YARIMA MUS'AB CHAPTER 3

YARIMA MUS'AB CHAPTER 3
YARIMA MUS’AB CHAPTER 3                  Www.bankinhausanovels.com.ng  Yayi kokari kwarai wajen ganin yayi yaki da damuwar shi da safe ya isa bangaren Abbah ya gaidashi kamar yadda ya saba idan har yana gidan sedai sama² ya amsa mishi ba yadda ya saba ba murmushi yayi na gefen baki domin yasan makircin waccan matar ce don yana da yakinin ita ce ta zuga Abbahn nashi kan maganar daren jiya..+ Mikewa yayi ya nufi bangaren Ummi da sallama ya shiga suna zaune a falon tare da ita suna ta fira wanda rabi ta makarantar su ce bayan ya gaida ta suma suka gaidashi Hafsa ce ta fara gaidashi “Gud morning Yaya” ya amsa da “Mrng Wifeey” cikin yanayin shi na tsokana zaro idanu tayi kafin ta rufe fuska alamun taji kunya shikam dariya ma ta bashi Hafsatou cikin kulawa tace “Barka da safiya Yaya” murmushi yayi yana kallonta yace “Barka dai Bestyn mu hope kin tashi qlau” a takaice ta amsa da “lafia lau” nan Ummi tace “to maza masu lattin tashi tunda dai kun makara mukam munyi Breakfast sai Ku tashi maza kuj…