ZANEN DUTSE CHAPTER 1 BY AISHA-SHAFIEE

ZANEN DUTSE CHAPTER 1 BY AISHA-SHAFIEE
ZANEN DUTSE CHAPTER 1 BY AISHA-SHAFIEE                   Www.bankinhausanovels.com.ng  Duk da girma irin na gidan sarautar KIYARI, babu lungu da sak’on da zaka kurd’a sautin wak’ar da ake gudanarwa daga can wajen kamun bikin bai shiga kunnenka ba, sannan ga mutane nan birjik! Tun daga bayi na cikin masarautar har zuwa tarin jama’ar gari da suke d’id’ikowa don gane wa idonsu shahararren bikin da aka fara gudanarwa a yau.+ Biki na gimbiya kuma ‘ya mace ta biyu a gurin mai martaba ‘Ahmad Uba Kamsusi’, Haka nan kuma biki na farko da aka fara gudanarwa a gidan sarautar tun bayan zamanin da mai martaba ya gaji mahaifinsa. Duk inda zaka duba ko ka kalla ado ne na k’awa anyi shi birjik cikin nau’i kala-kala don burge al’umma da kuma dangin ango wanda suma suka kasance jinin sarauta daga garin Sakkwato. Ba wai barin mutane ake su k’arasa can inda ake gudanar da Kamun ba, amma duk da haka saboda wadata abubuwa kai ba zaka ce ba ko’ina ake bikin ba, don kalolin abinci yawo kawai suke tsakanin mutane …