YAR LEKEN ASIRI CHAPTER 1 BY ANUP JANYAU (_SPY_?) YAR LEKEN ASIRI CHAPTER 1 BY ANUP JANYAU (_SPY_?) Www.bankinhausanovels.com.ng Bismillahir Rahmanir Rahim. A hankali wani Yellow Helicopter ya fara saukowa a tsakiyar sunk’umin dajin mai fad’in gaske. yana gama saukowa k’ofar jirgin ta bud’u, ba b’ata lokaci na cikin jirgin suka fara fitowa da sauri-sauri har suka fice ga baki d’ayan su. Mutane biyar ne, Maza biyu Mata uku. Hud’un cikinsu riguna farare ne a jikinsu, sai d’ayar macen dake sanye da red t-shirt, saidai matan sun d’ora wata leather jacket a saman rigunan jikinsu, kansu kuma sanye yake da sun hats, sai wasu black wellingtons boot dake sanye a k’afafuwansu. Ko wanensu akwai k’atuwar Backpack goye a bayan shi. Dukansu tsaye sukayi suna k’arema dajin kallo wanda yake kallo, don kuwa dajine ba k’arami ba, saidai bayada wadatattun bishiyoyi a cikinshi, saisa duk inda ka d’ora idanuwanka iya ganinka. “Anya! dajin nan lafiya yake kuwa?”. Cewar d’aya daga cikin mazan yana cigaba da wulga idanuwansa …