YAR LEKEN ASIRI CHAPTER 6 BY ANUP JANYAU (_SPY_?)

YAR LEKEN ASIRI CHAPTER 6 BY ANUP JANYAU (_SPY_?)
YAR LEKEN ASIRI CHAPTER 6 BY ANUP JANYAU (_SPY_?)                 Www.bankinhausanovels.com.ng  Wani irin taku Kuzeem keyi tamkar wata zakanya, cike da tsagwaron jarumta wacce batada algus. Yayinda Meerah ke gefenta sai Security’s da ke bayansu, har suka iso bak’in wani k’aton building, wanda a nan ne office d’in L.G Aliyu Iko yake.  Cikin sauri Security’s d’in wurin suka bud’e mata k’ofa tare da sadda kawunansu a k’asa saboda jin nauyin rashin bata girman da suka saba yi. D’an guntun murmushi Kuzeem tayi sannan ta shige ciki, ta bar su Meerah tsaye a wurin, don basuda izinin shiga ciki. Daidai lokacin wani Security ya iso wurin tare da shaida musu ana son ganinsu ga baki d’aya, hakan yasa suka bar wurin su dukansu. Ba shiri Major Khalil yayi saurin dakatar da dariyar da yake yi, yana mai sake tariyo ma k’wak’walwarsa yanayin kallon da Kuzeem tayi masa kafin ta bar office d’in. Hannayensa biyu ya hard’e a k’irji, tare da jinjina kai yace; “Tabbas akwai tarin ma’anoni a cikin kallon da tayi…