TAKOBIN DAUKAKA CHAPTER 4 BY MANSUR USMAN (SUFI) TAKOBIN DAUKAKA CHAPTER 4 BY MANSUR USMAN (SUFI) Www.bankinhausanovels.com.ng MUN TSAYA dattijuwar mata mai kimanin shekaru hamsin ta rugo izuwa inda sarauniyar lasmirat take ta zube Kasa bisa gwiwoyin ta ta kwashi gaisuwa Bakin ta na kyarma kuma kanta a sunkuye tace “me kike da buKata ya shugaba ta? Lasmirat ta dube ta tace”’ yake zarima kiyi sani cewa bakomai nake da bukata ba face ina so wannan bako dake tare da ni a basa kulawa da dukkanin wani abu da ya . . bukata kiyi sani cewa yana da matukar muhimmanci agareni . . Koda jin wannan batu sai zarima ta sake risina wa tace ” , angama ya shugabata bin umarnin ki ai shi ne ibada ta, – ‘Tana gama fadin hakan ta mike tsaye tana Mai yiwa saurayi yaslir nuni da ya biyo bayan ta ‘. Batare da bata lokaci ba yaslir ya kama linzamin dokin sa ya sauko sannan ya rufa mata baya Amma koda ya waiga ya hada idanu da sarauniya lasmirat sai yaga tana yi masa wani mayataccen kallo mai dauke da alamar tambaya. ZAMU TASHI ~ Cikin hanzari sarauniya lasmir…