YAR LEKEN ASIRI CHAPTER 5 BY ANUP JANYAU (_SPY_?)

YAR LEKEN ASIRI CHAPTER 5 BY ANUP JANYAU (_SPY_?)
YAR LEKEN ASIRI CHAPTER 5 BY ANUP JANYAU (_SPY_?)                   Www.bankinhausanovels.com.ng       Cikin takunta mai tattare da jarumta ta tako har zuwa wurin da yake tsaye, tare da hard’e hannayenta a k’irji tana jifarshi da wani irin kallon raini. Saurin had’e rai yayi, don baya son ta fahimci yanayin tsoron da yake ciki, saidai ya makaro don tun kafin ta iso office d’in ta san halin da yake ciki.  “Da izinin wa kika shigo cikin office d’in nan?, tun wuri kiyi gaugawar ficewa kafin inyi mummunan sab’a miki, don baki kai matsayi tare da darajar da zaki kwaso k’azaman k’afafuwanki ki shigo min cikin office ba. Oya get out of my office!”. Major Khalil ya fad’a mata a d’an daburce, don ba k’aramin rikita shi Kuzeem tayi da kallonta ba.  Wani murmushin gefen baki tayi sannan tace; “Kwantar da hankalinka zan fita ba ma sai ka koreni ba. Saidai kafin nan ina so in gargad’eka akan kada ka sake kuskuren yin abinda ka aikata. Banada wata mummunar manufa a kanka, da tuni na tona maka asiri sabod…