YARIMA MUS'AB CHAPTER 1 YARIMA MUS’AB CHAPTER 1 Www.bankinhausanovels.com.ng Tsaye suke ko wacce sanye da uniform mai launin ruwan madara (Milk colour) da kuma kore wanda bai turu sosai ba (Army green) riga da wando sai kuma hijab wanda kadan ya wuce kirjin su(ga musulmai kenan yayin da sauran kabilun zaka bambance su ta hanyar rashin hijab din)…… Dalibai kenan a makarantar ta GIWO SCIENCE ACADEMY dake hanyar barin gari in ka nufi Ningi (wato Kano Road) cikin garin na Bauchin Yakubu…..+ Tsaye a layin Assembly suna sauraren bayanin Principal din nasu cikin harshen turanci ko wacce ta kasa kunne tana sauraran shi in ka dauke dalibai guda biyu dake ta tadin su babu abinda ya dame su tsawa ya daka musu “Zainab nd Saudah! stop this nonsense” turo baki dayar tayi cike da rashin tarbiyya take ‘yan harare hararen ta. … Gama assembly keda wuya ko wacce ta shige ajinsu domin daukan darussa. Mafi yawancin daliban sun hada group ne as usual suna tattaunawa kan abinda Principal yace wato na zuwan d’an sar…