SHU'UMIN NAMIJI CHAPTER 1 BY FATYMA SARDAUNA SHU’UMIN NAMIJI CHAPTER 1 BY FATYMA SARDAUNA Www.bankinhausanovels.com.ng Wani irin gudu black colour car ƙirar RANGE ROVER ke falfalawa akan babban titin dake cikin garin *ABUJA* …+ Gaban wani irin makeken gate motar ta tsaya, minti kaɗan kuma ta soma wani irin ƙara kamar zata cire kunnen maisaurare, cikin mintuna ƙalilan maigadi da jikinsa ke rawa ya wangale makeken gate ɗin, da gudun bala’i ya cinna hancin motar tasa ciki, daga yanayin yanda yayi parking kaɗai ya’isa nusar dakai cewa wanda ke cikin motar, cike yake da iskanci haɗi da zallan taɓara… Duk yanda naƙosa wanda ke cikin motar yabayyana nasamu damar ɗauko muku hoton fuska da surarsa amma abun yaci tura, domin dai shegen ƙin fitowa yayi bare nasamu ganinsa…….1 15 minutes ya kwashe cas batare daya sanyo kansa waje ba, a hankali yasako ƙafarsa waje wacce ke ɗauke da tsadadden black canvas mai ɗauke da fararen igiyoyi a samanta, a hankali yagama fito da duka jikinsa daga cikin motar, Masha Allah !! shine abun dana …