RUBUTACCIYA BOOK 4 CHAPTER 7 BY FATIMA IBRAHIM GARBA DAN BORNO
RUBUTACCIYA BOOK 4 CHAPTER 7 BY FATIMA IBRAHIM GARBA DAN BORNO RUBUTACCIYA BOOK 4 CHAPTER 7 BY FATIMA IBRAHIM GARBA DAN BORNO Www.bankinhausanovels.com.ng MUN TSAYA Sultan ya dake, ya shafi kumatunta ya matso da ita jikinsa sosai, “Ke rubutacciya ce. Ina fatan shikenan kin fahimci ke wacece ko? Oya tashi mu je mu kwanta ko kuma in zane dan bakin nan da bulala.”Nasreen ta yi murmushi tace, “Lahh ai ba a zane baki Deena.” A kunne ya rada mata wata magana ta sunkuyar da kai kunyarsa ta kama ta, ta ruga da gudu tana WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG KyalKyaltar dariya. Sultan ya saki ajiyar zuciya da Karfi ya mayar da kai ya jinginar a jikin bangon yana nazarin ta hanyar da ya kamata ya biyo wa Nasreen. A ganinsa lokacin boye-boye ya wuce, yana ganin fada mata gaskiyar za tafi, domin lokacin da zai sada ta da danginta ya yi. Yana tunanin lokacin da zai mayar da hankalinsa akan matsalolin Nasreen ya yi. Ko babu komai a yanzu ya riga ya gama da matsalar idanunta, tana iya ganin kowa. Yana nan zaune bai tashi ba, ya ji hannaye masu taushi suka rufe masa idan…