ZUMUNTAR KENAN BOOK 3 CHAPTER 9 by Sumayyah Abdul-kadir
ZUMUNTAR KENAN BOOK 3 CHAPTER 9 by Sumayyah Abdul-kadir
ZUMUNTAR KENAN BOOK 3 CHAPTER 9 by Sumayyah Abdul-kadir Www.bankinhausanovels.com.ng kansa, don ma anfi karfinta ne amma da ko kusa baka cancanci auren Fa’izah ba, Aliyu shi ne mutum mafi dacewa da auren Fa’izah ba kai ba Fa’iz!”. Banda Mama ce, UWA! Wa ya isa ya dubi tsabar idonsa ya gaya mishi haka Ya yi kwafa kamar zai hadiyi zuciya ya mutu don takaicin kalaman Mama, ya yi shiru yana gwama numfashi kamin ya dubi Mama cikin sanyin jiki. “Wa yafi karfin nata? Gaba daya cikin ku wa yafi karfin nata a yanzu Mama? Cikin ku duka an rasa mai sanya baki a bani matata kamar yadda aka baiwa kowa tasa, saboda ita ishasshiya ce kowa yana tsoronta. To ni kam na zo daukar aurena ne (dead or alive)!” Mama tayi dariyar da ta kara kular dashi, ta ce. “Kofar hanyar Zaria a bude take ai kullum Fa’’iz, kai da baka tsoronta sai ka je ka dauki abarka, munji mu tsoron ta muke ji kada muje ta fasa mana kai kamar yadda ta fasawa jarumi Fa’izu Abubakar”. Haushin maganganun Mama koko ya ce shag…