UNCLE NE CHAPTER 9 BY NIMCYLUV
Www.bankinhausanovels.com.ng
Lamo tayi jikinsa tana sauraran daddaÉ—ar murya dake fita a hankali cike da nutsuwa kamala addini haiba, numfashi ya sauke kafin yace “jeki Æ™wanta” turo baki tayi tace “to baka daÉ—i yadda ake tsarkin ba..
Hancinta yaja yace “ni ban iya ba to”duk da baccin dake cinta bai hana tayi dry ba cikin siririyar muryarta tace “Allah Uncle ka iya,ai komai kai ka iya kafi kowa” baice mata komai ba sai lips É—inta da ya tsorawa idanu yana kallon yadda ta jiÆ™asu da yawo sai mutsawa suke a hankali, É—auke kansa yay yace “A taÆ™aice TSARKI kashi biyu ne,Hadasi da Kabasi amma zan buÉ—a maki bayanin yadda zaifi, hope zaiki fahimta?” Kanta dake saman Æ™irjinsa ta É—aga alamar “eh” shafa sumar kanta yay shima yace “good” kana yay shuru yana tunanin irin duguwar maganar da zaiyi a wannan daren, ajjiyar zcya ya sauke kafin ya É—ura da faÉ—in.
Ma’anar Tsarki
Ma’anar Tsarki A Larabci.
Tsafta Da Tsarkaka Daga Kazanta
Ma’anar Tsarki A shari’a
Kawar da kari da gusar da Najasa
Kashe ‿ Kashen Tsarki
1- Tsarki Na Voye
Shi ne tsarkake zuciya daga shirka da sabo, da duk wani abin da yake bata zuciya, babu yadda tsarki zai tabbata matukar akwai shirka a cikin zuciya, kamar yadda Allah ya ce, “Yaku wadanda suka yi imani ku sani cewa Mushirikai najasa ne, kada su kusanci masallaci mai alfarma daga wannan shekarar, idan kuna jin tsoron talauci to da sannu Allah zai azurta ku daga falalarsa in ya so. Haqiqa Allah Masani ne Mai hikima.‿ (At-Tauba : 28).
Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم ) ya ce, “Mumini ba ya zama najasa‿. [ Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi]
2- Tsarki Na Zahiri
Shi ne tsarkake jiki daga abubuwan da suke warware alwala da najasa, ya kasu gida biyu :
1- Tsarkin Kari
Kari shi ne : Abin da yake hana mutum yin ibadar da aka sharxanta tsarki a cikinta, kamar sallah, dawafi da waninsu. Kari ya kasu kashi biyu :
Kari yana hana yin sallah.
– Qaramin Kari
Shi ne wanda yake wajabta yin alwala, kamar fitsari da kashi da sauran abubuwan da suke warware alwala. Tsarki daga kari yana samuwa ne ta hanyar alwala.
Allah ya ce, “Yaku waxanda kuka yi imani idan kun tashi za ku yi sallah, to ku wanke fuskokinku da hannayenku zuwa gwiwar hannu, ku shafi kawunanku ku wanke kafafunku zuwa idon sawu‿ (Al-ma’ida :6).
Alwala tsarki ce daga qaramin kari
– Babban Kari
Shi ne wanda yake wajabta wanka, kamar janaba, haila, da wanin haka, ana tsarkaka daga gare shi ta hanyar wanka.
Allah ya ce, “Idan kuna da janaba to ku yi tsarki‿ (Al-ma’ida : 6).
Tsrkin jiki
2- Tsarkaka Daga Najasa
Gusar da najasa wajibi ne, saboda faxin Allah Maxaukakin Sarki “Ka tsarkake tufafinka‿ (Al-Muddassir 4).
Da faxin Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم ) “Mafi yawancin azabar qabari daga rashin yin tsarki ne idan an yi fitsari‿. [ Ibn Majah ne ya rawaito shi]
Da faxinsa ( صلى الله عليه وسلم ) “Idan xayanku ya zo masallaci to ya duba takalmansa, idan ya ga qazanta ko najasa to ya goge, sannan ya yi sallah da su‿. [ Abu Dawud ne ya rawaito shi]
Tsarkin jiki
Tsarkin wurin sallah
Tsarkin tufafi
Kashe-Kashen Ruwa
Na farko : Ruwa Mai Tsarki
Shi ne ruwan da najasa ba ta canza kamaninsa, ko xanxanonsa ko qanshinsa ba, kamar:
1- Ruwa Tsantsa
Shi ne ruwan da yake akan siffar shi da aka halicce shi da ita, kamar ruwan sama, ko qanqara, ko rava, ko kuma wanda yake gudu ne a bayan qasa, kamar ruwan teku, da qoramu da na sama, da rijiya. Allah Maxaukakin Sarki ya ce, “Mun saukar da ruwa mai tsarki daga sama‿ (AlFurqan : 48)
Allah Maxaukakin Sarki ya ce, “Yana saukar muku da ruwa daga sama don ya tsarkake ku da shi‿ (Al-anfal : 11)
Hakanan Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم ) yana addu’a yana cewa: “Ya Allah ka wanke ni daga zunubaina da rava da ruwa da qanqara[ Qanqara: Ita ce qanqarar da take zuba ya yin saurkar ruwan sama.]‿. [ Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi]
Manzon Allah ya ce dangane da ruwan teku “Shi ruwa ne mai tsarki, kuma mushensa halal ne‿. [ Ahmad da Abu Dawud ne suka rawaito shi].
Numfashi ya sauke,bayan ya gama dugun bayani akan tsarki,a hankali kuma ya leÆ™a fuskarta, murmushi ya saki sbd fararan idanunta daya hango suna juyawa alamar dai tana fahimtar zancen sa,gyara kwanciyarsa yay a saman kujerar kafin ya lumshe idanunsa yana sauraran bugun zcyarsa dake fita da sauri da sauri,cikin Æ™asa da murya kuma yace “sai kuma bayani akan WANKA en matan Uncle” É“oye fuskarta tayi a jikinsa tana sakin wani sound “uhm…uhm”cije lips É—insa kawai yay kana yace “shima wanka kashi-kashi ne a musulunce,WANKA ya kasu kashi BIYAR sune WANKAN HAIHUWA,WANKAN JANABA,WANKAN JUMA’A,WANKAN SHIGA MAKKAH,WANKAN MUTUWA”
shuru yay yana nazartar ta ya faɗa mata ko kuma ya rabu da ita,domin baya so ya faɗi abinda zata zo tana masa surutu akai,sai dai kuma maganar addini babu kunya ko ɓoye wani abu,domin shekarunta sunkai tasan komai, pouting lips ɗinsa yayi kafin yace.
Ma’anar kalmar “wanka” a larabci
Game abu da ruwa,
Wanka a Shari’ance
Shi ne gama jiki gabaxayansa da ruwa, a kan wata siffa kevantacciya, da niyyar bautawa Allah Mai tsarki
Abubuwan Da Suke Wajabta Wanka
1- Fitar Maniyyi
Maniyyi wani ruwa ne fari mai kauri, wanda yake fita tare da jin daxi, yana tunkuxar juna yayin fitowa, mutuwar jiki tana biyo bayan fitarsa, yana wari irin warin bara-gurbin qwai.
Allah Madaukakin Sarki ya ce, “Idan kun kasance kuna da janaba to ku yi wanka‿ (Alma’ida : 6)
da faÉ—in Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم ) ga Aliyyu : “Idan ka fitar da ruwa to ka yi wanka‿ [Abu Dawud ne ya rawaito shi].
Fitar da ruwa ana nufin fitar maniyyi…,”da sauri Jalilerh ta É—aga ta kallesa,bai kalleta ba ya haÉ—e rai hakan yasa dole ta maida kanta taci gaba da sauran sa.
Yace “misali shine
1- Idan mutum ya yi mafarki amma bai fitar da maniyyi ba, to babu wanka a kanshi, idan kuwa maniyyin ya fito bayan ya farka daga barcin to wajibi ne ya yi wanka.
2- Idan ya ga maniyyi, amma bai iya tuna yaushe ya yi mafarki ba, to wanka ya wajaba a kanshi saboda fitar maniyyin. Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم ) ya ce, “Ana tava ruwa ne saboda fitar ruwa‿ [ Muslim ne ya rawaito shi] Ma’ana ana yin wanka ne don fitar maniyyi.
3- Idan ya ji alamar zuwan maniyyi daga gabansa, amma bai fito ba, to babu wanka a kanshi.
4- Idan maniyyi ya fito saboda wani dalili ko rashin lafiya ba tare da sha’awa ba, to babu wanka a kanshi.
5- Idan mutum yana janaba ya yi wanka, sai kuma maniyyi ya fito bayan ya gama wankan, to ba sai ya sake wankan ba, saboda yawanci yakan fito ne ba tare da sha’awa ba, amma abin da ya fi ya yi alwala.
6- Idan mai barci ya farka, ya ji danshi a jikinsa, amma bai san dalilin zuwanta ba, to xayan abu uku ne :
A) Ya tabbatar da wannan danshin maniyyi ne, to wanka ya tabbata a gareshi, ya tuna ya yi mafarki ko bai tuna ba.
B) Ya tabbatar wannan danshin ba maniyyi ba ne, to wanka bai wajaba a kanshi ba, hukuncinsa hukuncin fitsari ne, sai ya wanke)
C) Ya yi shakka, maniyyi ne ko ba shi ba ne? To a nan wajibi ne a kanshi ya yi kirdado, idan ya tuna abin da zai nuna masa cewa wannan danshin maniyyi ne, to ya bar shi a kan maniyyi ne. in kuma ya tuna abin da zai nuna masa cewa maziyyi ne, to maziyyin ne, in kuma ya kasa tuna komai, to sai ya yi wanka don fita daga savani da ruxu.
7- Idan ya ga maniyyi, amma bai tuna yaushe ya yi mafarkinsa ba, to wanka ya wajaba a kanshi, ya kuma sake dukkan sallar da ya yi bayan tashinsa daga barcinsa na qarshe.
2- Saduwa (Jima’i)
Shi ne haÉ—uwar gaban namiji da na mace, wato shigar kan gaban namiji zaya sanya cikin farjin mace, ko da kuwa bai zubar da maniyyi ba, saboda faÉ—in Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم )“Idan kaciyar (namiji) ta shige kaciyar (Mace) to wanka ya wajaba‿ [Tirmizi ne ya rawaito shi].
3- Musuluntar Kafiri
Saboda “Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم ) ya umarci Qaisu É—an Asim ya yi wanka lokacin da ya musulunta‿ [Abu Dawud ne ya rawaito shi]
4- É—ukewar Jinin Haila Da Na Biqi
Saboda hadisin Aisha cewa Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم ) ya cewa FaÉ—imatu ‘yar Abi Hubaish “Idan al’adarki ta zo, ki bar sallah, idan ya wuce ki yi wanka ki yi sallah‿ [Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi].
Hukuncin jinin biqi kamar hukuncin jinin haila ne da ijma’in malamai.
5- Mutuwa
Saboda faÉ—in Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم ) a hadisin wanke ‘yarsa Zainab lokacin da ta rasu ya ce,“Ku wanketa sau uku, ko sau biyar, ko fiye da haka, in kun ga akwai buqatar hakan‿ [ Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi].
Yadda Ake Yin Wanka
Abin da yake wajibi a wajen wanka shi ne gama jiki gaba É—ayansa da ruwa, tare da yin niyya, koma yaya ya yi shi.
Sai dai abin da aka fi so ya yi koyi da siffar wankan Annabi ( صلى الله عليه وسلم ), kamar yadda uwar muminai Maimunatu ta siffanta shi, ta ce, “Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم ) ya sanya ruwa don yin wankan janaba, sai ya karkato abin ruwan da hannun damansa a kan hagunsa ya wanke hannayensa sau biyu ko sau uku, sannan ya wanke gabansa, sai ya doki qasa ko bango da hannunsa sau biyu ko sau uku, sannan sai ya yi kurkurar baki ya shaqa ruwa, ya wanke fuskarsa da sangalin hannunsa, sannan ya kwara ruwa a kansa, sai ya wanke jikinsa, sannan ya matsa gefe guda ya wanke qafafunsa. Nana Maimunatu ta ce, “Sai na kawo masa wani qyalle (hankici) amma bai karÉ“a ba, sai ya riqa share ruwan da hannunsa‿ [Bukhari ne ya rawaito shi].
– Yadda ake wankan a taqaice shi ne :
1- Zai wanke tafukan hannayensa sau biyu ko sau uku.
2- Zai wanke gabansa
3- zai doki qasa ko bango da hannu sau biyu ko sau uku.
4- Sai ya yi alwala irin ta sallah, ba tare da shafar kai da kunne ba.
5- Zai kwara ruwa a kansa
6- Zai wanke jikinsa gaba xaya.
7- Zai koma gefe ya wanke qafafunsa.
Bayan ya kammala ya sauke wata wahalalliyar ajjiyar zcya tare da jan numfashi yace “kinji wanan” shuru yaji sai kuma yaji saukar numfashinta mai zafi a saman Æ™irjinsa, leÆ™awa yay yaga tuni bacci ya É—auke ta,waro idanunsa yay da mamaki yana addu’ar Allah yasa dai duk taji me yace bai wahalar banza ba, miÆ™ewa yay da ita a jikinsa tare da ficewa daga É—akin,kai tsaye parlour ya nufa,a zaune ya samu Mama tana cin soyayyan nama da kuma lemo,kallo guda yay mata,ita kam baki ta saki tare da rafka salati tace “me zan gani yau?wai É“atan nono a Æ™irjin budurwa,zabgegiyar budurwa ka É—auka kamar yarinyar goye,maza maza sauketa na gani”haÉ—e rai yay kafin yace mata “hannunki ne?” Cikin Æ™ufula tace “to sallamamme yimin rashin kunya,da matarka ka É—auka ma da sauÆ™i” waro idanunsa yayi waje kafin yace “ok bari na ajjiye ta na É—auke ki” zama tayi saman kujera tare da fasa kuka tace “wlh ba hali na ka É—auka ba sai dai na dangin ubanka,amma tirrrr da mummunan hali irin wannan yanzu ni zaka É—auka Jalalu?” Mummy dake saman upstairs ta danne dryar dake cinta kafin tace “Bobo maza jeka Æ™wantar da ita kazo ka shige ka bamu waje” baice komai ba ya haura upstairs É—in,yana zuwa ya nufi part É—in su,babu wani haske É—akin sai wani light blue bed É—in ta ya nufa ya Æ™wantar da ita,kana ya zare nata hijab tare da gyara mata kwanciyar, jikinsa yazo zamewa tayi sauri riÆ™esa tare da turo baki gaba,kai kawai ya girgiza ya É—auki Æ™aramin pillow ya saka mata da sauri ta rungome pillow,sosai yay mamaki yadda tasan daÉ—in jiki gashi shi duk lokacin da suka É“ata babu abinda yaji a kanta,tsaki yaja kana ya tofa mata addu’a ya rufeta da duvet,wajan Nihila ya Æ™arasa tana jin zuwansa tayi saurin rufe idanunta,ba tare da wani tunani ba,itama yay mata addu’a kana ya bata light kiss a saman goshinta ya gyara mata kwanciya, remote ya É—auka ya Æ™aro masu gudun a.c kafin yaja Ƙofar ya rufe,da idanu ta bisa harya fice daga É—akin kafin ta juya ta kalli Jalilerh wacce take bacci cikin nutsuwa ta rungume pillow,rufe idanunta tayi a haka bacci itama ya É—auke ta ta.
Washegari,tun safe Jalal yabar gida sbd saura Æ™wana guda Election,kusan a office ya Æ™are yininsa,daga Wannan mutane suzo sai wannan suzo,haka yayta manyan baÆ™i wasu kuÉ—in compaign,wasu kuma abubuwan zaÉ“e suke karÉ“a, Jafar kuma yana can shida Prince Hassan suna ta shiga local government da Æ™auyika, Abbou ma ba’a barsa a baya ba dukkan abinda yake gani zai taiamy É—an nasa dashi shi yake, kuÉ—i kowa ya fitar babu adadi,haka Irfan Imran kowa da nasa É“angaren, Mummy da Mameey suma a gida sukai taran mata aka cika sosai yadda Hajiya Atine, Aryan kam yana É—aki abinda yana sharar bacci sabida bashi da matsala da wani zaÉ“e a cewarsa, Governor Mubarak Yahya cibo hankalinsu Æ™wance yake shida masu mara masa baya da kuma Lamir,domin sun tabbatar a wannan karan plan É—insu bazai taÉ“a barin Dr/Muhammad Jalal Kabeer bobo ba,Lamir ya ajjiye juice É—in dake hannunsa yace “ai wlh da zarar an saki wannan vedio kare bazai iya binsa ba,badai sakarar É—an uwan nasa na É—ura sa bisa hanya ba,to Tabbas nan da jimawa zance ya turo min da vedio’n ta whatsapp, mu kuma zamu sakesa matsayin breaking news kaga shi kenan mun tashi hankali jama’ar IBADAN,zamu sanya masu shakku da wasi-wasi a zuÆ™atansu,kasan mene zai faru Æ™arshe?”gaba É—aya suka ajjiye juice É—in hannunsu suna kallonsa kafin Hon Faisal Lawan yace”wannan kitimurmurar ai naka ne,tayaya zamu sani?”dry Lamir yyi kafin ya tsuke bakinsa yace “daga Æ™arshe hukumar inec za tace the election was cancelled”gaba É—aya suka saka dry hadda riÆ™e ciki, Wani mutum a cikinsu wanda ake cewa Baba Tunde yace “kai Lamir you’re so selfish,kai mugune exactly abinda nake imagine kenan” ya faÉ—a cikin gurÉ“tacciyar hausarsa,Hon Faisal Lawan yace “kaga ana haka za’a Æ™ara tabbatar da Ur excellence a matsayin cikakken Gwamnan jihar Ibadan” gyaran murya Governor Mubarak Yahya cibo irin a dole yama riga daya zama Governor lokacin kawai yake jira,yace “idan harshashenmu ya zama gaskiya kowa ni kaÉ—ai nasan me zan maku,albashin na kune,zan dauwama ina maku hidima,and tuggun farko da Jalal zai fuskanta rabashi da wannan Æ™abilar da zanyi kuma saina tabbatar maku da magana ta gsky ce”
Jalal bai dawo gida ba sai wajan 12:30,a hankali drever yayi parking motarsa sai kuma motocin securities É—insa,yana parking wani security ya buÉ—e masa Æ™ofa,cikin nutsuwa yake tafiya hannunsa riÆ™e da babbar rigar sa daya cire a hanya,ya É—an tura hular kansa baya,gaba É—aya a gajiye yake bama gajiyar ke damunsa ba sai yadda yake yawon faÉ—uwar gaba wacce bai san menene dalilin afkuwarta ba,murya can Æ™asa yay sallama, Mummy na ganinsa ta miÆ™e da sauri tare da amsar rigar hannunsa sai jera masa sannu take,da idanunsa kawai yake kallonta ya kasa cewa komai, É“ata fuska tai tamkar zatai kuka tace “wanne irin abune wannan wai?ace tun safe daga fita sai yanzu?ina da tabbacin ko abinci baka ci ba” ta faÉ—a tana É—ura hannunta a cikinsa,zaro idanu waje tayi kafin tace “what ina zuwa zauna a parlour ka jirani” Mama ta amshe zan can da faÉ—in “ke kuma saiki kama gabanki tunda ya dawo,algugguma ka ganta nan ta hana ranta sakat sbd baka dawo gidan ba,daga Æ™arshe ma kuka ta sawa Mutane”ta Æ™are maganar tana nuna Jalilerh wacce take tsaye tun shigowar sa,yana da inda Mummy ta ajjiye sa ya É—aga gajiyayyun idanunsa ya sauke a kanta,cikin Sa’a suka haÉ—a ido,da sauri ta janye nata idanun kana ta haura upstairs tana goge hawayen idanunta, idanunsa yaja ya rufe ba tare da yace wani abun ba,kallonsa Mama tayi tace “to Mijin yaya ake ciki ne yanzu?” Shuru yay mata dan baya jin zai iya mata amsa,dan ko yawon dazai haÉ—iya a bakinsa babu,yana nan zaune Mummy ta fito daga kitchen hannunta riÆ™e da wani babban tray,tana zuwa ta ajjiye saman carpet kana ta kallesa tace “sauko Æ™asa” bai mata musu ba ya sakko yana sakkowar ya zame rigar dake jikinsa,ya rage sai farar singlet a jikinsa,dugwayen Æ™afafunsa ya miÆ™e har Æ™arar gajiya sukai,duk abinda yake akan idanun Mummy sosai take tausayin É—an nata musamman yau,tasan dukkan abinda daza ta basa a yanzu ba lalle yaci ba,dambun shinkafa wanda yaji zugale da gyaÉ—a da kuma manyan albasa,yasha kayan Æ™amshi da zallar hanta ta zuba masa a plat,sai kunun gyaÉ—a mai zafi da zuba masa madara kana ta haÉ—a masa mug,sai kuma Æ™waÉ—on zugala data haÉ—a masa yasha tomato da albasa da kuma Æ™wai,da haÉ—aÉ—É—an Æ™uli,gaba É—aya ta jere masa a gabansa,kamar yaro haka Jalal ya kwaÉ“e fuska tare da langwaÉ“ar da kansa gefe, cikin wata muryar sangarta yace “Mummy na gaji bacci” bata kulasa ba taja Æ™afarsa ta É—ura saman cinyarta ta fara matsa masa su tare daja masa yatsun Æ™afarsa,zuro Mama tayi masu da idanu,domin a wannan lokacin tunanin mahaifiyar Jalal ne fal a Zcyarta,ko tana raye ko babu uhhhu,bayan Mummy ta matsa masa Æ™afar ta miÆ™e tsaye tare da faÉ—in “bari na kira daughter, Æ™ilan taci abinci yanzu” harya buÉ—e baki zai magana sai kuma yay shuru sbd wayarsa da yaji tana ringing,kallon makeken screen É—in wayar yay yana sunan Jabir na yawo akai yay,rasa waye Jabir yay har wayar ta yanke yana kallon screen É—in,a haka wani kiran ya shigo, É—auke kai yay tare da É—aukan spoon ya fara cin Æ™waÉ—on zugalan a hankali,yana zaune Aryan ya fito da sauri daga part É—insu yay waje,da sauri Aryan ya buÉ—e wayarsa da tun É—azo take a rufe,yanzu haka yazo buÉ—ewa wane domin ya tura wasu photona da vedio’n,fuskarsa fal farin ciki ya buÉ—e wayar sai dai abin mamaki wayar na gama buÉ—ewa yaga ta nuna an mata waifin,ta nuna restore…A tsorace Aryan yake bin wayar da kallo, lokacin daya tabbar komai na kan wayar ya tafi yasa hannu ya dame kansa, zcyarsa cike da Æ™unci yana mmkin yadda hakan ta kasance,yasan cewa rabonsa da wayar tun jiya da daddare sabida killace tan da yay,yana jiran lokacin da Baaba Lamir zai masa magana ya turo masa,sai gashi yanzu babu komai akan wayar ya rasa muhimman abubuwa bayan photonan da vedio’n,cikin takaici ya koma cikin gida,yana shiga ya shige part É—insa, Jalal na zaune yana cin Æ™waÉ—on zugalan ko kallon Aryan bai ba, cikin nutsuwa yake komai,ganin yana zaune kuma ya tabbatar Mummy baza ta barsa ya tashi ba,kawai sai data ya shiga network,kai tsaye twitter ya shiga ya fara duba news harya zo tweet É—in wani mutum daya sanya photon Jalal a Æ™asa kuma yasa _Garkuwar al’ummar gari Ibadan,dukkan farin ciki da kwanciyar hankali su tabba a gareka,in sha Allah garin Ibadan naka ne,nasara takace,kai ne jagoran mu ur excellence Dr Muhammad Jalal Kabeer bobo_ Murmushi ne ya subuce masa lokacin da ya ga Retweet É—in mutane sama da 5k,bayan ya gama kallon Tweet É—in daya samu lokaci,ya shiga wajan Tweet shima ya fara typing kamar haka _Allahamdulillah,Dukkan yabo ga godiya sun tabbata ga Allah subhanahu wata’ala daya bamu a ron dai da kuma lafiya kuma yake shirin nuna mana gobe,wacce ta kasance rana mai muhimmanci a gareni ta kuma dukkan masoyina,bana da wani abu dazan birgeku dashi ko zan kyautata maku dashi a halin yanzu,nasan soyayyar ku gareni daga rabbil samawati take, soyayya kuma domin Allah itace soyayya,to jama’a ban taÉ“a nema ba,kuma ban san yaya daÉ—insa ko wahalarsa yake ba,ni nasan ina nema da dukkan lafiya ta,ilimi na,arziÆ™ina,ina fatan kuma zaku nuna min zallar soyayya ta hanyar sanyamin albarka da kuma kaÉ—amin Æ™uri’unku masu albarka kuma wanda zasu zamu Garkuwa gareni, ku/ki/ka tashi maza da mata aje a fita zaÉ“e domin tabbatar wa kanku kun zaÉ“e dai-dai da ra’ayinku,Ni Dr Muhammad Jalal Kabeer bobo nake cewa Æ™uri’ata Æ´an cina_
Yana gama rubuta yaka ya saki Tweet (posting na twitter shi ake cewa Tweet, comment kuma Retweet) tun kafin ya fita COMMENTS ɗin mutane suka fara rubdugu wasu na kurar wasu, lokacin guda aka haɗa masa COMMENTS sama da 2k screenshot yay na Tweet ɗin ya shiga account ɗinsa na I.G nan yaga flowers ɗinsa sun ƙara yawa fiye da ko yaushe,shiga yayi ya ɗura screenshot ɗin,tun kafin ya fita nan ma aka fara like and COMMENT, comment na farko ya bashi dry ina wata take cewa
_Daman ka iya hausa?ko daman kai bahaushe ne i through kai Balarabe ne, serious ina son ganinka a zahiri ba photo ba,gani nake kamar photon na rage maka ƙyau,all the best_
Murmushi yay lokacin daya gama karanta comment É—in kana ya kashe datar wayar,yana nan zaune Mummy ta sakko dwonstrais É—in hannunta riÆ™e dana Jalilerh, É—an waro manyan idanunsa yayi sbd lokacin É—aya tayi amma ace har yanzu batai bacci ba,suna zuwa dai-dai wajansa ya É—auke kansa,zaunar da ita tayi a kusa dashi tace “maza kici abinci idan ba su kike ranki ya É“aci ba,shima ba kiga yaci ba saike za kiÆ™i ci”ta faÉ—i hakan tana zuba mata dambun shinkafa a plat,da mmki Mummy ta kalli Jalal,shima da sauri ya rufe idanunsa sbd yasan abinda za tace dashi tace “bobo yaushe na zama abokin wasanka?” Juya idanunsa yay ba tare kuma da yace komai ba,zama tayi tsakaninsu tare da haÉ—e rai,ba tare kuma da tace komai ba ta wanke hannayenta,a nutse tayi bisimillah ta É—ebo abincin ta nufi bakin Jalilerh dashi,yadda Mummy ta haÉ—e rai babu alamun wasa yasa dole ta buÉ—e bakinta ta amshi abincin,shikam Jalal yana sane ya rufe idanunsa wai ko zata Æ™yalesa,amma tana É—ebo abincin tasa hannu ta É—aka masa doka a shoulder É—insa,da sauri ya buÉ—e idanunsa yana kwaÉ“e fuska, Jalilerh tsayawa tayi da cin abincin tana kallonsa sbd bata taÉ“a ganinsa yana shagwaÉ“a ba,kodan bata fiya tsayawa a wajansa idan suna tare da Mummy bane ohuuu?sosai yay mata Æ™yau a idanunsa gaba É—aya ya shagwaÉ“e fuska yana faÉ—in “Allah Besty I’m full” dake something idan yana buÆ™atar wani abu haka yake ce mata ba,hararsa Mummy tayi tace “I’m not ur Besty,gaba É—aya me kaci daza kace ka Æ™oshi? nasan kuma haka zakai gobe kai kafin so kaita zama da yunwa kamar Æ™aramin yaro?banda ma Ubangiji ya yanka da auki ai baza ka gano ba sbd siranta” ta faÉ—a tana nufar bakin Jalilerh ta abincin da sauri ya janye hannun Mummy daga bakin Jalilerh ya nufi nasa bakin yana Murmushi doka hannunta ya tura cikin bakinsa kana ya zare hannun yana tauna abincin, kwaÉ“e fuska Jalilerh tayi tare da turo baki tace “Mummy” kanta Mummy ta shafa tace “rabo dashi daughter,tunda abin hulaÆ™anci ne saikin Æ™oshi zai ci”gwalo Jalilerh tai masa, kallonta yayi tare dajan idanunsa ya lumshe,haka Mummy ta kasance cikin su idan ta bawa Jalilerh saita bawa Jalal,duk da cewar itama yunwar ta keji amma burinta kawai taga yaci abincin,bayan sun gama Jalal ya ware idanunsa kana ya riÆ™e hannun Mummy yace “wait….”ya faÉ—i hakan shima yana É—iban abinci a hannunsa, riÆ™e haÉ“a tayi tace “nikam kaka ka maidani ko mene?” bai ce komai ya nufi bakinta da abincin,dole ta tsaya ta amsa,sai da Æ™oshi ya rabu da ita, miÆ™ewa tayi ta nufi kitchen tana faÉ—in “daughter maza jeki Æ™wanta kada ki manta da addu’a” idanunta ne ya cicciko da Æ™walla ganin Jalal bai kulata ba, miÆ™ewa tayi zata bar wajan yay sauri kama hannunta juyawa tayi tana zaro idanunta waje,shima nasa idanun ya zaro yana É—an juyasu kafin ya miÆ™e tsaye, hanyar kitchen ya kala yaga Mummy bata fito ba,da É—an sauri ya rungome ta tare da bata light kiss a goshinta kafin ya saketa ya juya ya nufi part É—insa,da ido kawai Jalilerh ta bisa,saurin juyawa tayi sbd munsharin da taji, Mama ce Æ™wance ta buÉ—e baki sai sharara munshari take,da É—an saurin da take tunanin tana dashi ta nufi upstairs,ganin hakan yasa Nihila tayi sauri juyawa ta shige cikin bedroom É—in tana shiga ta faÉ—a saman bed ta rufe jikinta da duvet a dole bacci take.
A kasalance Jalal ya Æ™arasa part É—insa yana zuwa ya zare wandon jikinsa da singlet É—in,ya rage daga shi sai boxer, bathroom ya shige ya sakarwa kansa shower sosai yaji daÉ—in ruwan,bayan yay wanka ya Æ™arasa wajan sink ya wanke bakinsa tare da É—aura alwala,sanye da towel ya fito iya waist É—insa,yana zuwa ya nufi wajan dressing mirror ya shafa lotion sbd jin da gari yay yana sauyawa,comp yasa ya taje sumar kansa kafin ya fesa parfume,wasu fararan kayan bacci ya É—auka ya sanya kana yay addu’a ya Æ™wanta tare da Æ™aro gudun a.c,kana ya rage hasken É—akin,babu jimawa bacci ya É—auke sa.
_Election day_
Dukkan abinda aka sawa rana sai yanzu,idan kaga abin baizo ba to tabbas ba’a sanya masa rana ba,abinda ake jira wajan shekaru 2 da rabi yau gashi ubangiji ya nunawa duk wanda ya keson ganin ranar,ranar da mutanan gari sukaci burinta, ranar da magauta suka shirya yin zaluncin da suka daÉ—e suna shiryawa,ba wata rana bace face ranar ZaÉ“e,ranar Governor Mubarak Yahya cibo yake jin ya gama cika burinsa na zama Gwamnan jihar Ibadan,ranar da zai mulki dubban jama’ar gari,a Wannan rana kuma Dr Muhammad Jalal Kabeer bobo yake tunanin zai samu cikar muradin sa,burinsa na shekara da shekaru zai cika,farin muradin sa zai tabbatar yayinda a ranar yake saka ran sauke nauyin al’Æ™awari daya É—auka wa kansa na zama Gwamnan jihar Ibadan (Who win between two of them, Governor Mubarak Yahya cibo or Dr Muhammad Jalal Kabeer bobo?).
Dukkan local government da ake zaÉ“e da ita ta gama cika da mutane,maza da mata yara da manya,tsofaffi da samari,kota ina mutane zuwa suke suna kaÉ—a ruwan Æ™uri’u,kowa kuma da mazaÉ“arsa,haka zaÉ“e ya fara wakana babu tashin hankali ko kuma wasu hargitsi.
Governor Mubarak Yahya cibo ne shida mayan amintattunsa a wani keÉ“antaccen waje suna tattaunawa akan plan É—in da sukayi nisa a cikinsu,gyaran murya yayi yace “ina ganin zuwa yanzu lokaci yay da zamu juya masa tunaninsa,hutunsa ya Æ™are farin cikinsa ya Æ™are,kwanciyar hankali gidansu ya Æ™are,a cikin Æ™aramin lokacin zamu ruguza komai nasa” dry Lamir yyi yace “yanzu na samu Labarin zaice ya kaÉ—a Æ™uri’a a mazaÉ“arsa” Hon Faisal Lawan yace “kaga abin zaifi dai-dai kenan,yana shiga cikin jama’a mu kuma saimu watsa labarai cikin sauÆ™i jama’a zasu fara la’antarsa”gaba É—aya suka sanya dry,wayar Lamir ce tayi Æ™ara hakan tasa ya tsaya dry yay yace “Au,au,au shegen ne,bana gaya maku ba?”ya faÉ—a yana picking call É—in kafin daga can É“angaren Aryan yace “Baaba Lamir na maka magana whatsapp ka duba”Lamir yace “yawwa yaro na,bari na duba yaya zaÉ“an?” Aryan yace “Allahamdulillah,yanzu na dawo su kuma mutan gidan zasu fita” shuru Lamir yay kafin yace “fatan muka marawa baya?”Aryan yay dare yana mai danne zafi da raÉ—aÉ—in da zcyrsa take masa yace “haba Baaba Lamir kasan cewa zuwa yanzu babu wanda nake ganin baÆ™insa irin Yaya tayaya kake tunanin zanyi abinda zai Æ™ara masa masoya?tayaya zanyi abinda zai kawo masa ci gaba never,babu wanda na tsana a yanzu sama dashi dan haka ni naku ne dukkan abinda kuke buÆ™ata daga gareni ni mai biyayya ne indai zan samu cikar muradin a”dry Lamir yyi kafin yace “shikenan ka É—auka ka samu wannan yarinyar,yanzu muna cikin jama’a dukkan abinda yake Æ™asa zan kiraka” daga nan sukai sallama.
A hankali Jalal ya fito daga cikin É“angaren sa,yana sanya cikin wani Maroon É—in boyal mai manyan zane kuma shara shara,domin har farar singlet É—in sa ana gani,sai kuma babbar riga irinta boyal É—in,kana baÆ™ar hula ta tangaran,sai half covert shoe shima baÆ™i, hannunsa sanye cikin agogon warist mai Æ™irar iphone,ya sanya farin bluetooth a kunansa,sai Æ™amshi yake bazawa tamkar ranar aurensa,yana fitowa main parlour ya samu dukkan Æ´an gidan suna jiransa, Mummy na sanye cikin wani Orange É—in lace mai manyan flowers masu Æ™yau,ta sanya farin mayafi a kanta,sai Mameey itama cikin milk É—in lace irin na Mummy,sai kuma Abbou shi kuma ya saka shadda gezner,shima maroon color,gefe ya kalla yaga Nihila tasa wata rantsatsiyyar abaya black mai milk É—in stones sai sheÆ™i take hannunta riÆ™e da waya sai faman dannawa take,tana Æ™ara yaÉ—a manufarsa da kuma tayin jama’a na suka zaÉ“i Yayan nata, idanunsa ne ya sauka akan Jalilerh wacce yaga tai masa Æ™yau sosai,ta saka light blue É—in lace mai Maroon touchs sai siririn mayafinta shima Maroon da kuma flat shoe shima Maroon,hannunta riÆ™e da hisilin muslum,babu komai fuskarta sai lipstick tayi fresh kamar amarya,sai ya kasance ita dashi kamar sunyi anko,kallo guda yaywa ahalin nasa yaji wani farin ciki ya rufe sa gefe guda kuma na zcyarsa yana buga tare da faÉ—uwar gaba,haka dai ya wanzu yana azkar a ransa, Abbou ne yace “muje lokaci naja”Mummy tace “Mama mun tafi” kallon Mummy Mama tayi tace “to Allah ya kiyaye” gaba É—aya suka fita Mummy still tana cikin parlour’n kamar wacce tayi mantuwar wani abun, Jalal ne ya dawo baya yaja hannunta yana amsa addu’ar da Mama keyi masa,Babbar motarsa Jalal ya shiga,ya zauna mazaunin drever, Jalilerh na gefensa baya kuma Mummy ce, É—aya motar kuma Mameey ce a gaba Abbou mazaunin drever sai Nihila a baya,sai kuma motocin securities wajan guda uku suna mara masu baya,a haka suka fice daga cikin gidan Baba habu nayi masu fatan nasara.
A haka suka Æ™arasa mazaÉ“arsu, kasancewar duk a mazaÉ“a guda za suyi zaÉ“en,nan waje ya hargitse kowa yana murna yaga Jalal bobo,da Æ™yar securities É—insa suka nema masu waje saida kowa yay zaÉ“en sanna yayi, Nihila na zuwa aka rufeta mutane suna karÉ“ar rabonsu haka dai ta dinga raba masu kuÉ—in jakarta,wani ne ya hangi Jalilerh yace “laaa ga matarsa can ai kuzo muje wajanta”tana tsaye sai raba idanu take domin bata saba ganin haka ba taji ance “Hajia muna maku fatan nasara Allah ya taimaki mijinki in sha Allah saiya haye” rasa gane maganarsu tayi,sai tunanin waye mijinta take kafin tai magana yaja hannunta zuwa cikin mota yace “baki iya amsa addu’a bane?” Turo baki tayi bata ce komai ba,a haka suka shiga mota suka nufi hanyar gida,cikin nutsuwa yake driving yana kallon Mummy ta madubin motar data zabga tagumi,ana haka wayarsa ta fara Æ™ara ganin sunan Jafar na yawo yasa ya danna picking kana yace “uhm” Jafar daga can É“angaren ya share zufar data karyo masa yace “kana ina yanzu haka?” Da rashin fahimta Jalal yace “hanya” Jafar ya Æ™ara kallon jama’ar gabansa na wajan zaÉ“e yace “maza kuyi gida,sannan ku baza securities a layin”Jalal na Æ™ara giyar motar yace “lafiya?” Jafar kamar zai kuka yace “Jalal bazan iya faÉ—a maka da bakina ba,amma ka kunna redio nima ina wajan zaÉ“e ake sanar dani wannan tashin hankalin” Jalal baice komai ya katse kiran kai tsaye ya kunna redio’n dake motar lokacin 12:30 an fara labarai,yana kaiwa yaji ana faÉ—in
_Kudin labaran kenan yanzu zaku saurari cigaban labaran..,A yanzu ne muka samu cikakken labari daga bakin wani mutum wanda ya buÆ™aci a É“oye sunansa,inda yake faÉ—in, Munata murna zamu samu shugaba adali kuma mai asali,ashe shima tumun dare ne domin bincike ya tabbatar mana uban Governor Muhammad Jalal Kabeer bobo bashi da asali kawai yayi dirar mikiya a garin namu na Ibadan,abu mara daÉ—i an Æ™ara tabbatar mana shi kansa Muhammad Jalal Kabeer bobo ba’a san inda mahaifiyar sa take ba,a taÆ™aice ma ance mahaukaciya ce ta haifesa…_
Bai Æ™arasa jin labaran ba ya kashe redio’n lokacin guda kuma jikinsa ya fara rawa a zafafe ya juya ya kalli Mummy wacce take baya,a zaune ya ganta idanunta sun firfito waje gumi sai yanko mata yake,kana ya juya ya kalli madubin motarsa nan ya hangi motar Abbou tana biye da tasa, Jalal Æ™asa magana yay gaba É—aya tunaninsa ya tsaya brain É—in sa ta daina aiki,a hankali kuma lakar jikinsa ta zare ya fara ganin duhu a cikin idanunsa,yadda tunaninsa ya tsaya haka hannunsa ya zare daga kan motar,motar tafiya kawai take Jalilerh tsoro da firgici ya hanata koda mutsawa musamman da taga kan motar yana sauka daga tsari,ganin inda motar tayi tasa ta fasa uwar Æ™ara tare dayin jikin Jalal wanda ya kifa kasa Æ™asa a kuma dai-dai nan motar ta daki jakin baban gida cikin rashin Sa’a motar ta tuntsira tare da mirgina wa sau biyu a tsakiyar titi….
Sau wajan uku motar na mirginawa tsakiyar titi, Abbou na cikin motarsa yay saurin yin baya cikin tashi hankali tsoro firgici dana sani, da suka masa rufdugu lokaci guda, Nihila tuni ta fasa ihu ta fara kiran sunan Mummy, Mameey kam tashin hankalin abinda ke faruwa yasa ta kasa kwakkwaran mutsi sai numfashi take saukewa, Abbou yana parking a gefen titi yama rasa me zai yi gashi dai a zahiri motar yake amma gaba É—aya tunaninsa baya ga motar,can yay Æ™arfin halin Æ™arasawa wajan motar domin ba Æ™aramin tension yake ciki ba,a lokacin da zaka tsaga jikinsa ba lalle jini ya fita ba, kasancewar ranar zaÉ“e ne sai ya tashi babu kowa a titin domin ko babura basa hucewa balle motoci,wayarsa ya É—auka yama rasa wacce number zai kira,kawai yay shahada ya dannawa ambulance kira,tare dayi masu Æ™watance,suna nan tsaye domin ba zasu iya mirgina motar ta dawo dai-dai, ba wajan 20minutes Abbou ya fara jiyo jiniyar ambulance É—in,kafin cikinar 22minutes ambulance É—in sun Æ™ara su wajan,dasu da Abbou aka haÉ—u waje guda aka tayar da motar,da sauri Abbou ya nufi side É—in Jalal yana zuwa ta wajan glass É—in daya fashe ya zura hannunsa tare da buÉ—e murfin motar, zuciyarsa ce ta bada sauti da Æ™arfi dammmm sbd ganin Jalal da yay zaune akan kujera ya kifa kansa akan motar,cikin sauri Abbou ya shiga kukawar É—aga Jalal wando ko mutsi bayayi,sai daya É—aga sa sannan yaga Jalilerh Æ™wance a jikin Jalal ashe daman Jalal É—in shiyasa rufeta da jikinsa,gaba É—ayansu babu mai numfashi a jikinsu kuma ko É—igwan jini babu a jikinsu,gaba É—aya aka fito dasu daga cikin motar zuwa cikin ambulance É—in,gaba É—aya kan Abbou ya kulle yama manta tare da Mummy suke gaba É—aya tunaninsa tana motarsa,dai da wani police yace “aÆ™wai wani a back seat ne?” Da sauri Abbou ya dawo wajan motar shida wasu Æ´an sanda kasa buÉ—e Æ™ofar yayi sbd jinin da yaga yana zuba ta Æ™asan murfin motar,suna motar murfin motar suka samu Mummy Æ™wance jini na zuba ta gefen kanta a gani glass daya caketa a wuya,da sauri aka É—ura ta a kan bed zuwa cikin ambulance É—in, Nihila na ganin Mummy ta Æ™ara fasa wani ihun tana kiran sunanta tare dayin wajanta,da sauri Abbou ya riÆ™e,gaba É—aya aka sanyasu a ambulance sai zuwa babban asibitin dake IBADAN,kasa driving Abbou yayi sai wani daga cikin police É—in ne yaja motar zuwa asibitin.
Lamir suna zaune shida Governor Mubarak Yahya cibo da Hon Faisal Lawan da wasu manyan mutane,suna zaune suna tattaunawa akan yadda zaÉ“en ke wakana da kuma alamomin masara da suka gani,wayar Hon Faisal Lawan ce ta fara Æ™ara yana É—auka yace “hello..”shiru yay kafin yace “what..?ok bari mu kunna”yana faÉ—in hakan ya kashe wayar yace “kirana akai wai mu kunna redio an saki breaking news” Lamir yace “kai ma dai da wahala,kasan ko labarin mene” Hon Faisal Lawan yace “bari dai muji”ya faÉ—i hakan yana kunna redio’n Æ™aramar wayarsa,babu jimawa aka fara labaran kamar yadda aka gaya masa,da sauri Lamir ya miÆ™e yace “what..? ubanwa ya faÉ—i wannan abun?” da mamaki suke kallonsa kafin Governor Mubarak Yahya cibo yace “kai mene naka?koma waya faÉ—a ai ya Æ™ara taimakon mune” cikin É“acin rai Lamir yace “waya fada wannan labarin a cikinku?idan kun san kuna da hannu ko faÉ—a min wanene?” Hon Faisal Lawan yace “haba Lamir,babu wanda yabar a cikinmu gaba É—aya muna tare,sannan dukkan abinda ake shiryawa ai dakai ake komai,munsan cewa munyi niyyar watsa photo nan,amma kuma ba’a samu ba,banda haka ai babu abinda muka tsara wanda kai baka sanshi ba” da kallo kawai ya bisu kafin ya É—auki key É—in motarsa ya fice daga cikin gidan.
Mama kam tana zaune ita ɗaya sai mai aiki Laure wacce tace tazo ta zauna wajanta kafin masu gidan su dawo,tana dai zaune amma minti kaɗan zata miƙe ta leƙa waiko sun shigo, ɓangaren Aryan bawai haka nan yaƙi zuwa wajan zaɓe ba, tunda safe ya tashi da kasala da faɗuwar gaba yanzu ma yana ƙwance saman bed sai juyi yake kamar wanda bai da lfy,Imran Irfan da Jafar duk suna waje guda wajan zaɓen,ga dai alamomi nasara suna gani amma fuskokin su gaba ɗaya babu walwala,gudanar da aikin zaɓen suke babu kuzari a tare da su, Ambulance ɗin na parking a harabar asibitin nurses suka ƙarasu wajan da gadon marasa lfy, ɗaya bayan ɗaya aka dinga ɗura su akai, Nihila da Mameey banda kuka babu abinda suke, Abbou kuwa yana baka taɓa gane halin da yake ciki, lokaci zuwa lokaci yake danne saitin zcyarsa, manyan likitoci suka rufo akansu.
Lokaci kaÉ—an Labarin accident É—in Dr Muhammad Jalal Kabeer bobo da iyalansa suka karaÉ—e Garin Ibadan da kewayanta, cikin tashin hankali Jafar da Imran da Irfan suka Æ™arasu wajan,kallo guda zakai masu su baka tausayi,babu jimawa shima Lamir ya Æ™arasu wajan,har yanzu babu wani labari gane da halin da suke ciki domin babu likitan daya fito,Wajan 1:40 Alhaji khamal mahaifin Nusaibat shida matarsa Hajia Atine suka Æ™arasu wajan domin ko Nusaibat basu faÉ—awa ba, lokacin guda asibitin ya cika da mutane,sai da securities É—in Jalal suka fara kurar mutane ya rage family ne kawai a wajan,misalin 3 dai-dai likitocin suka fito daga cikin emergency room É—in sai share zufa suke,da sauri Abbou dasu Jafar suka miÆ™e tare da faÉ—in “Dr wanne hali suke ciki?”goge glass É—in hannunsa babban likitan yay kafin yace “muje office tukunna” gaba É—aya suka mara masa baya banda Alhaji khamal da Irfan wanda ya kasa mutsi dan fargaba,kujera Dr yaja ya zauna tare da nunawa Abbou waje ya zauna,amma sam Abbou bai san me Dr yake cewa ba hankalinsa yana wani wajan daban,ga wani sarawa da kansa yake yana runtsa idanunsa sai yaga abubuwa da yawa suna maza gizo a cikin idanunsa, Jafar ne ya kama hannun Abbou ya zaunar da shi a kan kujera kana yace “Dr yaya ake ciki ne Please,ka faÉ—a mana halin da suke ciki ka riga kasan ko waye shi a wannan garin,so Please ka faÉ—a mana muma hankali ya kwanta” jinjina kai Dr yay kafin yace “Allhamdulillah,da farko wajan shi Ur excellence É—in da sauÆ™i,ya samu tension ne,wanda shine yaja masa É—aukewar numfashi tun kafin faruwar accident É—in,sannan ita yarinyar tsoro ne yay mata yawa sai kuma É—aukewar numfashi data samu wanda yaja mata ta shiga duguwar suma,to duk su biyun nan da wani lokaci zasu farko..,”shuru yyi yana sauke numfashi ba tare da kuma da yace komai ba,Imran ne yaja numfashi yace “Mummy fa?” Kallon Dr Abbou yay abinda yake ta son cewa kenan sai kuma Allah ya taimake sa,baya Dr yayi yana sauke ajjiyar zcya kafin yace “ban san yaya zance maku ba,amma dai ita sai dai mu bita da addu’a” zcyar Abbou ce ta buga da Æ™arfi kafin ya tattara nutsuwar yace “kamarya?” Jafar yace “kai mana maganar da zamu fahimta Dr kasa zuÆ™atanmu cikin zullumi da kuma fargaba” Dr ya fesar da numfashi kafin yace “Ta samu buguwa a kanta, ma’ana kanta ya fashe,sannan ancire mata wani Æ™arfe a cikin wata sanadiyar cakarta da Æ™arfan yay ya tsinka mata hanjin cikinta,abu mara daÉ—in kuma glasses É—in daya caki wuyanta harya taÉ“a maÆ™oshinta”Gaba É—aya suka haÉ—a baki wajan faÉ—in “innalillahi wa’inna ilaihir raji’un”kafin Jafar yace “yanzu Dr mene condition É—in da take ciki?” Fesar da numfashi Dr yayi kafin yace “she’s critical condition,amma in sha Allah everything will be fine ok”da Æ™yar ya sauke ajjiyar zcya kafin ya saita numfashinsa yace “zamu iya ganinsu yanzu?”miÆ™ewa Dr yay yace “of course”gaba É—aya suka miÆ™e tare da bin bayan Dr kowa da abinda yake tunani a ransa,wani ward suka nufa kai tsaye Dr ya shiga wani special side,wajan part biyar ne a side É—in,room É—in farko suka tarar da Mummy Æ™wance an juna mata Oxcygen ta cikin bakinta gefen kanta an naÉ—eshi da bandeji haka ma wuyanta, cikinta ba an sanya anduga da filasta,kana an rufe jikinta da wani green É—in abu, É—akin sai Æ™arar na’urori gefen hannunta an maÆ™ala mata drip yana shiga a hankali, Æ™irjinta dake É—agawa shine kawai yake nuna tana raye,da sauri Abbou ya juya domin bazai jure ganin halin da matar tasa take ciki a halin yanzu ba,cikin zallar tausayin halin da take ciki Jafar yake kallonta yana jin Æ™walla na tarar masa a idanunsa, juyawa yay ya fita a room É—in, Imran na fita yay ya rufe Æ™ofar,daga nan wajan Jalilerh suka shiga itama tana Æ™wance an saka mata Oxcygen sai drip,hucin numfashin dake fita ta hancinta shike nuna tana raye,amma babu kurjewa ko É—aya a jikinta,daga nan suka nufi room É—in da aka saka Jalal a ciki,tun daga nesa suka hango farar fatar jikinsa data Æ™arayin jaaa,ga wani haske data Æ™ara tai fresh,da sauri Abbou ya Æ™ara wajan Jalal yana zuwa ya zauna tare da kama hannunsa sai a lokacin wata Æ™walla ta sauka daga cikin idanunsa, Æ™wance yake flat ko riga babu jikinsa sbd wani gumi da yake haÉ—awa duk da sanyin a.c dake kaÉ—awa a É—akin,cikin nutsuwa yake fidda numfashi,fuskarsa ta faÉ—a lokaci guda kamar wanda ya shekara yana jinya,ga yadda sumar kansa ta hargitse,babu abinda aka juna masa sai drip da injection da ake masa,cikin Æ™asa da Murya Abbou yace “am so sorry Muhammad,nina ja maka laifi nane,dana san wanene ni da tuni na bai yana gsky,bana da ikon faÉ—in komai akai na sbd sa gske ban san yaya nake ba,ina da asali bana dashi ban san komai a kaina ba Muhammad,ka yafemin kada kalleni da laifin da banawa ba,ban taÉ“a dana sani irin na yau ba,ban taÉ“a Æ™unci da shiga damuwa irin na yau ba, Tabbas ni me laifi ne,bansan da wanne baki zanyi maka bayani akan wanene kai ko kuma wacece mahaifiyarka,dan Allah ka gafarta min Muhammad” ya faÉ—a yana Æ™ara Æ™anÆ™ame hannunsa,wasu siraran hawaye ne suka silalo daga cikin idanun Jalal,cikin rawar jiki kuma ya riÆ™e hannun Abbou’nsa nasa still hawaye na kwarara a idanunsa, Jafar tuni yabar room É—in sbd bazai iya kallon abin tausayin nan ba,lura da halin da Jalal ke ciki yasa likitoci suka rufu akan,cikin zafin nama ya miÆ™e tsaye tare da fisge drip É—in da yake hannunsa,wasu likitoci ne suka nufu inda yake suna zuwa yasa hannu ya hankaÉ—esu cikin sauri haÉ—i da gudu ya fice daga room É—in.
Wata zabura Abbou yay jikinsa duk rawa yake,cikin É—aga murya yace “what…kin san mene kike cewa kowa?noo!! Nasan zafin ciwo yake sakin wannan zantukan,komai zaiyi dai-dai Please Oum Jalal ki daina wannan maganar na roÆ™eÆ™i kada ki sanya zcyta bugawa”ya Æ™are maganar a lokaci na farko da wasu hawaye Masu zafi suke sakkowa daga cikin idanunsa, Jalal kasa da idanu Yake kallon iyayen nasa ba tare daya iya cewa komai kuma, Nihila kam saurin miÆ™ewa tayi tana jin maganar kamar a mafarki, Lamir kam tuni yabar room É—in yana zcyarsa nata fasa,sbd ganin komai yana shirin ruguje masa ba tare da yakai Æ™arshe ba, murmushin takaice Mummy tayi kafin wasu hawaye ya fara saukowa daga cikin idanunta zuwa saman fuskarta,cikin rawar murya tace “wannan ranar nake jin tsoran zuwanta, ranar da zan fallasa asirin zcyata,na cuci kaina da nabiye ruÉ—in shaiÉ—an,zata iya yiwuwa kuga laifina,amma banyi hakan da son raina ba,nayi haka ne domin ceton rai” Aryan ne yace “Mummy kinata bayani a rufe,yana da Æ™yau koma mene kika aikata ace kin faÉ—a domin ki ciremu daga cikin ruÉ—u” É—an yunÆ™urawa tayi zata miÆ™e zaune Jalal ya kama ta tare da jinginar da ita a jikinsa,wasu sabbin hawayen ne suka wanke fuskarta kafin tace “tabbas Jalal ni ba haifiyar ka bace kamar yadda kake tunani,dani da mahaifiyarka Æ´ar wa da Æ´ar Æ™anwa ce, Mama itace ta haifi mahaifiyarka Zulfa,ni kuma Mama Yayar mahafiyata ce dani da yaya Lamir, sanadiyar rasuwar iyayen mu yasa muka dawo wajanta da zama, Allah ya jarabci Lamir da son mahaifiyarka Zulfa so bana wasa ba,kafin ya bai yana abinda yake ransa mahaifinka yaga Zulfa yace yana SO,nan Lamir yace sam bazai taÉ“a yiwuwa ba,a nan ya faÉ—a mata cewa yana sonta,ita kuma lokacin soyayyar Alhaji Kabeer tayi nisa a ranta,don haka tace bata son Lamir Alhaji Kabeer takeso,sosai tashin hankali ya gama bai yana akan fuskar Lamir ya rasa wanne mataki zai É—auka,gashi bashi da tunun dafawa,ana haka aka fara shirye-shiryen aure,ana saura Æ™wana guda aure Lamir yazo da labarin mahaifinka Alhaji Kabeer bashi da asali domin babu wanda yasan wanene shi da kuma iyayensa, Mama tace babu komai ita dai ta yarda da shi,sosai Lamir yay baÆ™in ciki domin a tunaninsa Mama za tace an fasa auran shi kuma a bashi auranta,haka akai aure cikin mutunci da kamala,domin Alhaji Kabeer yana da dukiya da kuma rufin asiri,bayan an kai Zulfa É—akinta,wata rana ina zaune a cikin uwar É—aka kamar mai bacci naji Lamir yana faÉ—in _ya fison data haihuwa aje har gida a kasheta sannan a kashe mijin,idan kuma hakan zai basu wahala kawai su kasheta subar gidan,idan har suka kasheta shi kuma zai nemi auren wata yarinyar sai yace a bashi riÆ™on abinda ta haifa daga nan duk dukiyar da mahaifin Zulfa ya bari É—an ta zai kajeta shi kuma zai riÆ™e É—an kaga dukiya ta dawo wajansa_ wannan dalili yasa na fahimci manufarsa ta son auran Zulfa da yace zai yi,dalilin guda É—aya ne akan dukiyar da mahaifinta ya mutu ya bar mata kasan cewarta Æ´a É—aya tilo garesa,sosai na shiga tashin hankali,kullum cikin tunani nake har na rasa wa zan faÉ—awa abinda yake damuna,kwanci tashi aka wayi gari Zulfa nada ciki sai tashin hankali na ya nunku fiye dako wanne lokaci,wata rana na shirya naje gidanta,a zaune na sameta cikin shigar duguwar riga abaya mai kalar milk sai touchs É—in yellow,zama nayi ina gaidata kafin tai Murmushi cikin fuskar mai cike da annuri wacce ta rabuwa da fara’a tace “Ina Mama? TaÆ™i zuwa ta ganni bata sani ba zan haife abin cikina lafiya ko akasin haka” gaba nane ya faÉ—i sbd jin abinda ta faÉ—a,sai kuma a wannan lokacin na tuna da maganar Lamir, Murmushi nai mata nace “haba Anuty ki daina faÉ—in haka,in sha Allah zaki haihu lfy” kallona tayi sannan ta kalli cikin nata tace “ai ÆŠan da zan haifa bashi da wata damuwa indai kina raiye kamar ni ce,dan haka tun yanzu abinda na haifa mallakin ki ne”tsayawa kawai nayi ina kallonta sbd abin na keji kamar almara,daga haka mukai sallama na koma,ina zuwa naita tunanin yau shene E.D.D É—inta zai cika?kawai sai na kirata a waya na tambaya babu musu ni kuma ta gayamin,ana saura Æ™wana É—aya zata haihu na buga sammako zuwa wajan wani malami sbd na aikata abinda nake gani shine kawai hanyar da zanbi na tseratar da rayuwarta,nan najewa malamin da buÆ™atar ina son ya haukata min Zulfa,amma ba haukan da zai cutar da ita ba,nai masa bayanin komai,zane yay a jikin Æ™asa kana ya É—ago kai yace “za’ai maki abinda kikeso,amma tabbas abinda yake cikinta shima haukan zai taÉ“asa indai ba ta haihu kafin haukan ya risketa ba” shuru nayi ina nazarin maganarsa sai kuma nace “babu damuwa indai ba wani abu bane mai illa”ban baro wajan ba sai da aka tabbatar min da aiki ya kammalo,a ranar bacci É“arawo ne kawai ya É—auke ni tunanin abinda na aikatawa Æ´ar uwar tawa ya dinga damuna,shin nayi dai-dai kowa? Shi ne abinda zcyata ke ta damuna da tambaya kenan,amma idan na tuna abinda Lamir ke shirin yi sai naji abinda na aikata shine dai-dai, washegari da safe kasa breakfast nayi nabi na damu kaina,ina wannan tunanin na tsinkayi Muryar Mama na sallati da sauri na fito ji kina yana rawa,kallonta nayi nace “Mama lfy?” Cikin damuwa ta shaidamin haihuwar Zulfa da kuma neman ta da akai aka rasa, É—aki na koma naci kuka na Æ™oshi domin duk abinda ya faru NICE SILA,lokacin da Lamir ya samu labari kasa cewa komai yay sai zirga-zirga da ya dinga yi a gidan,yafi kowa damuwa akan abin,bayan haka nice na buÆ™aci auran mahaifinka domin riÆ™onka ya dawo gareni, Lamir baiso haka ba,amma haka na rufe ido nace dole ya barni, tun daga nan rainonka ya dawo gareni,ni kuma kullum cikin fargaba nake bana iya bacci ga kuma mafarkan da nake marasa daÉ—i,ashe abinda naiwa Lamir yana nan Æ™asan ransa kuma bokansa ya bashi Labarin ina da hannu wajan É“atan Zulfa,nan ya É—ura min Æ™iyayya sannan yaci alwashi akan abinda zan haifa nan gaba,tunda nazo gidan babu taÉ“a tarayya da Abbou Jalal ba naje an sauke masa sha’awata sbd wani dalili nawa”
Saurin yin shuru tayi sbd yadda numfashinta yake fisga da Æ™arfi ga kuma yadda computer take Æ™ara ihu alamun rai ya kusa halinsa, Muryar Jalal can Æ™asa kamar bai son magana yace “bani Oxcygen”da mmki Dr ya kallesa sbd yasan cewa Mummy ita sa rayuwa sai dai wani ikon Allah, Dr yace “Ur excellence Oxcygen kuma?”da ido kawai Jalal ya kalli Dr alamar “eh” bai gardama ba ya miÆ™a masa, tallafo kan Mummy yay zai sanya mata Oxcygen É—in tayi saurin riÆ™e hannunsa tace “mene yay saura kuma?baka son na faÉ—a maka cikar muradina ne?ko kuma baka son na faÉ—a maka asalin uban Nihila?zuwa yanzu kaine garkuwanta kai kawai zan iya damÆ™awa amanar ta,kai kaÉ—an nake da tabbacin zaka kula da jini na ko bayan babu rai na”sbd É“acin rai da tashin hankali idanun Jalal har wani ruwa yake,ga fuskar tayi jajir, pouting lips É—insa yay cikin dauriya yace “wanna maganar duk babu amfanin ta,abu guda nake nema wajanki wanda nakeso kiyi min alfarmar sa”cikin sauri Mummy tace “babu abinda bazan iya yi maka ba Jalal,sai wanda Ubangiji ya sanya bazan iya yi maka shi ba” ajjiyar zcya ya sauke tare da jan numfashi kana ya lumshe idanunsa yace “yaya kamin Ammina take?”Murmushi Mummy tayi kafin ta kalli Irfan tai masa nuni da madubin data gani a jingine,da sauri ya dauko madubin ya kawo mata, karÉ“ar tayi da hannu É—aya kana ta sai tashi a fuskarsa tace “buÉ—e idanunka” a hankali ya buÉ—e idanunsa tare da sauke ganinsa a kan madubi,cikin sarÆ™ewar numfashi tace “kaga kamannin mahaifiyarka,aduk sanda nake tare dakai inaji kamar da ita nake tare ne,komai nata ka kwashe sa,hatta dimples É—inka irin nata ne…Ware idanunsa ya Æ™ara yi yana mai Æ™ara kallon kyakkyawar fuskarsa ta cikin madubin,wayar Jafar ce tayi Æ™ara da sauri yay picking ganin sunan Prince Hassan,daga can É“angaren Prince Hassan yace “an kammala zaÉ“e gamu yanzu mun É—auki hanyar zuwa hukumar inec domin tabbatar da wanda ya samu nasara a zaÉ“an,amma in sha Allah Ur excellence Jalal shine da nasara domin muna ganin alama” jinjina kai kawai Jafar yay kafin yace “on mah way in sha Allah”yana faÉ—in haka ya kashe wayar kana ya juya yabar cikin room É—in domin bazai iya Æ™arasa jin wannan labarin ba,da idanu kawai Jalal yabi Jafar, Jalal ne ya kalli Mummy wacce take ta fama da jan numfashi kafin yay magana tace “bayan na É—auki hukunci É—aukewa Oum Jalal sha’awarsa akai na,saina fara tunanin tayaya zan haifi Æ´ar wacce zata zama na a gurbina ko bayan babu raina,hakan tasa wata rana naje har office É—in Alhaji khamal na nemi alfarma a wajansa,kallo na yay yace “haba Oum Jalal wanne abin naki gsky aÆ™wai hatsari a cikinsa,bazan iya cin amanar amini na ba,wannan ai shi ake kira da CIN AMANR RUHI,tayaya zanyi mu’amala da matar aminina,gsky bazan iya ba”cikin kuka na kalli Alhaji khamal nace “ka taimakin dan Allah, wallahi banyi da wata manufa amma ina dalili na faÉ—in hakan kuma kasan komai na faÉ—a maka” cikin wani hali Alhaji khamal yace “yanzu idan na yarda kika samu ciki kika haihu mene sunan yaro ko yarinyar da kika haifa? Shege fa kenan..⁷⁸ ⁷⁹
