RUBUTACCIYA BOOK 4 CHAPTER 6 BY FATIMA IBRAHIM GARBA DAN BORNO

RUBUTACCIYA BOOK 4 CHAPTER 6 BY FATIMA IBRAHIM GARBA DAN BORNO
RUBUTACCIYA BOOK 4  CHAPTER 6 BY FATIMA IBRAHIM GARBA DAN BORNO  Www.bankinhausanovels.com.ng  MUN TSAYA  Zan je duniya in fada da babban murya dan cikina ne ya sa ayi min kishiya da ‘yar aikina. Kai Sultan ba zan taba yafe maka ba, ka jima kana cutar da ni, ka kawo min mazinata gidana, ka kawo min ‘ya’yan arna gidana, ka kawo min _ kishiya gidana? Idan na ce na yafe maka kai kanka sai kayi shakkar kasancewata uwarka, wacce tasha wahala kafin ta haifeka. Da nasan wahalar da zaka jawo min kenan Sultan da na danne ka a lokacin da nake naKudanka ka mutu, da nasan tuggun da kake son ka girma ka hada min kenan, babu ko shakka da a lokacin da likita ya sanar da ni ina da ciki da na sha magani na watsoka kana matacce. Allah ya isa tsakanina da kai Sultan ban yafe maka ba.” Hankula fa sun Kara tashi, danasani ya sake shigarsa, bai taba tunanin abin zai kai haka zafi ba. Sultan ya riKe kansa da Karfi yana ganin  Www.bankinhausanovels.com.ng  mutanen wurin bibbiyu. Ya yi magana cikin dauriya da cije…