ZANEN DUTSE CHAPTER 2 BY AISHA-SHAFIEE

ZANEN DUTSE CHAPTER 2 BY AISHA-SHAFIEE
ZANEN DUTSE CHAPTER 2 BY AISHA-SHAFIEE                     Www.bankinhausanovels.com.ng  LARABA, TA BAWA RANAR SA’A.+ Kamar yadda burin kowacce uwa a duniyar nan shine ta aurar da d’iyarta da zarar ta kai munzalin aure, haka ma Baddo ke da wannan burin akan ki da kuma Jamila, kamar yadda jinkirin aure ga ‘yar ke sanya k’unci da damuwa a zuciyar kowacce uwa haka ma Baddo ta shiga wannan halin kafin Jamila ta samu tsayayyen da a yanzu har aka sanya musu rana. Kin sani Jidda, kin san hakan kuma kin san wannan yana daga cikin dalilin da yasa Baddo bata hana ki ganin Suraj tun farko ba saboda kar ta maimaita irin kuskuren da tayi akan Jamila ba wai don ta yarda dashi itama ba. Jamilar kad’ai kuma ta ishe ki misalin ganin irin ciwon dake cikin ‘Jinkirin aure’ ko kin manta lokutan da kike kamata a d’aki tana kukan da ma’anarsa bata wuce na yadda bayan danginku hatta mutanen dake kewaye daku ke mata kallon ‘K’ask’anci’ don kawai ubangiji bai k’addara aurenta a lokacin sa’anninta ba. Don haka kar ki…