YAR LEKEN ASIRI CHAPTER 10 KARSHE BY ANUP JANYAU (_SPY_?)
YAR LEKEN ASIRI CHAPTER 10 KARSHE BY ANUP JANYAU (_SPY_?) YAR LEKEN ASIRI CHAPTER 10 KARSHE BY ANUP JANYAU (_SPY_?) Www.bankinhausanovels.com.ng ___________________________ “Wannan wanne irin shirmen banza ne?, taya zaku bari ta shammace ku?, na san halin Fatima kamar yinwar cikina, ga dukkan alama kunyi sakacin da har ta gano kuna bibiyarta saisa ta sanja taku”. Inji Abba da ke tsaye a tsakiyar palornshi, wayarshi kare a kunne alamar waya ce yake, d’an shiru yayi yana sauraron su Rabson kana yace; “Zan baku dama ta k’arshe, da zaran kunyi sake da ita shikenan kwangilar ta wuce ku”. Yana gama fad’in haka ya ciro wayar daga kunnenshi tare da katse kiran. “Alhaji me kake shirin yi ne?”. Ammah ta tambaya, don tun d’azun take tsaye a palorn tana sauraren wayar da yake ba tare da ya sani ba. Saurin juyowa yayi ya kalleta, sai kuma ya sauke ajiyar zuciya yace; “Hafsa wannan bai shafe ki ba”. “Ban gane bai shafeni ba Alhaji?”. “Kamar yanda kika ji na fad’a miki ba!”. Abba na gama fad’in haka ya nufi hanyar bedroom d’insa ya bar ta nan tsaye, g…