WATA MACE CHAPTER 6 BY SANA S MATAZU

WATA MACE CHAPTER 6 BY SANA S MATAZU
WATA MACE CHAPTER 6 BY SANA S MATAZU                 Www.bankinhausanovels.com.ng  Look Ramlatu kinsan dai abinda ki ke be dace ba. Ta yaya na kai kuɗi gidanku amma kuma kina tsayawa da samari kuma dan cin fuska a gabana?” “Dakata Kabir, ni fa allura ce acikin ruwa ta yaya zan tsaya ka yi min sakiyar da ba ruwa. Na sani ko ƙarya ka ke ba aurena zaka yi ba, sai na gama sakankancewa sannan in ji wuf ka fece!” Wani miyau ya haɗiya yana jin kansa yana yi masa nauyi, “Be san abinda ya ja shi ga auren Ramlatu ba, duk da zuciyarsa ce ja gaban kwaɗaitar da shi cewa ita ce ta dace da shi amma kuma yana ganin kamar ya yi kuskure” Kallonta yake idanunsa jajjur, amma kuma wata shakkarta da be san dalilinta ba tana mammayeshi. Kamar wanda aka datsema baki ya kasa tanka mata haka ta juya tana girgije-girgije. Ƙasan ransa ya na jin kewar Zahidaht da komai nata. “Shikenan Ramlatu ki faɗa ma su Baba ji bi za a zo batun saka rana kuma wata ɗaya nake buƙata!” Guɗa ta yi tare da kai masa hug, “amma ka biyani wal…