SHU'UMIN NAMIJI CHAPTER 8 BY FATYMA SARDAUNA SHU’UMIN NAMIJI CHAPTER 8 BY FATYMA SARDAUNA Www.bankinhausanovels.com.ng Yajima zaune a kan gadon nasa, gaba ɗaya kansa ya kulle yarasa meke damunsa, wai shin da gaske SO yake ko kuwa? anya kuwa yanaga zaman sa haka zai yi wu? zaifi masa kyau yanemi Abid domin shi ne kaɗai zai iya fayyace masa halin da yake ciki, tabbas shi koda son Zahrah Abid ɗin yace masa yanayi yanzu bazai musa masaba, idan kuwa har haka so yake to yana mawa Zahrah so me tsanani, saurin laluɓar wayarsa ƙirar Samsung dake kusa dashi yayi. Numbern Abid ya dannawa ƙira, bugu biyu Abid ya ɗaga ƙiran cikin muryan kasala yace “Mutumin ya akayi ne, ka katseni ina cikin holewata”+ “mcheeww aikin ka kenan cin ƴaƴan mutane, kana ina yanzu inaso muyi serious magana da kai” Zaid yafaɗi haka cike da zaƙuwa. Miƙa Abid dake kwance shame shame a gado yayi haɗe da sakin daria, wai yau shi Zaid ke cewa baida wani aiki se cin ƴaƴan mutane, hmm ai duk iskancinsa shikansa yasan a ƙarƙashin Zaid yake, domin kuwa I…