RAYUWAR CAMPUS CHAPTER 14 BY Fateeyzah mbs✍️ RAYUWAR CAMPUS CHAPTER 14 BY Fateeyzah mbs✍️ Www.bankinhausanovels.com.ng ….Gidan da muke zaune yana *Maitama* ne, yayin da daddy da matarsa suke a *Asokoro*, gidanmu babban gidane gari guda, mai d’auke da gate har 4, inkin shigo gate na farko, parking space ne mai d’auke da canopies na mota har goma sha biyu(12), kowacce canopy tana d’auke da tsala tsalan mota guda biyu, yayin da suke dauke da Alon da aka rubuta *TURAKI* da manyan bak’i wanda aka yi kuma numbering dinsa from 1 to 12, dai² adadin yaran gidan, first born dinmu bro suleim shi keda canopy mai d’auke da Alon *TURAKI1* haka abun ya tafi har kaina last born da nawa ke d’auke da *TURAKI12*, hatta numbobin motar haka suka kasance, daga d’ayan b’angaren kuma part d’in masu gadine da sauran ma’aikatanmu maza, anan kuma zaki kuma shiga wani gate d’in na biyu, shi kuma nan d’akunan mazan suke, flat takwas ne shi kuma suna d’auke da Alo shima kamar na canoping mota, sai dai su flat hudu na kallon sauran h’udin,…