ZUMUNTAR KENAN BOOK 2 KARSHE CHAPTER 8 by Sumayyah Abdul-kadir END

ZUMUNTAR KENAN BOOK 2 KARSHE CHAPTER 8 by Sumayyah Abdul-kadir END
ZUMUNTAR KENAN  BOOK 2 KARSHE CHAPTER 8   by Sumayyah Abdul-kadir END ‘yar gidan mutunci kamar A.B. Su wadannan da kika bi kika tadawa_ hankali meye ruwansu ne? Me ya shafe su? Aure dai sun yi kuskuren daurawa. Amma igiyar warware shi da kwance shi ba ta hannunsu balle su kwance ko su warware. Duk wannan kakabi da zagi da tashin hankali ba nasu bane, ba su ya kamata ki yiwa ba tsakaninki da Fa’iz ne can. Amma ina ruwan Ummi, Hajjah ko Zanirah?”  Na galla masa harara na ce, “To shin ina na ganshi balle in yi mishi Yaya Aliyu? Ni kam yadda nake ji a zuciyata baki dayan A.B nake jin haushi. Har kai din wallahi’.  Murmushi ya yi, ya rausayar da kai, “Ta ina laifin wani ke shafar wani? Har da Yaya Aliyu? Fa’izah” Fa’eez shi ya nemi aurenki da kansa domin gyara zumuncinku da ya gurbata a baya”’. Ban san sanda na lailayo ashar ba na ce, “ZUMUNCIN me? In dai wannan shi ake kira gyara zumunci to ba shi bane, sai dai kara lalata shi. Na ji zan iya yafewa Fa’iz dukkan abin da ya yi mani, amma ba ta h…