take ji ne? Me yake fahimta? Madaki ne ya biyawa Fulani ɗawainiyar ganin likita a wata ƙasar? ya ɗauki matakin da ko shi ɗanta bai yi tunanin aikatawa anan kusa ba? Wanda ta tsana sama da kowa a duniyar nan? Madakin da ta azabtar, ta wulaƙanta shi sannan ta ƙare rayuwarta wajen ƙoƙarin ta kassara shi… A lokaci guda wani abu ya tsaya a maƙogwaronsa yaƙi tafiya, tunani ya hargitse a cikin ƙwaƙwalwarsa, kuma tsawon wucewar wasu lokuta ya rasa guda ɗaya da zai kama a cikinsu ya bashi ma’ana.

Abinda kawai ya sani shine, ubangiji kan azurta wasu daga cikin bayinsa ne da gargaɗi tun a duniya saboda wani ɓangare na rahamarsa, don haka a yanzu mahaifiyarsa ta samu shiga cikin wannan layin, Allah ya azurta ta da rahamar ta ganin sakamakonta a wannan zamanin da talala ta yawaita a rayuukan al’umma, zamanin da ba kowa ke gane kuskuren biyewa zuciya ba sai anzo gaɓar da mutum shi kadai zai gane wato bayan mutuwa.

Sai ya cije leɓɓensa a hankali sannan ƙwaƙwalwarsa ke ƙoƙarin sake tsinto muryar Madaki a lokacin da yake cigaba da yi masa bayanin abubuwan da asibitin suka buƙata a tafi dashi da zarar sun bada lokacin da za’a je. So yake yayi magana amma yana ganin kamar in ya buɗe baki sautin ba zai fito ba, ko kuma ko ya fito din bai san me zai ce ba gashi da alama abinda yake fada ɗin kuma ya kusa zuwa karshe, don haka sai kawai ya sake tattare wani abu cikin bakinsa ya hadiye kamar shi ke da nauyin da yake ji a kan harshensa. A lokacin ne kuma ƙwaƙwalwarsa ta iya lalubo tambayar da tafi dacewa fiye da tarin wanda ke yawo akansa, don haka sai ya iya jin ƙarshen maganar Madakin.

STORY CONTINUES BELOW

“…. Inaga kuma bayan CT-scan ɗin da kuma films ɗin x-rays ɗin da za’a tafi dasu babu wani abu, zanyi handling duk sauran abubuwa, and I will let you know the details in time Insha Allah.” (Kuma zan dinga sanar da kai komai insha Allah.)

“Me yasa kace wannan maganar sirri ce?”

Kai tsaye ya tambaya tun kafin hakan ya subuce masa.

Madaki ya motsa yatsun kafarsa kaɗan, don Saifudeen yazo gaɓar da yake shirin ƙarasawa shima, yazo kan zance mafi muhimmanci fiye da komai akan al’amarin.

“Saboda bana son kowa ya sani, so nake ka bar wannan maganar a matsayin sirri a tsakanin mu, kayi handling komai kamar kai kake yi ta yadda ko Mai martaba ba zai sani ba, especially ma ita kanta Fulanin idan ta warke, bana son kowa ya san da hannuna a al’amarin nan dan Allah Saifudeen.”

A take wani abu ya sake matsewa a ƙirjin Turakin, Turaki mai shirin hawa matsayin Ciroma… ya matse tamkar an ɗaure shi da waya don ba sai wani ya tuna masa ba, a rayuwarsu wannan shine karo na biyu da Madaki ya furta kalmar magiya a gare shi, a wancan karon wani zamani ne daya shude da tarin abubuwa, a wani lokaci da yake roƙonsa da cewar kar ya gayawa mahaifiyarsa yawan kudin da Mai martaba ya bashi wanda ya tambaya don ya fara harkar sana’a ta saida katin waya don a wannan lokacin ya kammala secondary kuma zama hakan ya dame shi.

Amma bai ko saurare shi ba ya kai rahoton wa Fulani, wadda bata wani ɓata lokaci ba ta kwace kuɗin bakiɗaya… Yanzu dududu shekara nawa kenan da bawa hakan baya? Amma sai gashi wai a yau magiyar ta canja, a yau rokonsa yake da cewar kar ya gayawa kowa irin taimakon da zai ga Fulanin yayin da tata rayuwar ke wani mataki da ba zata taba moruwa ba. Tabbas ne cewa wanda bai dogara da ƙudirar ubangiji ba a duniyar nan, shi yayi asara mafi girma.

Ƙarar ringtone ɗin wayar Madakin shi ya taimaka wajen tsamo shi daga abinda ya dace ya faɗa a lokacin, wanda bai sanshi ɗin ba.

Madaki ya kara wayar a kunnensa, Mubarak ne.

“Ka ƙaraso.”

Daga cikin wayar muryar Mubarak mai sanyi ta amsa.

“Eh har Sunusi ma ya kaini na yiwa su Mai martaba gaisuwa a fada, sai dai ban ga Turaki ba ance ya fita, kana ina kai?”

“Muna tare dashi.”

“Okay.”

“Ka gayawa Sunusi ya rako ka rumfar farko daga bayan fada, ba ɓangaren cikin gida ba.”

“Shikenan gamu nan.”

Madakin ya sauke wayar ya kashe. A haka suka ƙarasa maganar ba tare da Saifudeen ya iya faɗin wani ƙwakwaƙwaran abu ba saboda tarin abubuwan dake kai kawo a kansa, kuma a haka Mubarak ya iso ya same su, wanda bayan sun gaisa ne kuma Saifudeen ya koma can wahen karbar gaisuwar yayin suka yi zanansu a nan shida Madakin.

Sai da duk yadda Madaki ya kai ga ya saki jikinsa su tattauna al’amuran dake gabansu Mubarak ɗin ya kasa da cewar bashi da lafiya, don ya gama yi masa mitar dalilin da zai sa ya taho bayan bashi da lafiya tunda gaisuwar ba dole bace. A haka dai a daddafe ya shaida masa hukunci daya yanke na daukar ɗawainiyar rashin lafiyar Fulani, wanda sai a sannan Mubarak ɗin ya ɗan ware ya shiga nuna jin daɗinsa gami da kara ƙarfafa masa gwiwa akan muhimmancin hakan.

Ana yin sallar la’asar kuma suka yi sallama, Sunusi ya tafi kaishi Kano inda zai hau jirgin ƙarfe biyar da yayi booking, suka rabu Madaki na jaddada masa umarnin zuwa asibiti da kuma cewar ya zauna a gida ya huta ya bar komai na harkar office shi zai cigaba da monitoring daga nan kafin lokacin dawowarsa jibi.

Sai dai abinda bai sani ba shine, ɗan adam na tsarinsa ne Allah kuma yana nasa, faruwar wani abu ƙalilan shi ke tunawa bawa cewa tsarin Allah shine ja-gaba.1

Da misalin ƙarfe shida na yamma, yana zaune tare da Sunusi a wata haɗaɗɗiyar baranda dake can gefen Fada, mutane sun tsagaita zuwa a lokacin don haka iya ƴanuwa na gida ne kawai a cikin fadar tare da Mai martaba, kuma a sannan ɗan lokaci kaɗan ake jira kafin kiran sallar magriba, wanda bayan an idar ne Madaki ke sa ran ganawa da Mai martaba a cikin turakarsa.

Don tunda yazo a cikin jama’a suke gaisawa basu kebe su biyu va, saboda haka da kowanne bugu da zuciyarsa ke yi roƙon ubangiji yake yasa al’amuran da suka faru sun ɗan wanke zuciyar Sarkin game dashi, koda abubuwa basu dawo yadda suke a baya ba, ya samu ya kira shi da sunansa na Ibrahim sannan amon muryarsa ya fito da wannan kulawar da yake tsinta a cikinta tun yana yaro. Waɗannan kaɗai sun ishe shi a yanzu, A hankali ya san cewa Allah zai sa lokaci ya dawo masa da sauran.

Sannan a gefe akwai tunanin Jidda ma, yana tuna yadda yayi kissing ɗinta da safe a matsayin wani abu da ba zai iya fassara shi ba don bai taba tunanin cewa akwai abinda zai iya rikita tunaninsa yasa yaji kowacce jijiya ta jikinsa kamar ta kama da wuta irin haka ba. Saboda haka tun daga wannan lokacin zuciyarsa ta sake karyewa akanta, yaji yana kewarta, wata orin kewar da tayi tasiri a zuciyarsa duk kuwa da dama ya sani tarin abubuwan dake gabansa ba zasu sa ya kara ganinta ba sai dare, amma da yaga giftawar wata mace sai ya tuno da ita, ya tuno cewar bayan duk wannan kacaniyar yana da wani abu mai muhimmanci a gefe, wani abu da zai huce dukkan gajiyar dake zuciyarsa da zarar ya ganta.

Kuma Allah ya sani ya daura ɗamarar kai zamansu ga mataki na gaba, ta yadda zai hade zuciya da ruhinsu su zama abu guda, ta yadda zai bi duk wasu hanyoyi da zai baiyana mata irin begen ta da zuciyarsa ke yi koda kuwa zai zama wani Ibrahim ɗin ne daban a duk sanda suke tare, kuma tunanin hakan kadai ke watsawa zuciyarsa wani dadi mara misaltuwa, yana ƙara masa kuzari a duk harkokinsa na yau, wani kuzari mai dauke da alƙawari na zuwan dare. Kuma ga daren nan

ya gabato a yanzu.

Sai dai abinda bai sani ba shine, ba lallai ne ya ga Maijiddan tasa a wannan daren ba!

***Ladanin masallacin ya rangada sallama daidai lokacin da ɗaya daga cikin wayoyin dake jikin Madaki ta shiga gurzawa cikin vibration alamar shigowar kira, don haka yana yin sallamar ƙarshe yasa hannu ya danna ta ƙarar ta ɗauke, kuma bai damu da fito da ita yaga ko waye ba don ya san iya lokacin da zai dauka wajen addu’a ba zai canja komai ba. Saboda haka ya shiga jero addu’o’insa wanda mafi yawanci na nuna godiya ne ga Allah daya inganta rayuwarsa har zuwa matsayin da yake a yanzu.2

Ya buɗe zuciyarsa ga mahaliccinsa tsawon wasu lokuta kafin ya miƙe a hankali, a lokacin sauran  mutane na tashi ɗaya bayan ɗaya suma suna fita, a ɗazu da yake zaune tare da Sunusi ne ya sami kiran Hajja akan tana nemansa don haka ba tare da ya nemi rakiyar Sunusi ba ya tafi shi kaɗai yaje ya same ta, kuma bayan ya fito ne sai ya tsaya a wani masallaci daga gefe yayi sallar magaribar da ake kira, don haka mafi yawanci mutanen cikin unguwanni ne a masallacin ba wasu masu sarauta ba.

A daidai lokacin da ya zura ƙafarsa cikin takalmi ne bayan ya fito wayarsa ta sake cigaba da vibrating cikin aljihun sa don haka ya zira hannu a aljihu ya ciro ta, sabuwar namba ce da bai taba gani ba don haka ya ɗan yi nazarinta kafin ya kara wayar a kunnensa.

“Hello… Please I’m I speaking with Ibrahim Ahmad Madaki?1

Sai ya gyada kansa a fili sannan ya amsa da haka ne cikin harshen turanci shima, amma kuma sai mai maganar ya juya hausa.

“Sunana Donnovan, ina kira ne daga nan police station na Lagos, Ikeja.”1

“Okay.” Madaki ya sake amsawa ba tare da ya fahimci inda zancen ke tafiya ba. Donnovan ya sake gyara muryarsa sannan yace.

“Yau kimanin kwanaki biyar kenan da aka yi filing wani case cewa ana zargin wata yarinya mai suna Salwa Umar da sa hannu wajen harbin da aka yi maka kwanaki baya.”

Sai komai ya tsaya cak a cikin kansa, bai fahimci mai sunan ba amma a lokaci guda ƙwaƙwalwarsa ta nemo makamar zancen haɗe da fuskar Mubarak, wato ya cigaba da bibiyar al’amarin kenan? Bai hakura ba dama? Kuma har ya samu suspect amma bai sanar dashi komai ba tsawon wannan lokacin?1

Tambayoyin suka ɗarsu a ransa yayin da Donnovan ya cigaba da bayani.

“So bayan mun tuhume ta, mun samu dukkan bayanan da muke bukata, kuma ta tabbatar mana da ita tasa akayi harbin tare da taimakon wata ƙawarta da take a Abuja. Kuma mun yi kokarin tura jami’an tsaro na can don kamo ta ta yadda za’a sami bayanin inda masu harbin suke amma sai aka samu akasi cewar ta tsere tare da wani saurayinta, amma duk da haka dai mun tattara duk wasu isassun bayanai da zasu iya kai case ɗin ga kotu don haka muke nemen ka da kazo kasa hannu sannan kuma a ga shaidar harbin kafin a ƙarasa da da case ɗin kotun.”

Yawu ya wuce maƙogwaron Madaki a take, ya san cewa wannan al’amarin babba ne da bai kamata shi kansa yayi wasa dashi ba saboda rayuwarsa ce a cikin hatsari dama ta wanda zai raɓe shi tunda ya tuna har Jidda suka saita bayan sun same shi, amma haka kurum sai yaji wani iri game da zancen, ta yaya za’ace har anyi wannan nisan a bincike amma shi bashi da masaniyar komai? Dawa Mubarak yake shawara kenan? Me yasa sai yanzu ake gaya masa? Idan ma bai sani a Lagos ba saboda zancen rasuwar nan to ba yanzu Mubarak din ya tafi ba? Tabbas akwai wani abu, don ba haka al’amuransu suke ba, suna yin komai ne tare tsawon lokacin da ya sanshi zuwa yanzu, kuma ba zai yiwu ace hakan ya canja ba, dole skwai wani abu saboda haka yayi gyaran murya kadan sannan yace.

“Yallaɓai ita yarinyar ta gaya muku dalilin da yasa aka yi harbin?”

Akwai tarin tambayoyi fal akansa, yana son ya tambayi ma ta yadda aka samo ta da kuma wacece ita amma a lissafinsa wadannan tambayoyin na Mubarak ne.

“Idan kazo office ɗin zaka ji dukkan wani bayani  game da hakan.”

Sai kawai ya gyada kansa sannan yace.

STORY CONTINUES BELOW

“Okay, bari in tabbatar da wani abu zan kira ka anjima.”

Donnovan ya gyaɗa kansa shima daga nasa ɓangaren.

“Shikenan sir, muna jiran kiran naka.”

Da haka wayar ta ƙare, kuma bai matsa daga wajen ba ya shiga neman nambar Mubarak wanda yake da tabbacin cewa ya isa gida a yanzu. Sai dai har sau uku yana gwadawa kiran baya shiga.

Wani abu ya sarƙe tunaninsa don a yadda ya lissafa yaci ace ya isa gida tun ɗazu, to me me zai sa ba zai kunna wayarsa ba har yanzu? Ya cije leɓɓensa yana lalube a cikin kansa, zuwa can wani tunanin ya haska a cikin kansa, sai ya sake komawa kan wayar ya lalubo nambar Habibu.

“Habibu kana ina?”

Daga gidan cin abincin da Habibu yake tare da wata sabuwar budurwarsa mai suna Lulu, Habibu yace.

“Ina gida yallaɓai, Toyin ta aiko min da ragowar ayyukan nan ina ƙarasa project ɗin.”

“Kwanaki naji kana cewa Mubarak matarka ta san matarsa ko?”

Habibu ya girgiza kansa.

“Ai bani da aure yallaɓai, ƙanwata nake gaya masa cewa sunyi makaranta ɗaya da matarsa.”

“Okay, ina bukatar nambarta ne, and I need it now, zaka iya samo mun?”

“Eh, bari in kira ta ba matsala yallaɓai, zan turo maka yanzun nan.”

Wucewar wasu ƴan mintuna kuwa yana cigaba da tsayuwa a wajen sai ga ƙarar text saƙon nambar ya shigo, kuma bai ko tsaya kallonta ba ya danna ta zuwa call log ya kira, babu dalili zuciyarsa tayi  wani iri jikinsa babu ƙwari yake sauraren ƙarar kiran dake tafiya, ji yake kamar bashi da lafiya, jikinsa babu ƙwari sannan bugun zuciyarsa ma babu ƙarfi, yana jinsa ne kamar fallen takardar dake yawo a iska.’

“Assalamu alaikum..”

Muryar Khadija ta shammace shi ba tare da ya fahimci sanda ta dauka ba, sai ya ɗanyi gyaran murya sannan ya amsa sallamar.

“A’a ai ban gane nambar ba, wannan kuma sabuwa ce? Yaya kuke Ibrahim? Ya ƙarin hakuri? Ina Antinsu Hanan?”

“Alhamdlilah, Komai lafiya ƙalau.” Ya dunƙule amsar cikin jimla daya, sannan ya sake tambaya.

“Yana gida?”

Ta san wa yake nufi don haka ta girgiza kanta.

“A’a, yayi waya kafin su taso cewa ya sami delay din jirgi kusan na awa ɗaya, to ina ga yanzu ma basu daɗe da tasowa ba.”

Sai bai jira komai ba, kai tsaye ya wuce ga tambayar da tasa ya neme ta.

“… Khadija akwai wani abu da da Mubarak keyi?kin sani?’

Amon muryar tasa ya fito kai tsaye ɗauke da wani ɗaci da kuma fatan ya samu amsarsa.

Maganar ta daki tunanin Khadija, ta shammace ta don duk da ta sani cewa Madakin ba zai kira ta akan wani abu ƙarami ba, bata yi tunanin cewa tambayar zata zo a haka kai tsaye ba. Sai dai ta godewa Allah da ya tambaya ɗin, don a halin da suke ciki inda za’a ƙara koda kwana biyu ne tana jin ita da kanta ma zata iya kiransa.

Abubuwa sun cakudewa gidanta, Mubarak bashi da sukuni sam, hatta su Aliyu sun san wani abu na faruwa musamman rashin ganin Salwa a gidan don haka su kansu walwalarsu ta ragu. Sannan ita ba wani son Salwa take ba amma Allah ya sani a lokacin da ta matsawa Mubarak ɗin ya gaya mata dukkan abinda ke faruwa da kuma inda Salwan take sai da zuciyarta ta karye, taji tausayinta ya tsarga ta, kuma ta tabbata shima a yanzu tausayin nata ke damunsa kawai ba yadda zai yi ne tunda ya riga ya kai zancen wajen hukuma, don haka Madakin a yanzu shine kadai mafitar komai idan har ya sanya baki aka fito da Salwa to a cikin ƴan kwanaki rayuwarsu zata iya komawa daidai.

STORY CONTINUES BELOW

Saboda haka sai kawai ta nufi hanyar kitchen daga falon da take zaune tana yiwa Hanan da tayi bacci tsifa, ta shiga ciki ta rufe ƙofar sannan babu wani kwana-kwana ta shiga zaiyanewa Madaki dukkan abinda ya faru, da wanda ta gani da wanda ta fahimta da kuma wanda Mubarak ɗin ya gaya mata, bi da bi ta zayyane masa komai.

Tun da Madaki yake a rayuwarsa bai taba jin tashin hankali hade da tsananin mamaki sun ratsa cikin kansa a lokaci guda irin na wannan lokacin ba, ko lokacin da Mai martaba ya ɗaura aurensa da Jidda wani irin abu kawai yake ji wanda yafi kama da ruɗani ba irin wannan ba, don ko labarin daban ne, wancan matsalar tasa ce amma wannan ta shafi mutane da yawa… Mubarak yasa an ƙulle ƙanwarsa saboda shi? Yaushe ma tazo garin? Bai taba gaya masa ba, me ma yake gaya masa ne game da abinda ya shafe shi kwanan nan? Wane irin tabbaci yake dashi na cewa kanwarsa ta jini ce zata iya aikata wannan ɗanyen aikin da har zai hargitsa rayuwarsu akansa kawai? Ya tambaye shi ne tun farko? Ko kuwa shi yace dole sai an nemo wanda ke bayan laifin?”

Idanunsa suka canja launi a take, gyada kansa kawai yake yana saurarenta, har ta kai ƙarshe sannan ya girgiza kansa yayi mata godiya tare da bata hakuri.

Kuma yana sauke wayar bai yi wata-wata ba, wannan nambar da ta kira shi a yanzu ya lalubo ya kira a take, bugu ɗaya biyu kuwa Donnovan ya ɗauka.

“Hello sir..” Muryarsa ta fito raɗau ta cikin wayar.

“Donnovan right?”

“Yes sir.”

“Game da maganar da muka yi yanzu, i don’t need that case, a sallami yarinyar nan ko wacece.”

“Kana nufin ka janye ƙarar kenan?”

“Yes.”

“Okay to, duk da haka dai muna da bukatar kazo saboda ka rubuta statement na cewar ka janye kafin maganar ta zama official.”

“Zan turo representative ɗina gobe da safe, sunanshi Habibu Abdullahi.”

“Okay ba matsala, idan yazo ɗin an gama komai zamu kira wanda ya shigar da ƙarar sai ya karɓi belinta.”

“Shikenan, send me the address, zan tura masa.”

“Okay sir, Thank you.”

Wani abu mai nauyi ya tsaya a maƙogwaronsa yaki wucewa har bayan ya sauke wayar, amma sai ya sake zarcewa ya ƙara kiran nambar Habibun.1

A restaurant ɗin da suke zaune saman wata baranda, Habibu ya buɗe bakinsa kenan Lulu na shirin kara masa tambulan ɗin lemon da ta tsiyayo, wayarsa ta shiga vibration akan teburin dake gabansu, nambar da yayi saving wa Madakin da sunan ‘Sir’ ya bayyana tar a jiki, sai yaja wani ƙaton tsaki sannan ya jawo wayar ya ɗauka.

Madaki na gama yi masa bayani bai saurari doguwar amsar da yake shirin bayarwa ba ya katse wayar saboda wani irin abu dake tasowa daga ƙasan zuciyarsa, wani abu da bai san menene ba yabawa Mubarak kan irin wannan kaunar da har zai iya tuhumar ƴaruwarsa saboda shi ko kuma zafin cewa ya saka kansa a damuwa ya cutar da yarinyar da ƙuruciya ke damunta, don shi a haka ya dauki zancen, ya yarda cewa in ba ƙuruciya ba, babu abinda zai sa ta aikata wannan abin da sunan cewa wai tana son aurensa, haka ake auren? Bai taba ganinta ba, bata tuntunbe shi ba balle har ta sami dalilin da zai sa ta iya cutar da wani akansa? Abinda kawai ya iya kamawa ya riƙe shine Allah ya azurta shi da abokin daya cike tarin guraben mutanen daya rasa a rayuwarsa.2

Yaji wani abu kamar ƙwalla na shirin sauka a idanunsa, amma sai yayi saurin ƙifta su ya maida ita sannan ya sanya wayarsa a aljihu ya nufi hanyar da zata maida shi sashen fada don ganin in zai iya ganawa da Mahaifin nasa a yanzu kafin ya koma inda zai huta, sai dai da kowanne taku zuciyarsa na jin wani iri kamar bai gama warware matsalar ba, kamar wani abu daban kuma na shirin tunkaro shi bayan wannan ɗin. Ilai kuwa yana baro tafkeken soron farar ƙasa wanda ya ɓullo dashi sashen Mai martaban ya hangi mutane a tsaitsaye kan barandar turakar Sarkin kamar masu jiran wani abu. Kuma kafin ƙwaƙwalwarsa ta fahimci wani abun, ya hango Sunusi ya fito daga cikinsu da sauri ya nufo wajensa.

STORY CONTINUES BELOW

“Me ya faru?”

“Ranka ya daɗe wallahi wai jikin Mai martaba ne ya tashi, ance ana dab da tada sallar magriba ya faɗi shine aka ɗauko shi aka dawo dashi nan cikin turakar.”

Amsar Sunusin ta fito kamar wani dutse mai nauyi ta dake shi a ƙirji, Jikin Mai martaba ne ya tashi? Dama yana da wata rashin lafiyar ne bayan ciwon sugan da ya san yana dashi tun da daɗewa?

“Yana ciki yanzu?” Tambayar da yayi ta katse tarin wasu tambayoyin da zuciyarsa ke son jerowa. Sunusi ya gyada kansa.

“Eh yana ciki ranka ya dade…”

A lokacin sun ƙarasa kan faffaɗar barandar sashen, don haka Madaki bai ko kula da mutanen dake tsaye wanda dogarai ke ƙoƙarin sallama ba ya cire takalmansa ya kutsa kai zuwa ƙasaitaccen falon dake farko kafin turakar, Sunusi ya tsaya daga farko yayin da a ciki idanunsa suka gane masa manyan muƙarraban fada guda uku a zazzaune kan kujerun dake rarrabe falon, sai kawai ya tsugunna a gabansa kuma ba zai iya cewa ga ta sigar da ya gaishe su ba, ya san dai kawai bayan sun amsa wani daga cikinsu ya shaida masa cewa Saifudeen na ciki tare da likitocin da suma basu daɗe da ƙarasowa ba.

A lokaci guda Madaki yaji jikinsa yayi wani irin sakayau kamar an zare masa laka, zuciyarsa tayi wani iri sannan yawu ya bushe a bakinsa ƙat! Me ke shirin faruwa ne? Wace irin ƙaddara ce haka mai zuwa a daki-daki? Farko ƙaddarar data haɗa shi da Jidda, harbinsa, mutuwar Farouq, rashin lafiyar Fulani, al’amarin Mubarak da yaji a yanzu… Ya illahi ace a yanzu kuma Mai martaba ya kwanta? Wanne zai ɗauka ya fuskanta a cikinsu?

Sai kawai ya mike a hankali daga tsugunnon da yake ya nufi hanyar ƙofar, abinda ya sani shine koma wane irin ciwo ne ke damun Mahaifin nasa zai iya rantsewa cewa taruwar waɗannan abubuwan ne, don ko shi da yake kan ganiyar shekarunsa da ƙyar zuciyarsa ke ƙoƙarin taɓuka wani abun arziƙi cikin wannan hatsaniyar, balle kuma Sarkin da shekaru sun ja masa, ga nauyin mulki sannan ga raunin da baza a rasa tattare dashi ba. Fatansa kawai a yanzu shine ubangiji ya basu damar tsallake wannan ƙalubalen cikin sa’a.

Ƙafarsa tabi ta cikin ƙaton koridon dake manne da falon sannan kai tsaye ya nufi ƙofa ta farko da tun a baya ya san cewa nan ne turakar mahaifin nasa. Kuma kamar yadda ya zata ne, Mai martaban na kwance kan gadonsa yayin da likitoci biyu ke tsaye a gefensa suna faman gwaje-gwajensu, Saifudeen da Galadima ne kawai a ciki kowannensu na tsaye daga kowanne gefe.

Madaki na tsaye rike da murfin ƙofar wani abu ya wuce ta maƙogwaronsa, wani abu mai nauyi don ya manta yaushe rabon da a rayuwarsa yaga mahaifinsa a wannan halin, shi mutum ne mai jajircewa, mai himma da ƙoƙarin tsayawa akan ƙafarsa komai rintsi don haka tun a baya da wuya ne a ga ciwo ya raunana shi, amma yau ɗaya, rana guda kawai har ya kwanta  haka?

“Bismillah Ibrahim, ƙaraso mana.”

Muryar Galadima ta katse tunaninsa daga inda yake tsaye, sai ya saki ƙofar ya karaso a hankali ya tako cikin ɗaƙin ya tsugunna a gabansa sannan muryarsa can ƙasa ya gaishe shi.

“Muna lafiya Ibrahim, ayi hakuri kaji? Duk abinda ke faruwa tsarin ubangiji ne, mu namu tawwakali ne da addu’a, don haka muyi addu’a Ibrahim, komai MUƘADDARI ne.”

Wani abu ya motsa a ƙasan zuciyar Madaki, yaji kamar rauni na shirin kama shi amma kamar koyaushe a rayuwarsa sai yayi ƙoƙarin tattaro dukkan nutsuwarsa ta hanyar miƙewa tsaye.

“Ranka ya daɗe zamu tafi da waɗannan samples ɗin mu gwada su zuwa gobe kafin mu iya sanin ainihin abinda ke damunsa…”

Cewar ɗaya daga cikin likitocin yana ƙoƙarin miƙawa Saifudeen takardar daya rubuta magunguna a jiki.

“… Saboda mun duba mun gani ba ciwon sugansa bane hasalima shi yayi ƙasa saboda yana ƙoƙarin controlling ɗinsa, don haka a yanzu dai za’a iya bashi waɗannan magungunan pain relivers ne da kuma anti-biotics zuwa goben insha Allah.”

STORY CONTINUES BELOW

Da haka Saifudeen yabi bayan likitocin nan don zuwa bada saƙon magungunan yayin da Galadima ya matsa kusa da gadon yana wa Mai martaba magana a hankali daidai saitin fuskarsa, don haka sai Madaki bai matsa ba ya basu lokaci har suka kammala maganarsu sannan ya matso a hankali lokacin da ya lura Galadiman na yi masa sallama, a lokacin ne kuma idonsa ya  kai kan fuskar Sarkin wanda kallo ɗaya zaka yi masa ka tabbatar da cewar lafiyar tasa ba daidai take ba, yanayinsa ya canja ba kamar yadda ya ganshi da safe ba. Ikon Allah yafi komai, da magribar nan zaman jiran ison ganinsa yake, ashe haɗuwar tasu ta haka zata kasance.

“Ibrahim ne?…”

Ba shiri ya karaso bakin gadon ya tsugunna sanda ya tsinci muryar mahaifinsa a iskar ɗakin.

“Barka da yamma ranka ya dade, Allah ya ƙara afuwa, Allah ya baka lafiya.”

Wataƙila ya amsa amma dai bai ji ba, abinda yaji shine yayi tari kaɗan sannan yayi gyaran murya ya sake kiran sunansa.

“Ibrahim…”

“Ranka ya dade.”

“Taso, zamu yi magana.”1

Ba shiri ya dafa cinyoyinsa ya miƙe sannan ya lalubi saman bedside drawer dake gefe ya raɓe a farkonta, wani zama kamar a gefen wuta, kuma da zaman nasa Mai martaba ya sake ambato sunansa alamun ya fahimci ya zauna ɗin.

“Ibrahim..”

“Na’am.”

“Na dade ina son nayi wanna maganar da kai kuma nagodewa Allah da ya bani dama a yanzu, danar da zan baka hakurin da na dade ina kallonka dashi, don na sani duk wani abu da zaka samu a duniyar nan ba zai kai asalinka ba Ibrahim, rayuwarka bata ragu da komai ba amma na sani babu wani abu a duniyar nan da zai taba iya maye gurbin iyayenka, babu wani jin dadin duniyar nan da iya cike ramin kewarsu a zuciyarka Ibrahim na sani, don cikar mutuncin kowanne namiji a duniya shine iyalansa da iyayensa.

Kayi hakuri tsawon lokaci baka mallaki ko guda ɗaya daga ciki ba, ka zauna cikin iyalai da ƴanuwana ka jure duk wata tsana da kyamar da suke nuna maka, na sani Ibrahim cewa bayani ni da Hajja, har yanzu duk yawan tarin iyalan gidan nan basa maka kallon ɗaya daga cikinsu, wanda na sani hakan ya ƙaru ne da taimakon Fulani. Shi yasa nake so ka sani Ibrahim yau shekara ashirin da shida kenan tun daga lokacin da na fahimci halin da kake ciki a wajen Fulani, na sawa zuciyata ƙudirin nemo iyayenka, ba don in rabu da kai ba sai don in cigaba da kyautata rayuwarka a ƙarƙashinsu, ta yadda zaka mallaki kowanne ƴanci na ɗan adam a duniyar nan.

Nayi nema iya nena Ibrahim, nayi da kuɗina da kuma jikina, na taka zuwa garuruwa sama da goma ni da Iliya da Haruna, ka sansu, mutanen dana karɓe ka a wajensu daga ma’aikatarmu, har Haruna yazo ya rasu, har nazo na sami mulkin nan ya zama Iliyan kawai nake turawa kan duk wata fafutuka kafin shima tsufa ya kama shi, amma wallahi Ibrahim bamu taba samun wani ƙwakwaƙwaran zance game da iyayenka ba koma wanda ya sanka dasu ɗin, sau da yawa sai mun sami labari gamsasshe mun nitsa muna fafutuka a ƙarshe sai mu tarar zancen ba haka yake ba.

Kuma na sani cewa a shekarun baya kaima kayi yunƙurin yin irin wannan binciken, an shaida min cewa har Jimeta kaje cikin sakateriya inda aka tsince ka amma ban sani ba ko bayan nan ka cigaba da nema, abinda nake so ka sani Ibrahim shine akwai tarin mutane a duniyar irin ka, wanda basu taba sanin iyayensu ba balle danginsu kuma a haka suke tawwakali su shimfida rayuwa mai kyau har su koma ga mahallicinsu, ba kowanne ɗan adam ne a duniyar nan labarinsa ke cika ba, babu wanda ke samun rayuwa a yadda yake so ɗari bisa ɗari, ita ɗin wata aba ce mai cike da ƙalubale da kuma ƙaddara.

Ƙaddara wadda take da tarin ma’ana mabanbanta, don kamar yadda kowa rayuwar take daban haka ƙaddarar ma take daban-daban, kowa da irin tasa kuma ba wanda ya isa ya tsallake mata duk tarin dukiya ko mulkinka.

STORY CONTINUES BELOW

Kaga irin tawa ƙaddarar Ibrahim, na samu duk wani jin dadi, matsayi da ɗaukaka na duniyar nan, amma Allah ya sanya ƙaddarata a matar aurena, uwar ƴaƴana, ya jarabceni da Fulani wadda babu abinda tasa gaba a rayuwarta sai duniya. Sannan kaga irin tata ƙaddarar itama? Ta sami duk wani matsayi da damar da zata kyautata rayuwarta Ibrahim, ta sami damar da zata jefi tsuntsu biyu da dutse ɗaya ta bautawa Allah kuma tayi amfani da matsayinta ta hanya mai kyau, amma sai ta zaɓi ta maida ƙaddararta kan hanyar ɓata wanda gashi tun bata bar duniyar ba ta fara ganin sakamako.

Don haka Ibrahim nake son in jaddada haƙuri a zuciyarka, nake son ka karɓi wannan al’amarin a matsayin ƙaddararka, kayi tawwakali ga Allah ko bayan babu raina da na Hajja, kayi rayuwarka kan tafarki mai kyau ko al’ummar gidan nan zasu juya maka baya, kar ka bari sharrin ƙaddararka ya ja ka zuwa hanyar ɓata, ka kalli rayuwarka ta fuskar alkhairin da ka samu ka godewa Allah, shi mai sakayya ne kuma zai saka maka da haƙurinka ko ba’a duniya ba Ibrahim.

Sannan abubuwan da suka faru a kwanakin nan sun sa na fahimci wani kuskure mafi girma da na aikata a rayuwarka Ibrahim, kuskuren zaɓa maka mata ta hanyar da bata dace ba, wasu maganganu da Fulani ta gaya min sun saka naji kamar an wanke idanuna ne daga wani duhu daya mantar dani halayyarka, ya mantar dani kai ɗin dana raina ƙarƙashin tarbiya da irin hankalinsa, ina jin cewa na zarge ka ne kan wani abu da ban tabbatar ba, watakila na biyewa hasashen zuciyata ne akan wani abu da bai kamata ba har na yanke hukunci mai tsauri wanda duk da tsaurinsa bai sa ka ƙi yi min biyayya ba.

Ka goya min baya na aikata abinda tasirinsa zai iya shafar rayuwarka, don ni shaida ne Ibrahim kan yadda rashin dacen mace ta gari ke shafar rayuwar namiji, zan iya gaya maka illar da hakan ke haifarwa tun daga kan ƴan ƙananan abubuwan da baza ka san dasu ba ma har zuwa manya wanda a kallo ɗaya kowa zai gansu, don haka nake roƙon ka da ka yafe min, kowanne ɗan adam baya wuce kuskure a duniyar nan don haka ga nawa nan a wajenka kuma ina neman afuwarka tare da baka damar da zaka iya gyara komai tun yanzu, don na baka damar rabuwa da yarinyar nan Ibrahim in har baka da burin zama da ita, na yarje maka kayi bincike ka samo wadda tarbiyya da hankalinta yayi maka ka aura. Nagode da tsananin biyayya da sadaukarwar ka Ibrahim.

Tun daga kan kalma ta farko har zuwa ta ƙarshe suna shiga cikin ƙwaƙwalwar Madaki ne da wani irin amo mai sanyi, wanda ya raunana zuciyarsa yasa shi jin wani iri, wani irin abu da bashi da suna, yaji kamar ubangiji ya karbi fatansa ne da dukkan addu’arsa yasa fahimta a ƙwaƙwalwar Mai martaba har ya wanke zarginsa akansa haka, bayan haka ga mamakin cewa Sarkin yayi fafutukar neman iyayensa, fiye da irin nasa ɗan neman da yayi a shekarun baya, wanda yayi a ɓoye cikin gudun kar ya sani, kar ya sani don kar yaga kamar bai gode da kyautata rayuwarsa da yayi ba, ashe shi da kansa yana can yana abinda yafi nasa? Amma me yasa yake faɗa masa yake faɗa masa komai cikin wannan sigar? Me yasa zai ce ya yafe masa?

Sai ya haɗiye wani ƙullutun abu a maƙogwaronsa a hankali sannan idonsa ya kai kan fuskar mahaifin nasa, ya sanshi sarai, ya san daga yanayinsa yana jiran amsarsa ne, musamman akan abinda ya faɗa na ƙarshe, game da Maijidda, ya san zai so ya san idan ya karɓe ta ne a rayuwarsa ko A’a, kuma shima yafi so su tafi zuwa zancen nata, saboda haka sai kawai ya zamo daga kan bedside drawer a hankali ya sake tsugunnawa sannan yace.

“Zata zo ta gaishe ka insha Allah ranka ya daɗe.”

Ba kallonsa yake ba amma zai rantse da Allah cewa yayi murmushi don yaji sautinsa a cikin maganar da ya fada.

“Toh Allah ya kaimu ranar da zan ganta kuma da ɗan jikana.”

Tunda Madaki yake bai taba jin kunya irin wannan lokacin ba a rayuwarsa, wani irin abu ya tsarga daga zuciyarsa har yatsun ƙafarsa, sai kawai ya ɗora goshinsa a gefen gadon yana murmushi.1

“Allah yayi maka albarka Ibrahim, kaine ɗan da Allah ya bani na farko, kuma ko a gabansa sunanka zan fara ambatowa.”

Wani abu ya ƙaru akan kunyar ya lulluɓe shi ruf! Wai irin Mai martaba guda nawa Allah yake halitta ne a kowanne ƙarni?4

STORY CONTINUES BELOW

A haka Saifudeen ya dawo ya same su, kuma Mai martaba bai yi shiru ba, sai ya ja su zuwa wata hirar data shafi kasuwancin da Madaki ke juyawa, suka tattauna kusan komai ibda Saifudeen ya fahimci abubuwa da yawa wanda bai sani ba akan harkar sannan suka gangaro kan sha’anin hidan sarautar, anan ilimin Madaki ne ta ƙaru don don ƴan abubuwan da ya sani kaɗan ne sai gashi ya fahimci abubuwa da dama.

Wata irin hira suke mai ratsa jiki, dukkaninsu suna zaune a gefensa kan kowanne bedside drawer na gefe yayin da shi yake a zaune kan gadon sun jingina bayansa da filo muryarsa na ratsa ɗakin a hankali cikin wani amo da duk dauriyar dake cikinsa suna iya fahimtar raunin da kuma ciwon dake cin sa, a haka har bacci ya ɗauke shi, wani bacci mai nauyi don cikin bayanin Saifudeen suka lura idanunsa sun rufe, don haka Madaki ya kama jikinsa Saifudeen ya gyara filon suka mayar dashi ya kwanta, har a lokacin yana fitar da numfashi mai nauyi.

Sai dai lokacin yayi daidai da shigowar Galadima tare da wani dogari dake rike da magungunan nan da aka siyo.

“Ina ga ya samu bacci ne ranka ya daɗe.” Cewar  Saifudeen bayan Galadiman ya shaida masa cewa magungunan yanzu zai sha su.

“A’a, akwai buƙatar yasha su yanzu, kamata yayi tunda baccin baiyi nisa ba a tashe shi.”

“Haka ne, dama kuma su Haj. Maimuna da Nene Hadiza sun aiko cewa sun aiko cewar suna son ganinsa.

Sai Galadima ya girgiza kansa.

“Ina ganin a bari sai zuwa gobe tukunna, da alama yana bukatar hutu tunda har da kansa yayi bacci, amma yanzu dai yana buƙatar maganin.”

Sai Madaki ya gyaɗa kansa alamun shima ya yarda da hakan sannan ya juya a hankali zuwa gadon, da tafin hannunsa guda daya ya shiga buga gefen hannunsa a jikin filon da Mai martaban ke kwance yana kiransa a hankali yayin da Saifudeen ya isa wajen wani ƙaramin fridge dake gefe ya ɗauko ruwa da kofi, Galadima ya karɓi magungunan dake hannun dogarin nan ya matso kusa da gadon sai dai har a lokacin Mai martaban bai motsa ba.

Saboda haka sai Madaki ya ƙara matsar da hannunsa kan filon yana faɗin, ‘Ranka ya daɗe…”

Amma har a lokacin shiru bai buɗa idanunsa ba.

“Ibrahim, bari na gani.”

Cewar Galadiman da ya matso zuwa bakin gadon, sai Madaki ya matsa ya bashi waje, kuma bai kira sunansa ba kamar yadda shi yake yi sai kawai ya kara hannunsa a saman hancinsa, yasa yatsansa ɗaya akan wuyansa, sakan ɗaya, biyu, uku, kamar ya fahimci wani abu sai ya juyo ya kalle su, su biyun dake tsaye suna jiran abinda zai ce.

“Bajoga…?”

“Ranka ya daɗe!”

Wannan dogarin ya amsa a take.

“Kayi sauri, a kira Malam Murtala yanzu.”

Malam Murtala. A take sunan ya zanu a ƙwaƙwalwar Madaki, don ya riga ya san waye Murtalan,  likitan masarautar ne wani tsohon likita da ya dade yana aiki don tun tasowarsa ma a dattijo ya sanshi, amma me zai sa a kira shi yanzu? Bayan ga kwararrun likitoci nan sun zo har sun bada magani?

“Me ya faru? Me Malam Murtala kuma zai yi?”

Saifudeen ya furta tambayar zuciyarsa a fili.

Galadima ya girgiza kai.

“Babu wani abu, ina tunanin kamar baccin nasa yayi nisa ne ba sai mun tashe shi ba.”1

Amsar bata yi wani ma’ana a cikin kansu ba amma sai su duka biyu suka kasa cewa komai, kuma watakila Alam Murtala na ɗaya daga cikin mutanen dake tsaitsaye a  waje, don a cikin minti biyu kawai sai ga Bajoga ya dawo tare dashi. Madaki kawai kallon bakin Galadima yake amma bai ma san me yake cewa ba saboda wani irin ruɗani dake shigarsa, ya ga dai sanda Malam Murtalan ya matsa zuwa cikin gadon Mai martaba yayi wasu dube,-dube a fuskarsa da wuyansa kafin yayi abu na ƙarshe wanda har bayan ransa ba zai taba manta shi ba… Bargon da yasa hannu ya lullube mahaifin nasa a tsakanin minti goma da suka wuce shi ya jawo har sama ya rufe fuskarsa dashi!

STORY CONTINUES BELOW

Me kenan? Me yake nufi?

“A gafarce ni ranka ya dade, ayi min afuwa… Mai martaba Babu!”5

Kamar saukar tsawa cikin duhun dare, kamar karar tsawar data daki dutse cikin duhun dare, muryar Dr. Murtala ta sauka a ɗakin.

“Kamar yaya? Menene babu?”

Saifudeen ne mai ƙarfin halin tambayar.

“Turaki…” Galadima ya kira sunansa amma tun kafin ya ƙarasa ya katse shi, da wata muryar da Madaki ya sanshi a matsayin Saifudeen ɗinsa na asali ba wani mai muƙamin sarauta ba.

“Wai kuna nufin ya mutu? Yanzu fa muka gama magana dashi anan, this is insane ranka ya dade, wallahi ƙarya yake.”

Kuma kafin Galadiman ya sake cewa wani abu sai ya zaro wayarsa ya shiga kira.

“Yusuf ku ƙaraso yanzun nan tare da tawagar su Barde, zamu kai Mai martaba asibiti…”

Sai Galadima ya juyo ya kalli Madaki dake tsaye kawai bai ce komai ba.

“Zan fita in sanar da Jama’a, ka fahimtar dashi dan Allah kuma kar ka bari su fita dashi.”

Da ace Madaki ba kallon fuskarsa yake ba, zai rantse da Allah cewa bashi yake magana ba, don muryar tasa tana rawa ta fito, kamar ƙaramin yaron dake shirin yin kuka.2

Kuma abinda kadai Madakin ya fahimta kenan, bai ma ji me yace ba, don wani ɓangare na hankalinsa yayi cilli can wata duniya daban, wanda ya rage kaɗan ne, kaɗan din da ba zai isa ya bashi tabbacin cewa wai Mahaifinsa ya rasu ba, mahaifinsa da suka gama hira yanzu, sarkin da ya gama neman yafiyarsa, mai martaban da ya gama yi wa alƙawari zai kawo masa Jidda?

Haka ake mutuwar dama? Shi yasa ya gaya masa dukkan wadannan maganganun? A hankali yaji wani ɓari na ƙwaƙwalwarsa na biyo masa kalaman Innalillahi wa’inna ilahir raji’un… Innalillahi wa’inna ilahir raji’un!

Amma duk da haka bai yarda ba, bai yarda wai ya zama maraya a yau ba, bai shirya karɓar wannan maraicin ba..

Ƙafafunsa na sassarfa ya ƙarasa gaban gadon ya buɗe fuskarsa da aka rufe, bai san gawa ba, bai taɓa ganinta ba don haka ba zai ce ga banbancin dake tsakannin kamannin mahaifinsa da sunan Gawar ba. A lokacin yana jin maganganun Saifudeen dake cigaba da waya yana gayawa mutanensa cewar su ƙaraso ɓangaren da wuri, shi bai san ma meye akansa ba, bai san me zaice ba, bai san abinda zai yarda dashi da wanda zai ture gefe ba, saboda haka sai kawai ya gyara masa bargon ya rufe shi kamar yadda yayi masa ɗazu, sannan ya miƙa hannunsa ɗaya cikin bargon ya kamo nasa, yayi sanyi ƙalau kamar bargon bashi da ɗumi, ya ratsa hannayensa tsakanin nasa sannan kamar ɗazu ya nemi gefen bedside drawer nan ya zauna.

Abinda kawai hankalinsa ke gaya masa shine, daga Saifudeen ɗin dake kiran muƙarrabansa har Galadima daya fita babu wanda ya isa ya raba shi da mahaifinsa, idan mutuwa tana nufin rabuwa ne to yau nasa hankalin ya gaya masa cewa watakila zai canja wannan ma’anar don babu wanda ya isa ya fitar da Mai martaba daga wannan gidan.2

Cikin abinda bai fi awa guda ba, labarin rasuwar Mai martaba ya karaɗe cikin garin Kiyari baki ɗaya haka nan kuma ya cigaba da watsuwa kusufa-kusafa na sauran garuruwan Najeriya, sannan duk da dare ne amma masarautar ta fara cika da tarin al’ummar dake bulbulowa don nuna alhininsu, kwaryar garin ta ɗauka da wani irin shiru mara sautin hayaniya don hatta yara ƙanana mutuwar ta taba su balle kuma manya da zuciyardu ke kukan rashin Sarki adali mai hakuri irin Mai martaba Ahmad Uba Kamsusi, wani mutum mai tsanani son al’ummarsa da kuma son adalci a mulkinsa, mai kirki da saukin kai, wanda a tsawon shekarun daya ɗauka akan karaga babu wanda ya taba buɗa baki yayi kuka dashi.

Jama’a da yawa suka dinga danganta mutuwarsa da ‘Mutuwar ƙuruciya’ ba wai don shekarunsa ba sai don iya shekarun daya yi akan mulki, saboda a tarin sarautar zuri’arsu babu Sarkin da ya taba mulki ƙasa da shekaru talatin tun kafuwar garin Kiyari sai akansa, don haka mutuwar tazo a bazata ta girgiza al’umma, musamman da ya kasance tsakaninsa da ɗansa ƴan kwanaki ne kawai, ba’a ko share makoki ba shima yabi shi kuma babu wani ƙwakwaƙwaran ciwo ba komai.

Don haka ubangiji mai iko da zuciyar kowanne bawa shi kadai zai iya sanin adadin alhinin dake zuciyoyin al’umma, musamman iyalansa, wanda suka ruɗe da dimbin koke-koke, amaryarsa Nene Hadiza a daren aka tafi da ita asibiti saboda suma da take tayi tana komawa.

Fulani kowa ya san dama tana kwance, don haka ƴaƴanta ne duniyarsu ta sake rikicewa, basu gama alhinin ɗanuwansu ba, ga mahaifiyarsu dake jinya sannan kuma ace Uba ma babu? Tabbass ne cewa ubangiji ya jarrabace su da wata irin ƙaddara da inda za’a tara ma’anonin ƙaddara mabanbanta a waje guda ba lallai ne a sami irin tasu ma’anar ba, don haka zukatansu sun girgiza fiye da dukkan wani tunanin mai tunani. Ko gaisuwa ba mai iya musu, don duk wanda zai kalli fuskarsu ba zai iya lalubo kalamai mafi dacewar da ya kamata ya furta musu ba, shi yasa daga su sai ƴanuwan mahaifiyarsu ne kawai a ɓangaren da suke, su kadai ke iya tunkararsu da kalmar dai da duk adon da za’a mata bata wuce ‘Hakuri’ ba.

Bangaren Haj. Maimuna ne kawai al’amarin da sauki, don hana duk bayinta wannan koke-koken tayi, tace kowa ya masa addu’a kawai ko yayi shiru. Sannan sanin cewa baza su iya zuwa ganinsa a lokacin ba yasa ta haɗa kan ƴaƴanta suka shiga yi masa addu’o’i saboda ta yarda cewa abinda yafi buƙata daga gare su kenan a wannan lokacin.

Masarautar ta hargitse, koina ya rikice kuma koina ya cika da al’umma kamar a daren za’ayi jana’izar, don kafin ƙarfe goma na dare hatta dogarai sunyi kadan wajen hana mutane shiga ɓangaren Mai martaban inda ya zama babu masaka tsinke!

***

“Yanzu Allah Jamila, har dake kika biye mata a wannan shashancin? Ace sai magariba ta rufa sannan zaku fara wani kitso, kuma kin san ba’a nan zata kwana ba?”

Cewar Baddo tana kallon Jiddan data zauna ana shirin tsaga gashinta daya tashi a iska.

“Wallahi Baddo saboda naje gidansu Na’ima ne da tuni mun kusa gamawa ma, kuma nace ta bari sai gobe tace wai ba lallai…”

Zungurin da Jidda ta yiwa Jamila ne yasa maganarta ta katse amma duk da haka sai da ta ƙarasa.

“… Tace wai ba lallai su ƙara kwana ba.”

“Allah ya isa.”

Cewar Jiddan dake zaune a gabanta, kuma jin shirun da Baddo tayi ne yasa ta ƙara ƙufula, ai duk rashin hankalinta ta san cewa bai dace Baddo taji wannan zancen ba, wato ma zata ce har lissafin tafiya take kenan daga kwana biyu kawai da zuwanta.

Sai dai bata ce komai ba bayan hakan don ta san ba karamin aikin Jamilan bane ta mike yanzu a fasa kitson tunda ma gashi Baddo ta fara magana tunda ba yau aka fara hakan ba, kuma Allah ya sani bata jin zata iya kwana da kanta a haka damunta zaiyi da ciwo.

Wani tunani ya gifta a zuciyarta, sanda ta kalli kanta a mudubin ɗakin Madaki, jelar kitsonta gabaɗaya a tsefe, daɗi ya ratsa zuciyarta, irin daɗin da kowacce mace ke ji a lokacin da tuna cewa akwai wani a gefe daya damu da ita. Daga safiya zuwa wannan daren ta san cewa abubuwan da ta saƙa ta kwance a ranta zasu yi daidai da wanda wani ya shafe rabin rayuwarsa yana tsarawa.

Rana ɗaya kawai amma Madaki ya canja akalar zuciyarta zuwa duniyarsa bakiɗaya, yasa bata iya wani ƙwaƙƙwaran tunani sai nasa da kuma irin amsar da zata bashi.

‘Dama haka maza suke…’ Ta ayyana a ranta.

‘Mace na zaman zamanta su shigo su hargitsa mata dukkan tunaninta, su koya mata wani abun daban ta yadda zata ji in babu su rayuwarta ba zata tafi daidai ba.’

Hasashenta yayi nisa wajen tunanin yadda daren yau zai kasance mata dama rayuwarta idan har sun koma Lagos… Wani alƙawari mai daɗi zuciyarta ke mata, wata rayuwar sabuwa dal da bata san ya zata kasance ba idanunta ke hasaso mata… abinda kawai ta sani shine zuciyarta ta riga ta karɓi Madaki da dukkan al’amuransa don haka ba lallai abubuwa su zo mata da wuya ba saboda haka tunaninta ya sake nitsewa cikin wani abu mai laushi kamar alawar da ake kira sweet-kamfo, don haka bata iya jin hirar da Jamila da Baddon suka fara.

Jamila ta raba gashinta gida biyu, ta ɗaure gefe ɗaya sannan tayi tsaga ta farko a ɗayan daidai lokacin da ƙofar net ɗin ɗakin ta buɗe, Sadiya ta shigo ciki da wani irin sauri, fitarta kenan bata dade ba daga zuwa siyo musu awara da ta tafi yi, sai dai babu ledar awarar a hannunta balle sautun ɗatan da Baddo ta bata.

“Ke meye haka? Wa ya koro ki? Ina kayan?”

“Baddo Mai martaba ne ya rasu, yanzun nan ake sanarwa a cikin gida!”

“Innalillahi wa’inna ilahir raji’un…!”

Salatin Baddo ya taho tare da rushewar duk wani tunani na Jidda…! Kuma abinda bata sani ba shine tazarar dake tsakanin faruwar dukkan hasashenta da kasancewarsa.5

Tazara ce!. Eh mun isa mana, wai basu taho ba? Karfe tara fa za’ayi jana’izar nan Yusuf in baku taho yanzu ba sai yaushe?”3

Cewar wani farin matashi kenan cikin wayar da yake yi a bakin ƙofar sashen Mai martaba inda yake cike maƙil da ɗimbin al’ummar dake ta faman kai kawo yayin da baka jin komai sai hayaniya cikin kalmomin ‘Allah ya jiƙansa’ da Allah ya gafarta masa’.1

Idan ka biyo ta saman kafaɗun mutanen ka shigo zuwa cikin sashen, ka ratso ta cikin makeken falon da manyan mutane masu muƙamin fada ke zazzaune cikin jimami, ka baro falon ka biyo ta cikin koridon hanyar ɗakuna ka shigo ɗaki na farko inda ƙofarsa ke buɗe cike maƙil da jama’a wanda suke ƙanne da ƴaƴan Mai martaba ne, idonka zai tsallake su ya hango maka Ibrahim Madaki wanda jama’ar ɗakin suka taru akansa, wasu a tsugunne wasu kuma tsaitsaiye ana faman maimaita magana guda daya wadda ba alamun yana fahimtar ta.

“… Wallahi har yanzu yaki sakin sa, amma gamu nan dai ai ba za’a canja lokacin ba, ƙarfe taran ne…”

Wani magidanci mai suna Jamil, ɗan ƙanin Mai martaba ke faɗa a waya, daga bayansa ne iyayensa wanda suke ƙanne a wajen Mai martaba tsugunne a gaban Madaki kowannensu na ta lallashi da ban hakuri don ya saki hannun gawar da ya riƙe tun a daren jiya, gawar da ya kwana a gabanta ba tare da ko ya matsa sallar asuba ba.

“… Ba ka rabu dashi ba Ibrahim, anan gidan fa za’a binne shi, a makabartar bayan gida, duk sanda kake so zaka ziyarci kabarinsa Ibrahim, kayi masa addu’a zai ji ka, ka gaya masa dukkan abinda ke damunka ma yana daga ciki zai ji ka…”1

“Baffa duk wannan abinda kake faɗa ba kamar wanda nake gaya muku bane, wallahi Baffa da anyi embalming ɗin jikinsa shikenan babu abinda zai same shi zai zauna a haka, sannan ɗazun nan nayi ordering wani casket da ƙanƙara bata narkewa a cikinsa…”

“Innalillahi wa’inna ilahir raji’un…” Cewar wani daga cikinsu.

“Ya isa haka Ibrahim, kai musulmi ne kuma ba tun yau ba ka sani cewa binne gawa a musulunci wajibi ne…”

Madaki ya juyo ya kalle shi, idanunsa ƙyamas! babu alamun danshi balle kwalla, sannan yanayin fuskar tasa fayau! Babu wani abu da zaka iya tsinta a ciki illa fatan ya samu a fahimce shi.

“Na sani, na sani, bance ba za’a binne shi ba ai, cewa nayi ku bari ko nan da sati uku ne dan Allah, idan aka tabbatar cewa da gaske ya rasun, don wallahi zai iya yiwuwa Doctors din nan basu duba bane, muna gama hira dashi fa akace wai ya rasu, haka ake mutuwar?”2

“Ibrahim..?”

Wani ya sake karɓa cikin hayaniyar mutanen dake faman shigowa suna leƙe don ganin me ake ciki.

“… Mai martaba ya rasu, ya rasu da gaske, da yana da rai da tun jiya daka riƙe hannunsa da bai farka ba?”

“… Ka daure zuciyarka kayi tawwakali ga Allah, wannan itace mutuwar, haka take, haka kowa yake haƙura da ita.”

A lokacin Galadima ya ƙaraso cikin ɗakin daga zancen wajen da za’a haƙa kabari a cikin maƙabartar da kuma saurarar manyan baƙin dake ta faman isowa daga garuruwa mabanbanta.

Idonsa ya sake cikowa da kwalla ganin har ya tafi ya dawo zancen bai canja ba, Madaki yaki bari a fita da gawar har yanzu, tun jiya daya zauna a wajen nan bai motsa ba yana rike da hannun gawar akan bakansa na cewar ba za’a fita dashi a yau ba, hatta ya Saifudeen ya gama kiraye -kirayen likitocinsa ya kona can gefe guda yana goge kwalla cikin irin tasa dauriyar. Daga inda yake tsaye Galadiman ya hangi ƙwayar idanun Madaki wadda ta tabbatar masa da cewa ba’a haiyacinsa yake ba, ba ma fahimtar maganganun da ake masa yake ba, abinda zuciyarsa ta yarda dashi kawai yake ganewa.

Suma kuma mutanen dake zagaye dashi wadanda suke ƙannen Mai martaba masu riƙe da muƙamin hakimai da ire-irensu, sun kasa fahimtar cewa ba gane abinda suke faɗa ɗin yake ba, saboda babu ta yadda zaka hango ruɗani ko rikicewa a fuskarsa, da gaske shi ɗin namiji ne mai dakakkiyar zuciyar da ba kowa zai iya daukar wannan halin da yake ciki cikin nutsuwa irin haka ba, nutsuwar da babu ko kwalla balle ka fahimci rikicewarsa, shi yasa suke ganin kamar yana fahimtarsu ne amma babu abinda yake ganewa.

STORY CONTINUES BELOW

A lokacin guda kuma sai ƙwaƙwalwarsa ta haska masa wani tunani daya bashi amsar wannan matsalar da aka ki wuce ta. Hajja. Watakila ita Madaki zai iya saurarar maganar ta a yanzu, zuciyarta ta bata wani irin yaƙin irin yaƙin yanzu ita kadai ce duk duniyar nan zata iya ban baki ga Madakin har a samu ya bari a fita dashi, duk ɗimbin mutanen nan yayi imani cewa ita kaɗai Madaki zai iya saurara. saboda haka sai kawai ya juya cikin mutanen wajen ya fita, ya samu can ƙarshen dogon koridon ɗakin ya tsaya sannan yasa aka kira masa wani babban dogari da ake kira da ‘Sarkin ƙafa.’

“Kaje bangaren Hajja, ka gayawa Jakadiyarta cewa duk abinda take yi ta bari tazo nan, ko mota ce a ɗauka a shigo da ita har nan.”

Da haka Sarkin ƙafa ya juya ya fita, kuma cikin abinda bai fi minti ashirin ba sai ga Hajja ta shigo ita da wata jakadiyarta guda ɗaya dake rike da hannunta, tayi shigar wata farar atamfa sannan ta yafa fallen atamfar akanta, idanunta kamar atamfar ne sun ɗashe sunyi fari tas! Farin dake shaida irin ɗimbin nata alhini da ƙuncin da take ciki, don Mai martaba ya ɗauke ta ne tamkar mahaifiyarsa, tsawon rayuwarsa tun kafin ma ya hau mulki yana kyautata mata a matsayinta na matar mahaifinsa kuma wadda yake dauka a matsayinta na uwar da yake ganin ita kadai ta rage musu a matan mahaifin nasa, ya girmama ta a lokacin da mutane da yawa har da ƴaƴan masarautar ke mata kallon ƙasƙanci saboda bata taba haihuwa ba, a lokacin da ya hau mulki kuwa sai ta zama ƴar gata, ya farfado da ɓangarenta ya bata tarin hadimai sannan ya kyautata dukkan sutura da abincinta, ya kula da ita kamar yadda ko da ita ta haife shi ba zai canja komai ba.

Don haka lissafa irin ƙuncin da zuciyarta ke ciki ma abu ne da ba zai yiwu ba, haka aka shigo da ita ta cikin tarin mutanen dake tsaitsaiye a wajen dake matsawa suna bata hanya yayin da wasu ma ke mata gaisuwar da bata iya amsawa. Galadima ya ƙaraso gabanta lokacin da aka shigo da ita cikin koridon da yake tsaye, ya sunkuyar da kansa yayi mata gaisuwa sannan ya sanar da ita halin da ake ciki. A lokacin Hajja kasa nemo dukkan dauriyarta tayi, ta kyale hawayen dake kokawa a idanunta ya shiga zirarowa kan fuskarta, wani na bi wani.

“A ciki yake?” Muryarta a ƙasan maƙoshi ta tambaya.

Galadima ya ɗaga mata kansa a hankali sannan ya shige gaba zuwa ƙofar dakin, matasan dake tsaye a kofa na ganinsa suka shiga matsawa ana bashi hanya jakadiyar na riƙe da Hajja a bayansa wadda ke ƙoƙarin goge hawayenta da zaninta don kar hakan ya lalata abinda take shirin yi, sai dai a lokacin da Galadiman ya matsa, idanunta suka sauka akan Ibrahim ɗin dake zaune a gefen gado rike da hannun gawar da aka lulluɓe a gefensa, ba shiri wasu hawayen da suka ninka waɗancan yawa suka sake kwaranyowa kan kumatunta.

Madaki ya juyo daga sauraran wani ƙanin mai martaba dake masa bayani idanunsa suka sauka akanta, akan Hajja tsaye a gabansa tana kallonsa cikin kuka, sai duk wata dauriyarsa ta duniya ta subuce daga ikonsa, zuciyarsa tayi rauni ta narke gabadaya, don haka a lokaci guda hawayen da take dannewa suka fito cikin ƴancinsu, suka sauka masu zafi har kan fatar bakinsa da ita kanta sai a lokacin ta fara rawa.

“Hajja, zaki iya musu magana su fahimce ni? Wallahi ba saɓo nake ba ko wani abu daban, I just want to be sure, so nake in tabbatar kafin in yarda cewa na rasa shi…”

Bata goge hawayen ta ba sai ta karaso gaban nasa sannan ta rankwafa kamar mai yin ruku’u ta kamo ɗaya hannunsa dake saman wanda ya riƙe gawar dashi, don duka biyun yasa ya ƙankame hannun gawar.

“Taso Ibrahim, taso ka kyale su su shirya shi, wannan abinda kake yi ba gata bane a gurinsa, duk soyayyar da zaka yi masa baza ta wuce addu’a ba, jinkirin ba alkhairi bane.”

Girarsa ta cure waje ɗaya, leɓɓen bakinsa na ƙasa ya buɗe kaɗan, yace.

“Hajja, kema ba zaki fahimce ni ba?”

Sai ta girgiza kanta.

“Na fahimce ka Ibrahim, na san abinda kake ji, na san yadda zuciyarka ke maka, amma ka sani cewa ko shi ba zai so wannan abin da kake yi ba Ibrahim…”

STORY CONTINUES BELOW

Maganar ta doke shi a bazata, amma ba dukkanta ba iya kalamanta na ƙarshe kawai, suka ja shi zuwa duniyar baya, wani lokaci mai tsawo daya shuɗe, wasu maganganu suka shiga tarewa a cikin kansa, maganganun mahaifinsa…

‘… Kar ka taɓa yin abinda ba zan so ba Ibrahim, ko bayan raina…’

Jikinsa ya shiga rawa a take, Hajja ta fadi abinda ba zai iya sake musu ba kuma, ba zai iya sake ja da kowa ba, ta faɗi abinda ya kai shi gaɓar da kowa ma zai ci galaba a kansa, kuma bai san ne ta cigaba da cewa ba bayan hakan, ya san dai yana jin muryarta na fita ne daban da muryarta don haka ba fahimtarta yake ba.

Maganganun nan ke kawai ke yawo akansa har suka yi nasarar dawo da wani ɓangare na hankalinsa, ya fahimci kukan da take yi da kuma yadda ɗakin ya ɗauki shiru alamun kowa na jiransa ne, wata kwallar tayi barazanar sake fitowa amma yayi ƙarfin halin maida ta saboda wani abu da yaji yana sauka zuwa ƙafarsa kuma hankalinsa na maye gurbin inda abun ke saukowa, yana  gaya masa cewa hasashen da yake yi abu ne ba mai yiwuwa ba, da gaske ya rasa Mahaifinsa, ya rasa mutum ɗaya a duniyar nan da duk wani gatansa ya taru a ƙarƙashinsa, A yau ya rasa uba ya rasa uwa, a yau zai karɓi cikakken suna na maraya, a yau zai fara jin irin ɗacin da hakan ke ɗauke dashi, daga yau rayuwarsa ta zama fanko, wani irin fanko da ya tabbatar a zuciyarsa cewa babu mai iya cike shi… Yaji yana yarda cewa haka Allah ya ƙaddaro tasa rayuwar cike da ƙalubale kala-kala, wasu ƙalubalen da in ba ubangijin ba, babu wanda ya isa kuma ya bawa zuciya ƙarfin ɗaukar irin azabar dake cikinsu.

Saboda haka sai kawai ya miƙe tsugunne a hankali, kuma bai riƙe hannun Hajja ba sai ya zare yatsunsa daga na mahaifin nasa da yake rike dashi tun jiya, ya dawo dashi daidai saitin kansa ya tallafo shi ta sannan ya juya ga Hakimin Baruwa, wanda yake mai bin mai martaban kuma mutum mafi kusa dashi a lokacin, cikin muryarsa da ta fara karkarwa a yanzu yace.

“Baffa Bismillah..”

Sai ɗakin ya sake ɗauka da maganganun mutane, wasu na hamdala wasu kuma na ƙara ban hakuri gare shi, amma baya jin komai, baya ita fahimtarsu, gawar da yake rike da ita ce kaɗai ke gilmawa a duniyarsa, shi kadai ya san me yake ji kuna shi kaɗai ya san me yake hangowa, mutuwar nan ta shafi kowa amma zai rantse da dukkan rantsuwar duniya cewa yafi kowa shirin fuskantar ƙalubalen da zai biyo baya, bayan duk wannan taron da komai, bayan doron duniya ya ragu da mutum ɗaya a wajensu, a gare shi kuma tasa duniyar gabaɗaya.

Shi ya riƙe kan gawar har ɗakin da aka tanadi komai na wankan ƙarshe ga mamacin, kuma hannayensa na riƙe dai da kan nasa ba tare da ya saki ba har aka shirya shi, kuma ko Saifudeen bai shigo wajen wankan ba don watakila a lokacin hawayen da yake zubarwa ya tsananta, amma shi tun daga wanda ya fito a idanunsa bayan yaga Hajja, bai sake jin alamun danshin wani ba, kallonsu kawai yake su huɗu suna ta ƙoƙarin wanke mahaifin nasa da shirya shi, ƙannensa guda biyu sai Galadima da kuma limamin masallacin Juma’a, a haka har aka gama yiwa jikin shiri na ƙarshe dake jiran kowanne mai rai.

Kuma yana zaune a gaban gawar har aka tattaro dukkan iyalan gidan gabadaya don yin sallama ta ƙarshe gare shi, suka dinga shigowa ɗaya bayan ɗaya kowa fuskarsa tayi muzu-muzu cike da ƙunci da kuma tashin hankali, suka zagaye ɗakin, yana jinsu suna zama har a bayansa kafin Saifudeen ta fara karanto tarin addu’o’in da suke amsawa da ‘Ameen’, a haka har suka kammala, kowa kuma yayi tasa addu’ar sannan Galadima dake gefe ya bada umarnin masu fita dashi su shigo.

Don haka sai hankalinsa ya tunatar dashi cewa wannan ce tasa damar, damar da zaiyi sallama ta ƙarshe dashi a rayuwarsa, saboda haka ya zaro hannunsa daga ƙasan kansa daya tallafe, ya bude fuskarsa kaɗan daidai saitin idanunsa, sannan cikin muryarsa mai zurfi da zak’in dake ƙara haska kwarjininsa ya shiga karanto tarin addu’o’in dashi kansa bai san ya tara su a cikin kansa ba, sautin muryar tasa a hankali yake fita ta yadda in ba a kusa dashi kake zaune ba sai dai kawai kaga bakinsa na motsawa, yayi addu’a iya addu’a, tsawon lokacin da har aka shigo da makarar aka ajiye a gefensu shi da gawar da yake tallafe da ita, kuma idanunsa kyamas har a sannan babu alamun ƙwalla, muryarsa ce kawai ke rawa tana fitar da harafan cikin karyewa.

STORY CONTINUES BELOW

Sai dai ganin kamar addu’ar tasa bata da ƙarshe yasa Galadima ya taso a hankali, ya kamo hannunsa daya riƙe gefen likkafanin yace a hankali shima yadda shi kaɗai zai ji.

“Ya isa Ibrahim, lokaci na tafiya, mutane na can a wajen suna ta jira.”

Ga mamakinsa sai kawai ya gyada kansa a hankali sannan ya kai ƙarshe a addu’ar tasa, kuma da kansa ya jawo ya maida shi ya rufe kamar yadda aka yi, saurn mutanen suka matso aka sanya shi a makarar sannan suka kama suka yi waje da ita, a lokacin alhini ya ƙara taruwa a zuciyar duk wanda ke wajen, masu kuka suka ƙara sautinsu, masu salati muryarsu ta ɗaga yayin da Innalillahi wa’inna ilahir raji’un ta cika iskar ɗakin. Tabbas ko ba a babban gida irin na masarauta ba, ba ƙaramin alhini bane ace an rasa uba da ɗa a lokaci guda, tazarar kwanaki biyu kawai!

Anyi sallar jana’iza har a lokacin Madaki baya cikin hayyacinsa sosai, a tsaye kawai yake yayin da idanunsa ke kafe akan makarar gawar dake gabansu, daga baysnsu kuma ɗimbin jama’ar da ba zasu taba ƙirguwa a lokaci guda bane ko wajen masu ƙidaya ta ƙasa, don jama’ar gari yaro da babba, matashi da tsoho kowa ya taho don samun jana’izar tunda ma’aikatu dama makaruntu na cikin Kiyarin duk basu buɗe ba, bayan haka kuma ga baƙin da tun ƙarfe bakwai na safe suke sauka a garin.

An kai Mar martaba Ahmad Uba Kamsusi kabarinsa da misalin ƙarfe goma sha ɗaya saura na safe, an binne shi a maƙabartar dake cikin gidan sarautar inda ake binne duk magabatansa, kabarinsa kusa da na wani wan mahaifinsa da ya riƙe muƙamin Ciroma a lokacin da kakansa ke akan mulki, yayin da daga sama kuma kabarin mahaifinsa ne Sarki Uba, haka rayuwar take dama, hanya ɗaya ce da ita, ko kabi tafarkin gaskiya ko ka kauce duk dai ƙarshe waje guda kowa yake nufa, alkhairi ko sharrin da kayi kafin ka ƙaraso shi zama shimfiɗa mai kyau ko mai muni a yayin da ka isa! Sai dai fatan dacewa kawai.

‘Ka wakilci ni wajen saka Umar a kabarinsa Ibrahim, ka wakilce ni, na danka maka wannan damar.’

Kalaman mai martaba suka haska a cikin kan Madaki lokacin da suka sunkuya su uku, shi Saifudeen da kuma Hakimin Baruwa suka kamo jikin gawar don sanya shi a kabarinsa, ya tuna yadda ya riƙe hannunsa na hagu ya faɗi hakan cikin kausashshiyar muryarsa… Wa yake tara sani da ubangiji? Wa zai san cewa shima suna shirin rasa shi ne? Wa zai san cewa a cikin kwana biyu kaɗai irin ranar da suka binne Farouq zata maimaita a rayuwarsu? Wa zai san cewa Allah na shirin jarabtarsu ne da wani abu da babu mahalukin da ya isa ya ƙaddara shi in ba ubangijin ba? Wa zai san cewa a cikin kwana biyu kawai rayuwarsu baza ta taba komawa kamar yadda take ba?

Yana kallo har aka rufe kabarin nan akan idonsa, yana saurare liman yayi ta karanto tarin addu’o’in da da yawansu bai sansu ba ma, yana jin ƙarar takun mutane a lokacin da ake juyawa don tafiya, yana kallon nasa ƙafafun shima sanda yake tafiya yana barin maƙabartar, yana barin mahaifinsa a baya, sannan yana jin wani irin gumi dake tsatsatsafowa daga goshinsa duk da sanyin haɗaɗɗiyar motar Saifudeen ɗin da direba ke tuƙa su a ciki, a lokacin da aka koma masarautar kuwa, sai ya tsallake kowa ya nufi ɓangaren Mai martaban, cikin ɗakinsa, gefen gadon da ya kwanta yana roƙonsa ya yafe masa, ya tsugunna a daidai tsakiya ya ɗora goshinsa daga gefe yayi irin tsugunnon da yayi a lokacin da yake gaya masa cewa zai kawo masa Jidda har gabansa.

Jidda. Sunan ya maimaitu a cikin kansa, kwata-kwata yaso ya manta da ita,  yaso ya manta cewa aƙalla yana da ragowar wani gatan a rayuwarsa bayan ƴan ƙalilan ɗin mutanen dake kewaye dashi wanda ya sani duk tasirinsu baza su cike gurbin mahaifinsa ba a zuciyarsa, wannan gurin ya riga ya zama fankon da babu wani mahaluki da ya isa ya cike shi, don kowanne mutum da irin matsayinsa.

A hankali yaji hawaye na sauka akan kumtunsa, masu ɗumi da yawan da yaji kamar an buɗe bakin famfo ne ya fara zuba a hankali, kukan da baiyi ba tun a daren jiya shi ya taho a yanzu, kuma sanin cewa babu kowa a dakin daga shi sai ƙamshin turaren mahaifinsa dake manne da gadon shi yasa shi manta komai, ya ajiye dukkan wata dauriyarsa a gefe ya manta waye shi, ya manta matsayinsa da kuma shekarunsa, ya tuna kawai cewa shi ɗan mahaifinsa ne kuma mahaifin nasa ya rasu a yau, don haka kuka yake da babu sauti sai wani irin girgizawa da jikinsa yaje har yana barazanar motsa gadon yayin da hawaye masu ɗumi ke jika bedsheet din.

STORY CONTINUES BELOW

A wannan ranar Mubarak ya iso, can yamma sosai don sai wajen azahar labarin ya iske shi, yana kwance yana baccin huce gajiyar jiya da bai dawo da wuri ba, don haka yana tashi wajen azahar ɗin daya bude wayarsa ya iske saƙon mutane na taya shi ta’aziyya, tuni ya shiga fafutukar neman jirgi inda yayi sa’a ya samu wanda zai tashi zuwa Kanon da karfe uku, don haka Khadija kawai sai gani tayi yana shiryawa yace da ita Kiyari zai koma ga abinda ya faru, mutuwar ta shige ta mutuka itama har ta nemi su taho tare amma da suka lissafa ɗawainiyar makarantar yara da ba wanda zata barwa sai ta haƙura.

Kuma bayan ya iso Kiyarin bai samu ganin Madaki ba sai bayan sallar magriba, don an kulle sashen Mai martaba daga waje ba tare da an san yana ciki ba, haka mutane suka dinga tambayarsa a fada inda ake zaman ta’aziyyar, sai dai da yake tarin al’umma sunyi yawa ga alhinin da ake ciki sai ba wanda ya maida hankali wajen neman nasa, sai bayan zuwan Mubarak sannan shi da Sunusi da wani Sagiru da suka matsanta aka sami wanda yace yaga shigarsa sashen Mai martabar tunda safe, acan din kuwa suka ganshi su sunusi suka tsaya daga falo yayin da shi ya shiga ciki.

Kuma abu na farko da Madaki ya fara tambayarsa bayan ya masa gaisuwa shine..

“Ka fito da ita?”

Mamaki ya sarƙe Mubarak ɗin yayin da yake zaune a gabansa daga gefen gadon yana kallonsa, bai sa yadda ya zama bane? Bai san cewa yana zaune a waje guda tun safe bane, in ma yayi sallah ya dawo da alama dai wajen yake sake dawowa ya zauna, bai ko yi wanka ba, kayan jikinsa da suka rabu jiya sune har yanzu sannan ba alama yaci abinci, kuma a kallo ɗaya kawai ko daga nesa zaka fahimci irin ƙunci da alhinin da yake ciki, amma duk bayan wannan ya tuna da ƙanwarsa? Har yana tambayar ko ya fito da ita?

“Me yasa kake zaune anan Mdee?”

Ya tambaya maimaikon ya amsa tasa tambayar.

Madaki ya gyara zamansa a hankali, har a lokacin kansa na jingine da gefen gadon.

“Saboda bana son in fita wani ya min gaisuwa Mubarak, gaisuwar da na da ƙarya zan amsata, gwara in zauna inyi jinyar zuciyata ni kadai.”

Mubarak ya hadiye wani abu cikin maƙogwaronsa kafin ya sake magana.

“Dole sai kayi hakuri Mdee…”

“Na hakura ai Mubarak…” Ya katse shi a take.

“… Baka gani bane? Na bari fa an dauke shi, sannan da hannuna nasa shi a kabarinsa Mubarak wane haƙuri kuma zanyi da ya wuce wannan?”

Sai ya gyada kansa a hankali sannan yace.

“Kaci abinci?”

“I’m not hungry, I’m not hungry at all.

(Bana jin yunwa, Bana jin yunwa ko kadan.)

Mubarak ya cije leɓɓensa na ƙasa a hankali, yana jin zuciyarsa na fitar da wani irin tiriri, yana jin kamar ya bude zuciyar Madakin ne ya ɗauke masa dukkan ciwon da yake ji.

Don haka ne kawai zai iya zama mafita, ya yarda cewa babu adalci in har ma aka lallashe shi a yanzu. don haka ya cigaba da zama a gefensa kawai ba tare da dayansu ya sake cewa komai ba, kuma ba tare da Madakin ya sake tambaya akan Salwa ba.

Zuwa can wayarsa tayi ƙara, ya miƙe ya fita daga koridon dakin ya ɗauka, Donnovan ne.

“Me ake ciki?”

Ya tambaya kai tsaye don so yake kawai su ɗora daga inda suka tsaya a wayarsu ta jiya da daddare, sanda ya kira shi wajen ƙarfe goma bayan ya isa gida ya kunna wayarsa yake shaida masa cewa Madaki yace a sallami Salwa baya son case ɗin, baiyi mamaki ba tunda dama yana shigowa Khadija ta shaida masa wayar da suka yi da Madakin, don haka kai tsaye ya nemi alfarmar Donnovan ɗin don cimma matakin daya kudirta ɗauka akanta na gaba.

STORY CONTINUES BELOW

“Mun kai ta gidan kangararrun yallabai, har ma an bata ɗaki da komai, kuma ba’a haɗa ta da kowa ba kamar yadda kace, sannan mun gaya musu duk sharaɗan da kace a dauka akanta.”

Mubarak ya gyada kansa.

“Shikenan nagode Donnovan, I really appreciate it, sai ka turo min da total din abinda kuka kashe da kuma account numbernka.”

“Alright sir, Nagode.”

Da haka wayar ta katse, ran Donnovan cike fal da murnar kuɗin da yake shirin cafka, yayin da zuciyar Mubarak ke saƙa da warwara kan wannan ɓangaren da rayuwa ta juyo dasu.

***

Washegari.

“Wai shiga zamu yi?”

Sadiya ta tambaya a lokacin da suke tsaye daga nesa suna kallon harabar Babbar fada inda ake zaman karbar ta’aziyyar ɗimbin mutanen dake ta bulbulowa suna shige da fice akan idanunsu, manyan mutane sai faman shigowa suke da muƙarrabansu ana ta sunkuyawa ana gaisuwa tun kafin ma su ƙarasa ciki.

“Ba na jin fa zamu iya shiga Jidda, babu mace ko ɗaya anan.”

Sadiyar ta sake faɗa yayin da Jidda ta cakuɗa yatsunta cikin juna tana jin zuciyarta wani iri, bata da sukuni tun jiya, tun jiya da akayi rasuwar nan bata ga Madaki ba, bata san halin da yake ciki ba kuma bata sani ba ma ko yaci wani abinci, abinda ta tabbata kawai shine ta san yana cikin wani irin alhinin dashi kadai zai iya fassara shi.

Shi yasa take so ko daga nesa ne ta ganshi ko zuciyarta ta huta da azabar tunane -tunanen da take yi tun jiyan. Mutuwar mai martaba ta daki kowa ta sani, amma ita a lokacin da labarin ya iske ta, Madaki kawai take hangowa, shi kaɗai take gani a idanunta tana wassafa irin halin da zai shiga sai dai yawan hargitsin mutanen jiya da kuma yawan al’ummar da suka cika masarautar taf! Yasa bata ma san inda zata tunkara ta nemi shi ba, a jiya bayan jana’izar dai sunje ɓangaren Hajja ita dasu Jamila har ma da Baddo, kuma Hajjan na ganinta duk ɗimbin jama’ar dake gabanta da kuma alhinin da fuskarta ke nunawa sai ta miƙa hannu ta kamo ta, ta zaunar da ita a gefenta sannan suka gaisa dasu Baddon cikin mutuntawa, sai dai bayan wani ɗan lokaci da mutane suka yawaita har ta tashi ta tafi falonta na farko don karɓar gaisuwar maza dake shigowa basu ƙara ganinta ba, haka suka gama zamansu suka taso tunda basu san kowa ba bayan itan.

Da yamma kuma suka shiga cikin gida har da Baddon bayan sun yini jugum-jugum kamar sauran al’ummar masarautar. Sai dai a cikin gidan ma babu wani takamaimai wanda ake wa gaisuwa don ɓangaren Hajiya Maimuna ne kawai da mutane, bangaren Fulani kuwa ba’a shiga kwata-kwata cikin umarnin ƴaƴanta da ƴanuwanta da suka ce basa bukatar zaman makokin saboda rashin lafiyarta. Wajen amaryar Sarki ma Nene Hadiza, daga asibiti ƴanuwanta basu dawo da ita gidan ba, an kaita can gidan Mai martaban na bayan gari wai don kar hankalinta ya daɗa tashi har jininta ya sake hawa da ganin jama’a.

Don haka a ƙarshe wajen ƴanuwansu ma’aikata kawai suka sami waje suka zauna aka cigaba da jajantawa juna yayin da ita nata tunanin baya kansu kwata-kwata, yayi tsuntsunwa ya tafi lalube kusufa-kusufa yana ƙoƙarin nemo mata inda Madakin yake, amma duk da haka bata samu ganin nasa ba har dare, haka ta kwanta tana ta sake-sake da tunanin taya shi alhini, kuma sai wajen ƙarfe ɗaya na dare sannan ta samu bacci ya ɗauke ta. Shi yasa a yau da ta tashi sai zuciyarta ta kasa daurewa sam, ta tattaro Sadiya tace tazo ta raka ta suzo wajen da maza ke karɓar gaisuwar ko wani ta samu idan ta tambaya akace mata tana ciki watakila zata ji sauƙi.

“Nima na zata ko zan ga da mata ne sai mu ƙarasa mu tambayi wani.”

Ta bawa Sadiyar amsar da bata kai har zuciyarta ba, don a yadda take jin kanta, zata iya ratsa cincirindon mazan nan ta shiga ciki in har zata iya ganinsa, ta damu dashi a lokacin bata ɗauke shi a matsayin komai ba ma balle yanzu da ya samarwa kansa waje a zuciyarta…

STORY CONTINUES BELOW

“… Amma mu ɗan matsa gaba ko idan wani yazo wucewa zamu iya masa magana.”

Sadiya ta kalle ta.

“Wai kin manta rashin mutuncin dogarawan nan ne? Kinga wadancan dake tsaye a gefe to yaran Alhaji ne, kuma kin san irin rashin mutuncin Alhaji dai kafin ya daina aikin dogari, tsaf zasu yi abinda yafi nasa ma..”

“Wane Alhaji? Ko wanda ya taba zane mu a soron wailari?”

“Shi. Wallahi to suma ba mutunci zasu yi ba kina ganin fuskarsu.”

Jidda ta tamke leɓɓenta.

“Kinga muje, ai wallahi yanzu babu wanda ya isa ya taba ni a cikinsu ya kwana lafiya.”

“Babu fa wanda ya sanki Jidda, idan sun mana wani abu sun riga sun yi, daga baya sai dai kawai ace ayi haƙuri…”

Sai dai Jiddan bata ko saurare ta ba tayi gaba, mamaki ya kama Sadiyan ganin da gaske ta tafi gadan-gadan zata shiga harabar kai tsaye, ai ance hali zanen dutse, gani take ba aure ba ko ƴaƴa goma Jidda zata haifa wannan ɓangaren halin nata na rashin tsoro da tunkarar duk abinda tayi niyya kai tsaye ba zai goge ba, don haka kamar lokutan baya itama in Jiddan ta tattaro ta suzo suyi wani abun, sai zuciyarta ta shiga bugun goma-goma na taraddadin kar dogarawan sun hango ta amma sai wani abu ya faru kafin Jidda ta kai ga yin nisa a harabar…

Wani ne yazo wucewa, wani da bata sanshi ba amma da alama ita Jidda ta sanshi a wani waje, don tun kafin ya gifta ta tsaida shi kuma shima daga yadda yake mata magnar kamar da girmamawa a ciki don har ɗan sunkuyar da kansa yake yi, abinda yaso bata dariya kenan, wai wannan ƙaton saurayin ne ke girmama Jidda, yar ƙarama da ita a gabansa da in ba don matsayin da Allah ya kaita ba bai fi ya take ta ya wuce ba.

“Sunusi yace ba zan iya ganinsa ba Sadiya, tunda akayi rasuwar yana can turakar Mai martaba bai fito ba, ko shi baya iya shiga iyakarsa kofa kawai.”

Abinda ta fada mata kenan bayan sun gama magana da saurayin ta juyo, kuma abin kamar wasa sai gashi Jidda bata sami ganin Madaki ba har sai washegarin ranar da aka share makoki da kwana bakwai, a lokacin dukkan wata gaɓa ta zuciyarta ta gama ragargajewa da tunaninsa, har sai da hakan ya shafi kuzarinta ya zamo har Baddo na ɗan bata baki cikin magana.

Kullum dai ita da Sadiya zasu je ɓangaren Hajja ta mata gaisuwa, har ma ta dan zauna kuma itama Hajjan sau ɗaya ta taɓa tambayarta in ta haɗu da Madakin tace mata A’a, kuma daga nan bata kara tambaya ba itama don mutane sun sha kanta ga ɗimbin alhinin da take ciki don har ƙarin ruwa sai da aka mata na yini guda.

Shi yasa kwata-kwata bata cikin nutsuwarta a kwanakin hatta idonta ya nuna ta hanyar faɗawa ciki, abu daya dake ɗan bata ƙwarin gwiwa ya tuna mata cewa da gaske Madakin na nan shine muƙullin ɗakin nan, idan taje ta bude taga akwatinsa da kayansa, wanda shima sau biyu kawai taje na farko da taje ɗauko kayanta da kuma flask ɗin abincin nan da Allah baiyi wani zai ci ba don ya lalace, sai na biyu kuma ita da Sadiya kawai suka bude suka shiga da kewa ta dame ta, kuma a ranar ne wasu dogarai suka shigo suka tsare su da tambayar su waye su da kuma yadda akayi suka sami muƙullin wajen, da kyar Allah yayi suka fahkmce su suka kyale su. Shikenan sai Baddo tace kar ta ƙara zuwa, ta karbi muƙullin ma ta ajiye a wajenta.

Don haka yau kwana takwas kenan da rasuwar Mai martaba, an share makoki kuma har an fara raɗe-raɗe da jita-jitar Sarki na gaba da za’a naɗa, mutane da farko na ganin cewa tunda ga ɗansa nan babba Saifudeen maganar ba wata mai tsawo bace, amma sai ga labari daga kusufa-kusufa cewar ana ganin ƴaƴan gidan Auwalu Rumfa da yake wan kakan Mai martaban sun fi shi cancanta saboda wai sun daɗe suna fafutukar sarautar ta dawo gidansu tun lokacin hawan Sarki Uba, don haka sai zancen alhini ya fara gushewa daga zukatan al’umma aka fara cece kucen naɗi kuma, dama haka duniyar take, wanda ya mutu shi ya tafi, kuma tafiyarsa ba zata hana komai ba.

STORY CONTINUES BELOW

“Yanzu saboda Allah ina hankalin su masu alhakin zaben yake? Har yaushe za’a haɗa shi Saifudinin da wannan yaron Yakubu? Farkon zuwana gidan nan fa har giya akace mahaifinsa na sha…”

Cewar Baddo, a lokacin da take zaune ita da Hajiya Laraba da kuma wata ƙawarsu Inna mai aya, da misalin ƙarfe ɗaya ne na rana, Jamila na kitchen tana girki yayin da daga can gefen ɗakin Jidda na kwance tana wasa da zaren tabarma a hannunta, Sadiya kuma na daga gefenta kan tabarmar tana karanta masu wani littafin yaki data aro a wajen wata sabuwar ƙawar da tayi bayan tafiyar Jiddan.

Sunan yarinyar Laila, ƴar ajinsu ce a makarantar dare, sai dai a da basa yi mata ko magana saboda ita a gaba take zama su kuma a baya wajen ƴan surutu, sune irin zakwakuran ajin nan ƴan gani na iya wanda malamai ke ji dasu, shi yasa da Sadiyar ke gaya mata cewa suna shiri sosai bayan tafiyarta sai kawai tabi ta kara tsanarta ba gaira ba dalili, shi yasa ma ko sauraren labarin bata yi sosai, saƙe-saƙenta kawai take yi wanda a ciki har da tunanin kayan da Madaki ke sawa tsawon wadannan kwanakin, tunda gabadaya kayan da ya taho dasu suna masaukinsa har yanzu kuma muƙullin na wajenta.

Aunty Zainab ta buɗe ƙofar dakin ta shigo, dawowarta kenan daga asibiti kan matsalar ciwon cikin da take fama dashi har yanzu.

“Sannu Zainab, sai yanzu?”

Cewar Inna mai aya yayin da kowannensu ya amsa sallamarta.

“Wallahi Inna, layi kamar me.”

Ta fada tana neman wajen zama.

“Ai dama, zuwa asibitin gwamnati yanzu sai godiya wulakanci ne ka same shi, an ɓata mutane da karya in sauki kake nema sai dai ka cire kudi ka tafi mai zaman kansa.”

Cewar Baddo, Hajiya laraba ta karba itama.

“Wallahi ai sai dai addu’a, yanzu ki ga fa tana sallame asuba ta shirya ta tafi amma sai yanzu rana ta ɗaga sannan ta dawo.”

“Aunty Zainab Sannu da zuwa.”

Jidda da Sadiya suka fada kusan a tare lokacin da Jamila ta fito daga kitchen tana tambayarta ta samu ganin likitan, sai dai kafin ta bata amsa ƙofar ɗakin ta sake budewa, wasu mata biyu suka shigo tare da sallama, Aunty Zainab da Inna mai aya suka hada baki wajen amsa musu, yayin da amsawar tayi daidai da tahowar bugawar zuciyar Jidda a lokaci guda. Ɗaya daga cikinsu ta gane, wannan baiwar ce, wadda aka aiko da wayar Hajja ranar da Madaki ya kira ta zuwa masaukinsa.

Suka shigo ɗauke da murmushi a fuskarsu su duka biyun yayin da suke gaishe dasu Baddo, sai Jidda ta tattaro dukkan nutsuwarta ta damke zaren tabarmar dake hannunta ta mike zaune tana cigaba da jin yadda zuciyarta ke bugawa har a yanzu.

“Madaki ne ke neman ison shigowa ya gaida ku…”

Maganar da ta biyo baya, ta cika kunnen Jidda tare da ƙarar rugujewar wani abu nai nauyi a cikin ƙirjinta, Madaki ne yazo? Wane Madakin? Ibrahim? Ibrahim ɗin dai da ta sani? Yazo gaida Baddo? Da kansa? Ya ilahi!

Ba shiri ta miƙe zaune yayin da take ganin fuskokin kowa a dakin na haskawa da irin nata tsantsar mamakin.

“Yanzu? Yanzu ike tafe?” Baddo ta tambaya da alamun mamaki da kuma murna a muryar tata.

Baiwar ta gyada kanta.

“Eh suna can soro, munzo mu sanar daku ne kafin su shigo kuna a gayawa jama’ar tsakar gidan ma.”

Su shigo. Ba shi kadai bane kenan… Jidda ta ayyana a ranta, sai dai karfin mamaki da kuma wani dadi da ya shiga ratsa zuciyarta a take yayi cilli da tunanin komai sai na yadda zata ga Madaki a cikin dakin nan nasu…

“A’a ba komai ai, je kiyi masa maraba, bismilansu su karaso.”

Cewar Hajiya Laraba da murmushi a fuskarta, baiwar ta amsa itama tana murmushi sannan ta mike ta juyo zata fita, a lokacin idonta yaga Jiddan dake zaune a gefe don haka ba shiri ta sake durkusawa tana gaishe ta tare da ɗayar dake bayanta.

STORY CONTINUES BELOW

Kuma suna sa ƙafarsu suna fita, Jamila da Sadiya suka bazama kan kwashe kowanne tarkace dake falon suna hankada su cikin daki, Sadiya duk abinda taga yayi tudu kawai ɗiba take tana cilla shi ciki yayin da Aunty Zainab ta ɗauko tsinken turaren wuta guda biyu daya rage a cikin kwalinsa ta nufi kitchen da sauri ta kunno shi, don kamsin girkin Jamila gabadaya ya gauraye ɗakin ta rufo kitchen ɗin ta fito tana neman inda zata maƙale shi yayin da Baddo ke gayawa Jamila ta ɗauko mata hijabi a ɗaki.

Sai ga Jamilar kuwa ta fito da sabon hijabinta na sallar bara da kuma katuwar dardumar da Baddo ta siya sabuwa don baki na musamman irin wannan. Jidda na zaune jawai kallonsu take ba tare da ta san takamaimai abinda ya dace tayi ba ita kuma.

“Ki miƙe ki sami mayafi kema, ko sai sun shigo tukunna?”

Muryar Aunty Zainab ta katse ta daga yadda take kallon Sadiya na diban duk abinda idonta ya kai tana hankada shi cikin ɗaki.

Cikin abinda yake ƙasa da minti uku kuwa sai ga falon Baddo yayi fili da faɗin da Jidda bata taba ayyanowa yana dashi ba, amma cikin ɗaki da kyar aka rufo ƙofar ta rufu saboda cunkushewar da yayi, ita kanta ta kan kaya ta taka tabi ta ɗauko baƙin mayafin data yafa akan rigarta.

Kuma a lokacin ne Jidda ta tabbatar da cewar baiwar nan ba ƙarya take ba ko kuma ita ba mafarki take ba, don tun daga nesa suka fara jiyo muryoyin mata daga waje na gaisuwa, ana ta fadin, ‘Barka da shigowa ranka ya daɗe, ya ƙarin hakuri, barka da isowa, barka dai… Barka dai…’

Ita da Sadiya da Jamila suka zaune daga can gefe inda in mutum ya shigo ba zai gansu ba yayin da su Baddo suka hau layi a gaban dardumar da dole in suka shigo nan zasu zauna Aunty Zainab kuma na zaune daga gefensu.1

Kuma sai komai ya cika sanda ƙofar dakin ta buɗe, bayin nan biyu suka shigo kuma biye dasu  na farko Mubarak ne, sai Sunusi sai kuma mutumin daya canja rayuwar Jidda, ya shigo sanye da wasu fararen kaya na yadi masu ɗan banzan kyau. Gefen fuskarsa kawai Jidda ta gani sai bayansa a lokacin da yabi su Mubarak suka zauna kan dardumar nan, amma duk da haka sai da gabanta ya faɗi saboda irin ramar da taga yayi…

Kuma a lokaci guda sai ɗan turaren da Aunty Zainab ta kunna ya disashe cikin ƙamshin turarukansu da suka baɗe iskar dakin, kowannensu kansa a sunkuye suka shiga gaishe dasu Baddon cikin girmamawa, Sunusi ne kawai ke ɗagowa yana kallonsu.

Su Baddo suka shiga yi musu ta’aziyya yayin da Baddon ta ɗora da ƴar nasiharta da kuma ƙarin bayanin haƙuri cikin irin zancensu na tsofaffi mai cike da salati su Hajiya Laraba na amsa mata, Allah ya taimaka Aunty Zainab tayi saurin katse su ta hanyar yiwa su Jiddan magana da su karaso su gaishe su.1

Kuma har a lokacin da suka je gabansu suka tsugunna Madaki bai ɗago da kansa ba, Mubarak ne kawai ya kalle su sai kuma Sunusin dake bin kowa da kallo, amma Jidda ta lura ita yake kallo, ta yadda idanunsa suka taho zuwa saitin ƙafarta. Sai taji kamar a barsu su biyu kawai don ya ƙarsa ɗago da fuskarsa ta kalle shi sosai.1

Wucewar wasu ƴan mintuna sai suka miƙe suka yi sallama, Baddo dasu Hajiya Laraba na ta faman sa albarka suna godiya, kuma idanun Jidda basu bi su da kallo ba sai suka sauka akan wrappers ɗin kuɗin da Sunusi ya ajiye guda biyu, ƴan ɗari-ɗari.

“Dama ke suka zo ɗauka ranki ya daɗe, sunce zaku koma ne yanzu.”

Maganar da Baiwar ta fada bayan fitarsu yasa kowannensu ya juyo ya kalle ta sannan kuma Jidda dake zaune a gefe idanunta suka zare, sai ta juyo daga kallon Baiwar itama ta kalli Baddo.

“To tashi mana ki hada kayanki, kin san jiranki zasu yi.”

Saboda munafunci irin na Jidda sai tace.1

“Baddo ko wanki banyi ba fa.”1

“Eh gaskiyane, ai jiranki zasu yi yanzu ki wankin har ma su bushe Jidda, zauna.”

STORY CONTINUES BELOW

Cewar Jamila.

“Tashi kije ki hado su haka acan ba’a wankin ne.”

Aunty Zainab ta fada tana miƙawa Baddo kudin da aka ajiye.

Sai ta mike ita da Sadiya suka shiga dakin, ta taimaka mata suka ninko kayan nata har da karin wasu ma a wardrobe dinta da take so, suka jera su a cikin wata ƙatuwar leda sannan suka fito, sai kuma taji wani iri, tana son tafiyar amma bata shirya a yau da wannan tsakar ranar ba, yanzu in ta tafi ma sai yaushe?

Tana tsugunnawa a gaban su Baddon da niyyar yi musu sallama sai kawai taji hawaye sun zo.

“Au, to meye na kukan, kar ki damu komai dadewa dai ai zai dinga barinku kizo ki ganmu. Kuma ni dai na gaya miki duk abinda ya kanata ki sani Jidda, saura ki dauka kiyi amfani dashi kawai, don wannan itace ƙaddararki kin sani idan kika rungume ta ki maida ita alkhairi ke zaki fi kowa jin dadin hakan.”

Cewar Baddo, itama muryar tata ta nuna tafiyar tazo mata a bazata amma ba yadda zatayi. Aunty Zainab ta fita a lokacin don haka dasu kaɗai tayi sallama, yayin da Baddo ke faman ta maimaita cewa tayi masa godiyar kudin da suka ajiye.

Jamila ta ɗauko hijabinta da niyyar raka su yayin da bayin nan suka shige gaba.

“Gashi, nambata ce data Aunty Zainab na rubuta, in baki sami waya ba ko tasa ki ara wani lokacin ki kira mu, mu dinga gaisawa.”

Jamilar ta faɗa tana miko mata wata takarda, ta karɓa ta cusa cikin ledar kafin tace.

“Insha Allah zan kira kuwa inji komai, zaki kirga min ma duk kayan da suke cikin lefen nan in an kawo.”

Sai jamilar tayi murmushi daidai lokacin da Aunty Zainab ta dawo ɗauke da wata leda kamar ta magunguna.

“Jidda kowacce kwalba acikin nan da bayanin yadda zaki sha da kuma abubuwan da zaki haɗa dasu, na san dai kayan da zaki haɗa dasu ɗin baza su gagare ki ba. Kuma wallahi ki sha don na san halinki sarai.”

Jidda ta cure girarta waje guda.

“Aunty wai magani ne? Ni fa lafiyata kalau. Ko wai idan zazzaɓi ya kama ni ne zan sha?”

“Ba maganin zazzabi bane, na gyaran jiki ne, kuma kowanne sau uku a sati zaki dinga shansa, na dai yi bayanin komai a jikin takardarsu zaki gani.”

Jidda bata gane ba, amma da yake dai a lokacin sauri ne, sai ta ɗaga kai kawai ta karɓa sannan tace zata sha din, kuma anan suka yi sallama da Aunty Zainab ɗin bata biyo su ba,ta tafi tana jin wani iri yayin da matan da suka firfito ke ta binta da addu’oin ‘Allah ya kiyaye hanya’ wanda mafi yawanci ba saboda Allah bane.

Can harabar parking lot bayin nan suka kaisu, kuma Sunusi yana hangosu ya karaso ya karbi kayan hannun Sadiya ya nufi jikin wata dalleliyar mota ƙirar Hyundai dake kyalli cikin hasken ranar, ya sanya ta cikin booth ɗin dake buɗe ya sanya su a ciki.

Har Jidda ta fara tunanin inda suke sai ƙofar motar ta baya ta buɗe Madaki ya sanyo kafa ya fito daga ciki, kuma sai da Jidda ta ƙifta idonta saboda hasken ranar ya sauka direct akan fuskarsa ya dallare mata kammaninsa, ya rame da gaske, sannan idanunsa sun faɗa ciki sun ƙara lumshewa, har yanzu bai dawo daidai ba da alama, har yanzu alhinin bai barshi ba, kuma ba tare da ta sani ba ƙafarta ta cigaba da tafiya daidai saitinsa a lokacin da shima yake kallonta.

“Mubarak yaje baya kadan, yanzu zai dawo sai mu tafi.”

Muryarsa, wannan muryar tasa mai taushi ta shiga kunnenta sanda ta tsaya a gabansa. Sai ta gyaɗa kanta a hankali sannan tace.

“Banyi sallama da Hajja ba.”

Sai ya girgiza kansa.

“Kar ki damu, I told her ba lallai ta ganki ba.”

Ta kasa janye idanunta daga fuskarsa, kallonsa kawai take tana ƙoƙarin lalubo dukkan abinda ya canja cikin ƴan kwanakin nan.

“Toh mu zamu koma Allah ya bamu alkhairi, Allah ya kiyaye hanya.”

Cewar Jamila daga bayansu.

Sai ta juyo da sauri ta kalle su amma Madaki ya riga ta amsa musu.

“Ameen mun gode sosai.”

Sadiya bata ce komai ba, murmushi kawai take tana ɗan ɗaga mata gira har suka juya suka tafi.

“Bismillah…”

Muryasa ta sake fada daga samanta bayan su Sadiyan sun danyi nisa, sai ta sake juyowa ta kalle shi, cikin motar yake nuna mata alamun ta shiga. A hankali ta haɗiye wani abu a maƙogwaronta sannan ta shiga ɗin, kuma sanyin A.c ciki mai daɗi ya mata maraba zuwa duniyar Madaki da tayi kewa cikin kwanakin nan, ya biyo bayanta sannan ya rufe ƙofar yayin da Sunusi ke tsaye daga jikin booth ya juya musu baya.

Ta kalle shi da niyyar yi masa gaisuwa amma sai yayi saurin katse ta ta hanyar jawo ta kusa dashi don gaya mata abinda ke yawo a ransa tun ɗazu da idonsa ya sauka akan yatsun kafarta sanda take gaishe su a ɗakin Baddo.

“I missed you…” Ya furta a hankali yana ɗora goshinsa akan nata, numfashinsu ya hade waje guda.3

Jidda ta cije gefen leɓɓenta sannan ta rufe idanunta ba shiri, kalaman guda uku ne kawai amma bi da bi take ji suna tafiya suna kunna tarin jijiyoyi a ko’ina na jikinta.

Tayi kewarsa fiye da yadda shi baya tunani, tayi kewar wannan muryar tasa dama fuskarsa musamman da safe, tayi kewar yadda zata ganshi a duk sanda ya dawo daga office, dama aikin da zai zauna yana yi bayan isha’i, tayi kewar yadda ta fara sabawa da jikinsa a ƴan kwanakin nan, tayi kewar maganganun da ya gaya mata a masaukinsa da kuma yadda ta dinga hasashen faruwarsu ba tare da ta hasaso wannan tazarar ba.

Ta sake haɗiye yawu cikin maƙogwaronta a hankali tana wani lissafi, lissafin cewa a yanzu ko zata sadaukar da dukkan farin cikinta na duniya ne wajen farantawa Madaki rai zata yi, don me hausawa suke cewa ne? Wai Allah ya kashe ya baka in har ka sami wani abu da baka taba sa rai dashi, don haka a yanzu babu abinda zai hana ta kyautata zamansu, zata bashi amsar duk maganganun da ya gaya mata ran nan, zata cike guraben duk mutanen daya rasa a rayuwarsa, in yace zai koya mata yadda zata so shi, itama zata koya masa yadda zai so ta… Don ta riga ta yarda cewa shi ɗin dai shine ƙaddararta ƙaddarar data dade tana hasashen zuwanta, sai gashi ta ƙaraso mata ma a siffar alkhairi, dama masu iya magana sun ce, dukkan ƙalubalen da bawa zai fuskanta a rayuwarsa in yayi hakuri sai ya zame masa alkhairi.

Wannan shine nata ƙalubalen.

Tata ƙaddarar… Da take tamkar zanen dutse da ba wani abu da ya isa ya canja ta!

***