TAWA TA SAMENI CHAPTER 4 BY HALIMA ABDULLAHI K/MASHI
TAWA TA SAMENI CHAPTER 4 BY HALIMA ABDULLAHI K/MASHI TAWA TA SAMENI CHAPTER 4 BY HALIMA ABDULLAHI K/MASHI Www.bankinhausanovels.com.ng MUN TSAYA nace mama wanene yake ma baba sharri?tace aa mugun abu ai ba sai kasan me maka zaka roki Allah ba,nace to insha Allahu zan dinga yi mishi,da dare sai ga dan aiken baba,yaya Ibrahim ne baba ya aiko wai muzo ni da mama babban falo babu neman ba’asi ya dauki hannu a gaban mutane ya mari mama ga yan aiki ga yayyena ga ni ga anty faty bayan marin ya cigaba da fada wai karya kuma jin an taba mishi mata inko ta kuma marinta ta mari aurenta mama tana rike da kumatu sai nan tace cewa tayi maka na mareta?yace to yau kuke me yasa tun da kuke tare bata ce kin mare ta ba sai yau kuma tace tana son in rama mata shi yasa mama tace shi kenan ni Allah ya rama mani ta shige daki,duk da karancin shekaru na sai da nayi mamakin baba wai ya rama wa anty mari? na juya ZAMU TASHI na dubi anty sai naga tana wani ciccika tana batsewa wai an rama mata, na bi mama daki na iske tana kuka na dafa ta nima na soma kuka ina cewa…