WATA MACE CHAPTER 1 BY SANA S MATAZU

WATA MACE CHAPTER 1 BY SANA S MATAZU
WATA MACE CHAPTER 1 BY SANA S MATAZU                  Www.bankinhausanovels.com.ng  Tun daga bakin ƙofar gidan ta ke jiyo muryarta cike da rauni, waƙa ce take rairawa murya a sarƙe. A haka ta ƙarasa shigowa gidan, mammaki ya kasheta ganin hawaye a idanun Labiba. Bata ƙara tabbatar da mamakinta ba sai da ƙamshi mai ni’ima ya sami masauki a massarafar shaƙar numfashinta. Jiki a sanyaye ta zauna idanunta cikin nata. daidai lokacin da ta ƙara ɗaukar wata waƙar, “Zamantakewa ba ƙarya ne ba. Cin amanar soyayya, an rabani da me sona” Jikin Amina ya ƙara sanyi, bata taɓa tunanin akwai ranar da zata ga nadama a idanun Labiba ba, bare kuma zubar hawaye. Lallai masu iya magana sun yi gaskiya, duniya juyi-juyi ce. Tunaninta ya katse lokacin da hannunwan Labiban suka sarƙafo nata hannuwan murya a raunane ta furta, “Yaya Amina ke ma murnar ki ke yi? Kina cikin masu murna an min saki ɗai-ɗai har guda uku? Kodayake ba kowa ya cuceni ba sai yaya Khamisu da bai sakasu sun je sun daki Yusuf ba da bai sake ni…