TAWA TA SAMENI CHAPTER 14 BY HALIMA ABDULLAHI K/MASHI

TAWA TA SAMENI CHAPTER 14 BY HALIMA ABDULLAHI K/MASHI
TAWA TA SAMENI CHAPTER 14 BY HALIMA ABDULLAHI K/MASHI Www.bankinhausanovels.com.ng  MUN TSAYA  na dubi kayan jikinshi kampala green nima haka sai naji tamkar na koma na cire ya dube ni zo muje na saukeki nace ka barshi yace duk da nayi latti sai na kaiki,dole na shiga muna shirin fita yayanmu ya shigo shi da wasu abokanshi cikin kayan training duk da kaninshi ne sai da gabana ya fadi yako tsira mana ido sai ya tsaida motar ya dubeni yace kin mani shara?na dubeshi yayi wani kicin kicin nace a’’a yace to fita ki min bai saurari amsata ba yayi gaba na dubi yaya Kabir nace to kaji fa abinda yace,yaya Kabir yace don Allah ki rabu dashi bari mu tafi nace wai ba haka a tsakaninmu haushi ya kama yaya Kabir yace toko dai yana sonki ne?nace kaji ka da wata magana kaima kasan ko mata sun kare yayanmu ba zai soni ba yace saboda me kikace haka?nace ni nasan bani da kyau kuma gani baka yayi murmushi sannan yace ganinki kenan kina abubuwa masu fizgar hankali so ni dai yanzun ki yarda na fito sai a hada …